MASARAUTA 16

143 25 0
                                    

💙💙💙💙💙💙💙
*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).

*SHAFI NA SHA SHIDDA. 16*

Ɓangaren shi ya nufa a gigice, ahanya wasu bayi suke gaidashi amma sam Yarima baya cikin hayyacin shi,ya sani sarai murabus ɗin Maimartaba dai-dai yake da ɗago fituntunu a gidan.

Tun a farfajiya ya fara ɓalle agogon hannunshi,ya shiga yana mai cire Jabba daya ɗora saman kayanshi,wurgi yayi da rigar kan Kujera tare da agogon daya fitar

Hakan shi ya ja hankalin Gimbiya Aymana.kaɗan ta kalle shi ta kauda kai.

Kaiwa ya farayi yana komowa.ya fara haɗa hannuwanshi yana taɓawa a hankali ya fara magana"Sam bana son mulki da abinda ke cikinsa,miyasa Maimartaba zai yi murabus kuma yace nine zan hau karagar shi,ba zan iyaba bazan iya mulkar mutanen gidannan ba,Miyasa sai ni bayan yana sane akwai mutane da suke jiran kujerar shi."

Gimbiya Aymana tana kallon shi ta aza ƙafa daya akan ɗaya.Wani murmushi ta fara yi kafin ta fara magana"Ba a raba harshe da haƙori!
Kowa ya keta riga tasa, ya san inda zare ya ke! In Allah ya so falke sai kayansa ya tsunke a bakin kaba! Sai wani ya rasa wani kan samu!"

Ta ida zancen tare da miƙewa tsaye,har lokacin Yarima kallon ta yake,maganganunta yake nazari.

"Mi yasa kake jin ba zaka iya mulkar mutanen gidan nan ba?kana son mulki Yarima sai dai kana tsoron sha'anin cikinta,mi yasa sai su zasu so zama Sarakuna kai banda kai?ka manta Wanda Allah ya zuba wa garinsa nono ba zai sha da tsamiya ba! Ko wane gauta ja ne sai dai ba a kai shi rana ba."

Hannunshi ta riƙe"kayi Alfahari da kanka,ka kuma amince zaka iya mulkar duk wanda yake ƙarƙashin ikonka."

Kallonta yake maganganunta na yau sunyi tasiri sosai a zuciyar shi,Yarima ya rungumeta yana aje lumfashi da ƙarfi"Ina ji kamar bazan iyaba Aymana"

Akaron farko da ya kira sunanta"Kaifa ɗan sarkine, Sarkin da babu kamarshi a nahiyarmu,da yardar Ubangijin musulunci zaka yi nasara"

Tana maganar tana janye jikinta,ajiyar zuciya ya sauke tare da komawa kan Kujera ya zauna.

****

Washe gari mai martaba ya kirayi kowa masu riƙe da masarautun gidan don sheda masu ƙudirinshi na son yin murabus,

Waziri,Galadima,sarkin Yaƙi,shantalin sarki,da sauran Yaran shi maza.

Bayan ya gama bayani kowa ya fara magana,sarki ya masu bayanin yana so ne wanda zai mulki ya samu horo daga wajan shi.

Galadima yace"Allah ya taimakeka,kayi uzuri nan da wani lokaci"

Maimartaba baiyi magana ba,Waziri yace"To Alhamdulillah dama muna jiran wannan lokacin,zuwa yaushe ka yanke za a fitar da masu son zama karagarka.?"

Yarima Saifu ya gilgiza kai"Babu buƙatar fitar da wasu sunayi,cancanta kawai za a duba,nine zan hau karagar mulki"

Sarki ya gyara zama,baiyi magana ba.

Yarima Amin ya sunkuyar da kanshi ƙasa,shi baya jin daɗin komai balle bayyana wani abu dake zuciyar shi.

Haka aka tashi daga taron sauran ɓangarorin suna murna zasu zama akan karaga.

Waziri yana isa gida ya shedawa Inna da Ayda,murna suka kama yi.

Ayda tace"Baba daga lokacin da ka hau karagar mulki zaka tilasta Yarima Amin aure na ko baya so"

MASARAUTAWhere stories live. Discover now