MASARAUTA 5

145 20 0
                                    

💙💙💙💙💙💙💙💙
      *MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA BIYAR. 5*

*SADUKARWA GA Mrs S. Waziri.*

Yau zaman su a fadar mai martaba ne,wata ƙaramar fada da yake zama da mutanen gidanshi,sai dai babu wanda yake magana kowanne da abubuwan da yake tunani,Yarima Amin ya na gefen sarki, Aymana tana nesa dasu,Bilkisu kuwa tana gun Umma suna dan magana jefi-jefi.

Hajiya da Mama kowane yana nazari akan zaman Yarima Amin da maimartaba,gabaɗaya sun kasa fahimtar yadda Maimartaba yake son zama da Yarima a yanzu duk wata kulawar da yake ba yaranshi maza ya koma kan Yarima Amin.

Shi kuwa Mai martaba a bisa zaman da yayi da Amin ya fahimci asalin kyawun hali da ɗabi'u irin na shi musamman akan na ƙasa da shi.

"Zuwa dare ina son ganin ka a ɗakina."

Yarima Amin ya kalle shi cikin ɗan razana don ya san tunda yazo gidan bai taɓa shiga cikin sashen sarki ba balle har ɗaki.

"To in sha Allah Baba."

Mai martaba Ya miƙe yan kallon gimbiya Aymana ita ɗinma shi take kallo,murmushi yayi hakan ya bata damar miƙewa tsaye don yi mashi rakiya.

Sauran mutanen wajen kuwa,sauka lafiya suka yi mashi.

Umma ta miƙe tana barin wajan tare da faɗin "Na barku lafiya."

Wasu daga cikinsu sun amsa sai dai wasu sun bita da kallon ko in kula.

Yarima Amin kuwa ya tashi zuwa ɓangaren shi,yayin da ya masu bankwana cikin ladabi.

Anan fa suka buɗe babin cigaba da gulmace-gulmace da maganganun nuna tsana akan Yarima.

Hajiya ta ce"Ya zama lalle mu san abin yi tun wuri,don naga wankin hula yan neman kaimu dare."

"Yarima nan yana gab da komawa mafifici a gidannan"cewar Mama da ke gyara zama.

Yarima Shuraim ya ce"Ki bar komai hannu na da kanshi zai tattara ya koma don ba zan laminta,ina mai jiran gado in koma ɗan kallo daga nesa ba."

       ****
Da yamma  Sarki ne zaune da Umma tana zuba mashi shayi a kofi,a duk cikin matan shi Allah ya gani ya fi son Umma,domin Soyayyar ne ya shafi Aymana,saboda sauƙin hali,da ba abu baya,sam ita babu ruwanta da shiga shirgin da ba nata ba.

"Gimbiya ina so muyi wata magana da ke?"

Ta miƙa mashi kofi tana faɗin"Ina jinka rankaya daɗe."

Murmushi yayi tare da tashi zaune daga kishingiɗe da yake"Me kika fahimta kan yaron nan Yariman Toro."

"Wajen me kenan."

"Halaiya da kuma ɗabi'u."

"Yaro ne mai ganin girman mutane ga sanin darajar al'umma, kafin zuwansa banyi tunanin zamu same shi a haka ba..."

"Shi kenan barni nan,dama na saba jin bakinki yana faɗin alkhairan mutane"

Yar dariya tayi"Kenan baka yadda ba,to ka tuhumi fadawa da sauran mutanen gidan Ni dai nasan...

"Ina son ba shi Auren 'yata Aymana na..."

Cikin yar razana ta ɗago"Shi yace maka..."

"Ni ne nake son haɗa auren"

"A gani na idan bashi yayi maganar ba kar mu fara,ganin yadda zamani ya canza" tayi maganar cikin sanyin murya don tasan bata isa sauya ra'ayinsa ba, domin ya bata haƙƙinta ne na mahaifiya.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now