MASARAUTA 45

123 20 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA ARBA'IN DA BIYAR. 45*

*SIYYA COLLECTION* 07033111950

Ki na buƙatar HUMRA mai ƙamshi? *Nemi Siyya collection.*

Ki na neman TURAREN WUTA, Na jiki, kaya, da na tsugunno, kina son zama ƴar gayu saboda ƙamshi mai sanyi ? Nemi *Siyya collection*

Ina Amarya da uwayen gida dake son dawo da martabar Auren su *Siyya collection* na da ingantatun kayan gyaran jikin amare. Akwai kayan mata masu ciko da jiki da kuma saukar da ni'ima.

Kina son fatar ki tayi laushi da santsi tare da haske mai kyau? *Siyya collection* ta tanadar maku, light cream, whiterning cream da Glowing cream kala-kala.

Sabulun wanka masu saka fata haske, ingantattu da basu da illa. ki nemi *Siyya collection*

Supplement domin ciko da inganta Breast da hips, akwai na kyaran fata xalla, ba sa da illa ga lafiyar ku.

Don gyaran gidanku da tsabtar shi *Siyya collection* tana siyar da turaren mopping.

Ku dai ku Tuntuɓeta akwai sauƙin kuɗi, haka kuma muna tura kayanmu duk garin da kuke. *Siyya collection*
Call:-09136159778
Whatsapp 07033111950.

*Page 45*

Sultan ya shiga kewar matarsa, kowa na gidan ya kasa gane kan shi, Gimbiya Ummi ta fara damuwa amma tunda ta fahimta hakan ya kwantar mata da hankali tasan idan Aymana ta dawo komi zai dai-daita.

Yau yana fada zaune, Baba Waziri ya shigo, yana son magana da shi akan Aymana don ya ga tunda ta tafi babu wanda ya ƙara magana mai muhimmanci akan takobin.

Sultan ya sa hanki da ke hannun shi ya ɗan goge fuskarshi, Waziri ya rusuna da gaisuwar munafunci, fadawa ne suka amsa da "Sultan ya gaishe ka."

Waziri ya jinjina kai ya zauna dirshen a ƙasa, tsawon lokaci kafin ya fara magana "Allah ya taimakeka, akan maganar Aymana da takobi da ta tafi dashi..."

Cikin sauki Sultan ya ɗago yana kallon shi, Waziri ya ci gaba "Ya kamata ayi wani abu akai, ga ya za'a barta ta tafi da takobin ba tare da an ɗau mata ki ba, ya kamata ta maido ta sabod..."

Kafin ya ida Wani bafade cikin fadawan da gefen Sultan ya ce "Hattara dai Waziri, Sarki ba ya kyauta ya amsa."

Waziri ya ɗago yana kallon Bafaden ya na cije leɓo, cikin jin haushin shi, Shi kuwa Sultan ko da bafaden bai yi magana ba, ba zai ce komai ba ganin waziri yana neman mayar da shi ƙaramin mutum.

Tsawan daƙiƙu goma sha biyar babu wanda yayi magana, Sultan ya miƙe zai shiga gida, hakanne ya tabbatar masa da ba zai yi magana ba.

Ɓangaren Gimbiya Ummi ya shiga, yanzu nan yake zaman shi, yayi ta fira da ita. Zaune ya sameta ya gaisheta yana kallon yadda take huci, ya ƙara matsawa gaban ta "Allah ya la'anci abinda ya ɓata zuciyar mahaifiyar Sultan."

Gimbiya Ummi ta jinjina kai "To mi ye ruwana don ka bada Takobi, Gimbiya Mai gado zata zo ta yi min tsaye da maganganun rashin hankali."

Dariya yayi yace "Haba Kamar yau ki ka fara ji, ai wannan ba sabon abu bane."

Ajiyar zuciya tayi, ganin ranta ya ɓaci hakan yasa bai sanar da ita Waziri ya je mashi ba.

Gimbiya Ummi ta ce "Ko yaushe za ka je duba su? kar Magajin gobe yayi fushi da Sultan."

Dariya yayi yana miƙawa, don baya so ta ce zai je, yana son ƙara rikita Aymana ne, yana kaiwa ƙofa ya juyo "Au Kinga na manta, Ina saratu? wannan mutanen sun zo da maganar a saka ranar Auren, na basu zaɓi sunce wata ɗaya."

MASARAUTAWhere stories live. Discover now