MASARAUTA. 22

137 22 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA ASHIRIN DA BIYU. 22*

Layin Bilkisu ƙanwarta ta kira, Bilkisu ta ɗauka suna gaisawa ta ce "Dama gobe mu ke son zuwa don taya ki shirin naɗin nan."

"Ni ba wannan ba, ki tashi ki je ki kai ma Kaka waya ina son tambayarta wani abu."

Haka suka ci gaba da waya har ta isa wurin Kaka, ta bata wayar Kaka ta amsa ta saka a kunne "Sai yau kika tuna da ni tun tafiyarki?"

Aymana tayi dariya "tsegumi ne ko Kaka?

"Dole inyi yaro har ya fiki kula damu, amma..."

"Kaka dan Allah ki saurara ni fa tambaya na kira na maki."

Kaka tace "ina jinki."

Aymana ta ci gaba da yi mata bayani tun farko har zuwa wannan lokacin Kaka ta numfasa ta ce,"Wannan wata martaba ce ake son yarinyar ta samu, kuma ba na tunanin ita ce ta tsarawa kanta, sai dai wanda yasan muhimmancin tarar sarki a ranar naɗin shi."

"Yanzu me zanyi Kaka?"

"Ki ba shi takardar sai mu saurari ranar, tun nan zamu ga ne ra'ayin shi Yarima akan yarinyar."

Haka Kaka ta ci-gaba da koyar da Aymana wasu abubuwan, sun jima kafin suka yi ban ƙwana, Aymana ta fito ta zauna a falo ta na jiran shigowar shi.

Ya ɗan jima bai shigo ba sai zuwa yamma, tana zaune kan Kujera ta ɗan zame jikinta dan hutawa, wani littafi ne hannunta akan sarauta da al'adun wasu masarautun tana karantawa.

A bakin ƙofa fadawan shi suka juya Yarima ya shigo yana sallama, Aymana ta amsa tare da miƙewa tsaye ta ajiye littafin tana ɗan saukar da kai ƙasa "Sannu da dawowa Allah ya taimakeka."

Matsawa ya yi kusa da ita, tun lokacin da aka sanar shi ne zai hau mulki ya kula da ita yadda take girmamashi wajan gaisuwa da kuma magana, sai dai yasan lokuttan da tata Izzar ne ya motsa tofa akwai aiki a gabansa.

"Fatan kina Lafiya?"

"Alhamdulillah" ta faɗa.

Sultan Amin ya zauna kan kujera hakan ne ya bata damar zama ita ma, shiru suka yi na lokaci Aymana tana son ba shi saƙon sai dai kuma bataso ya ga kamar ta ƙagara ta ba shi ɗin ne.

"Sultan zai samu abun motsa baki kuwa?" Ya faɗa yana kallonta.

Aymana ta miƙe ba tare da ta yi magana ba ta yi hanyar farfajiya, Farida ta nema ta bata umarnin kawo shayi da kayan lambu.

Lokacin da ta koma Yarima ya jingina da kujera ya ɗan saka hannu ya dafe kan shi, ta jima a tsaye tana kallon shi, tana son gane miye damuwar shi.

Farida ta shigo da tire ita da Kuyanga Aisha suka zube suna gaisuwa tare da ajewa suka fice.

Yarima bai motsa ba Aymana ta jawo tebur a gaban shi, ta mayar da tiren sama.

"Ga shayin ka"

Ta faɗa tana ɗaukar kofi ɗaya ta miƙa, Yarima ya ɗago ya amsa sai kuma ya ajiye gefe tare da ɗaukar tuffa ya kai bakin shi, duk yau bai saka komai cikin shi ba.

Nazarin shi ta yi kaɗan, ya ajiye sauran tuffa akan tire ɗin Aymana tasa hannu ta ɗauki ayaba ta ɓara tare da miƙa ma shi ya amsa ya kai bakin shi a hankali har ya cinye.

Ta gane akwai rashin cin abinci a tare da shi hakan yasa ta ɗauko za ta ƙara ma shi ya ce,"Shayi ya rage."

"Ko a kawo maka abinci? kamar akwai yunwa a tare da kai?"

MASARAUTAWhere stories live. Discover now