MASARAUTA 9

129 17 0
                                    

💙💙💙💙💙💙💙💙
      *MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA TARA. 9*

Maganar Aymana ta faranta ran kowa haka ta miƙe tana barin wajan duk wanda ya haɗu da ita a gidan sai yayi mamakin ganin yadda ƙunci ya yaye daga zuciyarta,sashen Mahaifinta ta nufa babu wata sanarwar zata gana dashi haka aka bata umarnin shiga.

Cikin Mamaki ya kalleta ganin yau babu ƙunci atare da ita"'Yata  zo zauna nan."

Ita kanta tasan ta rasa kulawar mahaifinta na wani lokaci"Baba ina mai tuba a gare ka akan gardama ga umarninka a lokacin farko,yanzu na Amince zan auri Yarima kamar yadda ka umarta."

Yasan wani lokaci tana da sanyin hali kalar na mahaifiyarta,sai dai kuma yasan basu iya juya ma abu baya ba,haka kuma basu da wahalar canza ra'ayi har ƙara Aymana tana da kafiya da jajircewa.

"Shi kenan Aymana,ki je kuyi shiri anjima ƙarfe huɗu ne ɗaurin auren,kuma ya sanar dani gobe ne zaku tafi,ina so abada umarnin shirya mutanen da zasu rakaki,a turomin Jakadiyya."

Sunkuyawa tayi tana faɗin"Saƙon ka ya isa kamar yadda kace."

Fitar Gimbiya Aymana ta yi sashenta, kuyangu ta samu a sashen aiki kawai suke mata,ta tsaya tana kallon Farida"Ayi gaggawar samar min kayan da zan saka nan da mintuna sha biyar"

Cikin bin umarnin ta bar wajan ta shiga ɗakinta,tana shirin shiga wanka taji shigowar Kaka,da wani ƙoƙo ɗauke da magani a ciki.

"karɓi kisha wannan zai maki amfani wata rana."

Aymana ta amsa ta aje gefe"Za ki sha ko ajewa zakiyi?"

"Zan sha" ta bata ansa tana shigewa ciki Kaka tabar ɗakin tana jin haushin yaran zamani.

Lokacin da ta fito ta samu Bilkisu a zaune da kaya akan gadonta,Aymana ta ajiye abun data tsane gashin kanta,ta kalli Farida data shigo da jakunkuna hannunta.

"Ki fitar da kowane"

"To ranki shi daɗe"

"Ga kaya nan na kawo maki fa,zasu yi kyau a wannan muhimmiyar ranar taki Gimbiya"cewar Bilkisu

Ɗaga kayan Aymana tayi"Na gode 'yar uwarta,amma zani barsu sai zamu tafi ina saka."

Bilkisu ta miƙa"Na barki lafiya."

"Ki jira ki taimakawa Farida wajan gyara ni,ina ga kamar aikin zai mata yawa"

Komawa tayi ta zauna tana haɗa kaya,Aymana ta shiga shafa tsadaddun mayuka da turaruka nan take ƙamshi ya game ɗakin.

Kayan suka fara miƙa mata,Bilkisu ta je gun madubin tana ɗaukar kayan kwalliyarta"Zan ɗan gyara maki fuskarki kaɗan."

"Bana buƙatar kwalliyar da zata sa agane akwai koda kwalli a tare dani"

"Ba da yawa zan yi ba"

Shiru tayi Bilkisu tayi mata kwalliya mai haske kaɗan zaka gane tayi kwalliya,wani tsadadden farin leshi ta saka,Bilkisu tana ɗaura mata ɗankwali Farida kuwa takalma take saka mata,tare da wasu sarƙoƙin ƙafa na asalin zinare.

'yan hannu da agogon hannunta masu haske da kyalli,Bilkisu zata miƙo mata Alkyabba Aymana tace"Bani maganin can na sha kar kaka ta kuma harzuƙa."

Aymana tana zaune jiran masu fita da ita,Jakadiya dasu Hajiya sai Mama sune suka zo fita da ita.

Yarima Amin kuwa lokacin yana Babbar fadar mai martaba wanda acanne ake ɗaura auren.

Duk wanda ya halarci ɗaurin Auren ya fahimci kyau da taƙama kalar ta Yarima,kowa yayi sha'awar shi a ranar.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now