*MASARAUTA.*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA TALATIN DA BIYU. 32*
Riƙe hannunshi da tayi hakan ya sa shi tuna cewar bata da lafiya, nutsuwar shi ya nema, tsawon lokaci Aymana tana riƙe da hannun shi, har bacci ya kwashe ta, sai da ya sauke ajiyar zuciya ganin bacci ya ɗauke ta, ya ƙara gyara kwanciyar shi, ta hanyar ƙara haɗe jikin su, ya jima kafin shima baccin ya ɗauke shi.
Asuba nayi Sultan ya lallaɓa ya janye jikinshi, don tafiya masallaci, ba ya son tashinta, abinda bai sani ba Aymana tana jinshi, ta yi kamar bacci take, tana jin fitar shi ta miƙe ta shiga banɗaki tayi wanka ta fito tana gabatar da salla.
Kafin shigowar shi ta bar ɓangaren zuwa nata, ta jima tana zaune tama rasa abin yi sai tunane-tunane take, can wani tunani ya faɗa mata, ta miƙe ta fara shirinta.
Sultan yana ɗakin shi, bayan ya tabbatar ta fita, shiri yake don fita fada.
Ƙarfe tara dai-dai Jakadiya ta fara maganganu da guɗa bayan taje dubo Ayda, ta samu labarin tana da ciki.
Kowa na gidan sai da ya shiga kaɗuwa, kafin kace me, gida murna ake kowa na gidan ya samu zancen cikin Ayda.
Aymana tana zaune ta miƙe tana son zuwa wajen Sultan a karo na biyu don taya shi murna.
Sultan ya tsinkayi maganganu dake wakana a gidan, hakan ya ɗaga hankalin shi, kan kujera ya koma ya zauna yana mai dafe kanshi, kenan Ayda ciki ne da ita.
Sai da ta buga ƙofa kafin ta shigo, ganin shi tayi dafe da kai ta yi murmushi "Allah ya ƙara tsawon kwana ga Sultan, Zan zo ace saƙon da aka sanar dani nice zan fara maka albishir."
Ɗagowa yayi ya kalli yadda Aymana ta durƙusa gaban shi, kallon shi take sosai tana son gane yanayin data tsinkaye shi, ganin tana nazari hakan yasa ya fara neman tattaro Izzar shi da mulkinshi.
Ya gyara zaman shi "Ina jinki."
Murmushi tayi "Allah ya taimaki Sultan, Sarki ɗaya tamkar da dubu, idan an bani dama ina da zance baki na."
"Ina jin ki!" Ya faɗa babu alamun fara'a sai Izza dake bibiyar jinin shi.
Aymana ta fahimce shi sosai, hakan ya sa ta fara neman ta ta Izzar tare da faɗin "Farin ciki zuciyar masoyan Sultan, Ina mai sanar dakai Gimbiya tana gab ƙara kawo mana Yaro."
Kuri yayi mata da ido, wai ita baisan kalar halinta ba, sam baison taya zai jawo farinciki ya nuna ba, murmushin yaƙe yayi "Wa ya sanar da ke?"
Ta ɗan sunkuya "Allah ya baka nasara!" Ta faɗa ba tare da ta bashi amsa ba.
Take zuwan su Ɗakin magani ya faɗo mashi, ya kalleta sosai tare da miƙewa "Allah ya riƙa mata!"
Ya faɗa Aymana ta kalle shi, ya gane tana da ko tambaya ya juyo da sauri "Gimbiya zata samu tukuici don sanar da Sultan ƙaruwar da za a samu a gidan shi."
Gyaran murya tayi "Na gode!" Sultan ya cigaba da kai kawon da baima san yana yi ba, Jakadiyya ta turo ƙofa, tana kwasar gaisuwa.
"Allah ya ja zamanin Sarki."
"Da buƙatar wani abu?" Ya tambaya, jiki babu kwari ganin yanayin Sultan tace "Allah ya maka tsawon rai, Abul yana gab samun ɗan uwa!"
Sultan ya juya ya nufi kujerar shi ya zauna, lokaci guda jakadiyya taga Sultan ya fara murmushin da babu shi a azuciyar shi.
"A bata kulawa da abinda ke cikinta."
"Saƙon taya murna daga mutanan cikin gida."
"Na amsa." Ya faɗa.
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.