MASARAUTA 50

122 15 1
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA HAMSIN. 50*

*SIYYA COLLECTION* 07033111950

Ki na buƙatar HUMRA mai ƙamshi? *Nemi Siyya collection.*

Ki na neman TURAREN WUTA, Na jiki, kaya, da na tsugunno, kina son zama ƴar gayu saboda ƙamshi mai sanyi ? Nemi *Siyya collection*

Ina Amarya da uwayen gida dake son dawo da martabar Auren su *Siyya collection* na da ingantatun kayan gyaran jikin amare. Akwai kayan mata masu ciko da jiki da kuma saukar da ni'ima.

Kina son fatar ki tayi laushi da santsi tare da haske mai kyau? *Siyya collection* ta tanadar maku, light cream, whiterning cream da Glowing cream kala-kala.

Sabulun wanka masu saka fata haske, ingantattu da basu da illa. ki nemi *Siyya collection*

Supplement domin ciko da inganta Breast da hips, akwai na kyaran fata xalla, ba sa da illa ga lafiyar ku.

Don gyaran gidanku da tsabtar shi *Siyya collection* tana siyar da turaren mopping.

Ku dai ku Tuntuɓeta akwai sauƙin kuɗi, haka kuma muna tura kayanmu duk garin da kuke. *Siyya collection*
Call:-09136159778
Whatsapp 07033111950.

*Page 50*

Cak ya tsaya yana juyowa, ya kalli Mama da take ƙoƙarin tambayar Aymana abinda yake faruwa, hakan ya tsaɓa zuciyarshi sai lokacin ya fara tunanin abinda ke damun Aymana, cikin rashin jin daɗi ya nufe ta, ba ya son abinda zai shafi matarshi.

Cikin taƙama ya tsaya, sai dai bai iya magana ba saboda izza, sai shan gabanta da yayi fadawa suna binshi, ya fara durƙusawa kujerar gabanshi wanda Mai martaba ne da mutanenshi.

Sai lokacin ya kula ashe hankalin Mai martaba yana kan Aymana da ke sauke ajiyar zuciya.

Ta Sunkuyar da kanta cikin jin daɗi tare da son gage kwallarta kar mutane su gani, ta bi nayanshi tana duƙusawa gaban Mai martaba dake dafa kafaɗar Sultan.

Sun jima kafin suka miƙe, lokacin kuyanginta suka matso itama suna take mata baya.

Ta zame jiki tare da barin shi, ta dawo wajan Uzairu suna magana "Ka canza kujerar, duk wanda ya tambaye ka dalili ka sanar nice na bada umarni."

Uzairu ya sunkuya yana faɗin "To Ranki shi daɗe."

Sultan lokacin yana gaban Gimbiya Mai gado, ya juya yaga babu Aymana babu dalilinta, ya yi ƙoƙarin ɗagowa sai ya hangota tana magana ta Uzairu.

Kafin ya nufeshi da sauri, haka suka ci gaba da gewayawa, gaba ɗaya bakin suka gaisa, Haka suka nufo mazaunin su, a gefe kaɗan Kujerar Ayda ce zaune wadda tuni haushi da ƙululun baƙin ciki ya gama turniƙeta.

Sultan ya matsa gabanta, ya ɗan sunkuya yana kallon fuskarta, Ayda ta kawar da kanta kefe, cikin sauri ta juyo kar Sultan ya mata fatafata.

Murmushi ya yi don ya fahimceta, ya sa hannu yana riƙo khairat dake saman cinyarta, yana wasa da hannunta.

Aymana ta zo tana sunkuyawa ita ma, cikin salon kissa ta ce "Sannu da zuwa Gimbiya."

"Yauwa." Cewar Ayda, Sultan ya miƙe yana nufa matattaƙalar da kujerar shi take.

Dai-dai lokacin ya ga Uzairu ya mayar da kujerar farko gefe, yana dai-daita sabuwar da ya kawo.

Cikin rashin fahimta yake kallon su, Sunkuyawa sukayi da girmamawa, Sultan ya hau fadawa suna gewaye shi, kallon tuhuma yake wa Uzairu.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now