MASARAUTA 15

158 26 2
                                    

💙💙💙💙💙💙💙💙
*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).

*SHAFI NA SHA BIYAR. 15*

Sai wajan ƙarfe tara Gimbiya Aymana ta samu nutsuwa ganin bacci ya ɗan ɗauki Yarima,harta zauna sai ta tuna tayi salla ba, banɗaki shi ta je acan tayi alwala ta fito tayi natà sashen,Anan ta samu Farida zaune,sannu tayi mata,Aymana tayi salla,sannan tace"Farida."

"Allah ya taimake ki?"

"Kije ki sanar da Ummi Magajin gobe ba shi da lafiya,yana buƙatar addu'ar ta."

Har ta miƙa Aymana tace"Ki sheda mata,baya son kowa ya ji hakan,kema ki kiyaye."

"An gama ranki shi daɗe"

Tana zuwa aka sheda mata Ummi tana wajen Maimartaba,hakan yasa ta nufi ɓangaren Maimartaba,sai da ta sheda daga Sashen Yarima aka aikota sannan aka barta shiga.

Ummi ta fito daga turakar shi,tana amsa sallamar Farida,Farida ta duƙa tana kwasar gaisuwa,Ummi tace"Allah yasa lafiya."

"Da sauƙi dai maigidanmu ne bashi da lafiya shine Gimbiya tace nazo na sanar dake,don kiyi mashi Addu'a."

"Subhanalllah me yake damunshi"tayi maganar cikin nuna damuwa.

"Bani da masaniya,kuma ta ce Yarima yayi hani da baiyyana rashin lafiyar shi ga Mutanan gidan nan."

Ummi ta ɗan razana"ki je ina zuwa"

Farida ta miƙe tana cewa"Allah ya kawoki cikin Aminci,na barki lafiya"

Farida tana fita Ummi ta koma turakar sarki,kallon fuskar ta yayi ya gane akwai abinda yake damunta"Fitarki cikin walwala sai kuma kika dawo akasin hakan"

"Magajin Gobe ne ba shi da lafiya."

Da sauri mai martaba ya miƙe daga kishingiɗe da yake"nayi mamaki har wannan lokacin Yarima bai zo yayi mani bankwana ba,ga alama ciwo ya fi karfinshi."

Ummi ta kaɗa kai"zan koma ciki na leƙo shi".

"Dole muje tare"

"Yarima yace kar a sanar,zuwanka zai bayyana rashin lafiyar"

Irin son da Maimartaba yake wa Yarima bazai jure ace bashi da lafiya bai je ya duba shi ba"Zanje ba tare da sanin kowa ba"

Ummi ta miƙe suna fitowa,bafade ɗaya ne suka tafi tare sai wata Kuyanga dake jiran Ummi a wajen.a tare suka yi sashen Yarima.

Aymana tana zaune ta gama canza mashi ruwa saboda na farkon ya ƙare.Ummi ce ta kwankwasa,Aymana ta miƙe sai dai ba asalin ƙofar da ke kaika ciki bane.

Kenan akwai ƙofa ta baya,zuwa tayi tana faɗin"Waye anan."

Kuyangar tace"Ranki ya daɗe kuna da baƙuncin Maimartaba da Gimbiya Ummi

Da sauri Aymana ta buɗe tana basu hanya tare da Faɗin"Sannun ku da hanya."

Ummi ta riƙe hannunta sukayo ciki,Maimartaba ya maye masu baya,Kuyangar taja ƙofar suka tsaya a waje.

A bakin gadon suka tsaya,Aymana ta durƙushe tana gaidasu amsawa sukayi,Maimartaba yace"'yata tun yaushe ne bashi da lafiya?"

"Ga dukkan alamu ya jima da zazzaɓin,amma ɗazu na shigo nasamu baya iya komai"

Shiru Maimarta yayi,Ummi tace"Ɗakin magani basu sanar bashi da lafiya ba."

"Ummi nice na duba shi."

MASARAUTAWhere stories live. Discover now