*MASARAUTA.*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA ARBA'IN DA HUƊU. 44*
*SIYYA COLLECTION* 07033111950
Ki na buƙatar HUMRA mai ƙamshi? *Nemi Siyya collection.*
Ki na neman TURAREN WUTA, Na jiki, kaya, da na tsugunno, kina son zama ƴar gayu saboda ƙamshi mai sanyi ? Nemi *Siyya collection*
Ina Amarya da uwayen gida dake son dawo da martabar Auren su *Siyya collection* na da ingantatun kayan gyaran jikin amare. Akwai kayan mata masu ciko da jiki da kuma saukar da ni'ima.
Kina son fatar ki tayi laushi da santsi tare da haske mai kyau? *Siyya collection* ta tanadar maku, light cream, whiterning cream da Glowing cream kala-kala.
Sabulun wanka masu saka fata haske, ingantattu da basu da illa. ki nemi *Siyya collection*
Supplement domin ciko da inganta Breast da hips, akwai na kyaran fata xalla, ba sa da illa ga lafiyar ku.
Don gyaran gidanku da tsabtar shi *Siyya collection* tana siyar da turaren mopping.
Ku dai ku Tuntuɓeta akwai sauƙin kuɗi, haka kuma muna tura kayanmu duk garin da kuke. *Siyya collection*
Call:-09136159778
Whatsapp 07033111950.*Page 44*
Gimbiya Ummi ta ƙarashe maganar tana yin hanyar fita, hankalin Aymana ya ida ta shi ainun, lallai wannan wani babban Al'amari ne yake shirin faruwa da ita.
Ta bar ɓangaren jiki babu kwari, tayi Sa'a duk mutanen gidan suna filin hawa, hakan yasa babu wanda ya ganta balle a tantance tashin hankalin da take ciki.
Ayda kuwa ado ta ci, ta saka ɗaya daga cikin kayan da ya bata lokacin haihuwarta, don yanzu ta gama da kwantar da hankalinta, tunda har Sultan ya bawa Aymana takobi shi kenan zance ya ƙare, har ta fara tunanin irin yadda zata ja ragamar mutanen gidan.
Aymana ta isa falon tana kallon Ruƙayya dake rurruga An-nur yana kuka. Ta zauna ta cikin damuwa Bilkisu tace "Wai ya ake ciki ne?"
"Zanje ma samu mai martaba, naga abin mai girma ne, ban taɓa tunanin Sultan zai min hakan ba, ga shi Gimbiya Ummi ta ce ba zata saka baki ba."
Ruƙayya ta ce "Ni dai ba shi Madarar shi ya sha, in ya so sai ki yi duk yadda zaki yi."
Aymana ta amshi yaron, su ka cigaba da fira, sai dai banda ita don ba hakanne gabanta ba.
Ta aje yaron ta miƙewarta ta fice, babban ɓangaren gidan ta nufa, ta na zuwa ta ga Mai martaba ya fito da fadawa shi.
Aymana ta zube tana gaisuwa, cikin Mamaki ya ce "Lafiya kuwa, Me ya hana ki halartar hawan Sultan?"
Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Allah shi taimake ka, dama na zo don ganawa da kai ne."
Baya ya koma yana faɗin "To fa, zo muje ciki."
Ayman ta miƙe ta bi bayanshi, suka shiga falon, ya zauna kan kujera ita kuma ta zube ƙasa, Saida ya nemi ta faɗa mashi dalilin zuwanta.
Aymana ta duƙar dakai jikin jin nauyi ta faɗa mashi komai har zuwanta wajan gimbiya Ummi.
Mai martaba ya sauke ajiyar zuciya tare da yin dariyar manya, ya miƙe ya nufi tebur da ke tsakiyar falon ya tsiyaya ruwa a kofi, yana kai kawo, kafin ya ce "To ni miye nawa anan, dole a bi hukuncin Sultan a gidan nan, shi ne shugaban kowa."
"Don Allah Baba ka taimaka min."
"Aymana na riga na saka araina Sultan ba zai yi wani abu babu hujja ba, saboda haka a bi duk abinda ya hukunta shi ne girmamawa."
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.