MASARAUTA 19

107 14 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA SHA TARA. 19*

Ɗakin taron aka ɗau murna da hayaniya hakan ya ɗan dakatar da Mai martaba daga maganar.

Da sauri Yarima Amin ya buɗe ido yana son tabbatar da abinda kunnuwan shi suka ji, Bilal dake gefen shi ya riƙo hannun shi yana murna, Yarima ya fara Hamdala ga ubangijin shi, kafin ya juya yana kallon duk mutanan wajen.

Take fadawa suka fara kirari, Mai martaba yana ci gaba da zance sai dai wannan lokacin babu mai sauraron shi, kasancewar maganganun da yayi sunyi tasiri wajan janye hankullan mutanen wajan.

Waziri yayi wata iriyar razana wadda har sai da Galadima ya zaunar dashi.

Yarima Saifu ya buga kanshi akan kujerar gaban shi tare da miƙewa yana barin ɗakin taron, ya nufi sashen mahaifiyar shi Gimbiya Mai gado.

Tana zaune kan Kujera da wasu Kuyangi suna tausa mata ƙafafuwanta a hargitse ya shiga yana wata irin ƙara "Ba zai yiwu ba."

"Yarima." Gimbiya ta kira sunan shi.

"Yau Abba ya ƙara tabbatar da banbancin da yake nunawa tsakanina da Amin, yau ya zama ranar da bazan manta ba a tsayin rayuwata, Abba ya miƙa mulki zuwa ga Amin a gaban ɗumbun Al'umma."

A kiɗime Gimbiya Mai gado ta miƙe hakan yasa ta hanɓarar da Kuyangar dake mata tausa.

"Kar ka tambatar min da haka Yarima Saifu."

"Ki kirani da Saifuna don yau..." Sai dai bai ida ba.

Jakadiyya ta buɗe labule cikin sauri tana zubewa gaban su "Yau wane irin juyi duniya take son yi mana? Allah ya taimakeki."

Gimbiya Mai gado ta kalleta tana jinjina kai, take ta fara kai kawo.

***

Da guda Kuyanga Aisha ta isa ɓangaren Gimbiya Ummi, don ta san uwar ɗakinsu Aymana tana can.

Ummi ta kalle ta "Lafiyar ki Aisha?"

Kuyangar ta ƙara sunkuyawa gaban Ummi tace "Na zo shaida maku abin Alkhairi, Ranki shi daɗe, Allah y..."

Kafin ta ida Aymana dake tsaye lokacin ta fito tace "Ki je maganar ki."

"Allah ya taimakeki Yau matar sarki ta zama mahaifiyar sarki, haka ɗiyar sarki ta zama matar sarki a gidan nan."

Da sauri Ummi ta miƙe "Lallai Allah yayi gaskiya, Allah shi ne mai iko."

Aymana ta durƙusa gaban Aisha tace "Waya sanar da ke?"

"Yanzu na ji a gidan nan, Mai martaba ya sanar Yarima Amin shi ne zai hau karagar shi."

Aymana ta miƙe tana murmushi ta juya ta kalli Ummi, cikin Sauri Ummi ta riƙo Aymana suna rungume juna.

Sai lokacin suka fara jiyo guɗa da hayaniya na tashi a gidan.

Ficewa Aymana tayi zata nufi sashen Baba Galadima wajen Mama, ahanya suka haɗu dariya suka yiwa juna Mama ta riƙo Aymana "Kin ga ikon Allah ko?"

Aymana tace "Muje ciki Mama."

Mama tace "Ni fa sai na ƙarasa wajen Gimbiya Ummi don shigar da murnata."

Aymana tace "Zan je ɓangarena, zuwa ku gama.

***

Taro Ya tashi Mai martaba ya sallami kowa sai dai Yarima Amin baya ganuwa ya shige cikin sarakunan dake taya shi murna.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now