💙💙💙💙💙💙💙💙
*MASARAUTA.**EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA TAKWAS . 8*
*SADAUKARWA GA Oum Shuraim*
Aymana ta cigaba da Magana"Idan kuma har ba zaka janye maganar Auren nan ba,to akwai sharaɗi na biyu,sharaɗin kuwa shine idan har kana so na aureka Sai ka yarda kaine zaka maido da martabar gidanmu,mulkinmu da kuma muƙamin masarautar mu"
"Me hakan yake nufi"Ya bata amsa yana nazarinta.
"TAKOBIN Gidanmu da take hannunku,dole ya dawo hannunmu,kuma kai ne zaka maido wannan muƙamin da kanka,in har kana so na aureka."
Miƙewa yayi yana jin wata izza tana fuzgar shi jin yau ana bashi umarni,kamar aike haka yake jin yanayin maganarta,hakan ya tafarfasa zuciyar Yarima.
Yanzu ne ya tabbatar tana wasa da sarautar shi,tana tunanin shi baya son ɗaukakar tashi masarautar.
Gyaran murya kawai yayi, sakin fuskar da yayi a farko ya kau,Azuciyar shi bai san me Aymana take jin tana taƙama da shi ba,idan mulki ne ya sani a tasu masarautar aka fi mulki da nuna izza amma a masarautar su Aymana ya gama fahimtar itace kawai ta ɗauki kwatankwacin Izza da ya kamata duk ɗan MASARAUTA yayi.
Baiga laifin ta ba hakan ya sa ya ɗaga laɓɓan shi da kyal ya furta"kee!!! ina so ki sani ni ban kasance wanda nake bin umarnin wanin da bai kai nabi umarnin sa ba,kamar yadda na amincewa Sarki ba zan taɓa canzawa ba."
Daga faɗar haka ya fice cikin takon ƙasaita,su duka biyun kallo suka bi shi dashi,Bilkisu ta matso gun Gimbiya Aymana.
Fitar Yarima kuwa ɓangaren Sarki ya nufa,gaishe da shi fadawa suka fara yi,sunyi mamakin ganin fuskar shi babu walwala kamar yadda suka saba.anan ya sanar yana son ganin mai martaba,aka sanar da Sallama,sallama kuwa ya isar da saƙon agun Sarki.
Sarki jin ance Yarima ne hakan yasa ya bada umarni ya shigo.
Yana zaune saman kujera Yarima ya sunkuya ya yi gaisuwa tare da faɗin"Allah ya taimake ka nazo akan maganar auren ne ina son komawa gida cikin 'yan kwana ki,lokuttana ba su da tsayi a yanzu,gaya Maimartaba ya fara damuwa akan rashin komawata."
Tsawon mintuna goma Sarki baiyi magana ba yana nazari akan maganar Yarima,cikin rashin tsammani Sarki yace"Zan ɗaura Aurenka gobe,zan sa asanar da Mutanan TORO."
Yarima bai ji komai ba don yadda ya fara jin izzarshi hakan bazai sa ya nuna damuwa ko razana ba"Ranka shi daɗe,ina godiya sannan ina neman wata alfarmar akan Kar a sanar ma mutanen Toro,zai fi naje da matata don bar ma su abin mamaki kuma hakan zai kawar da tunanin su na son sai an ƙara wani lokaci domin suma su halarci taron.ina mai neman Alfarma."
Yarima ya yi saurin yanke hukunci ne,don sanin idan har wasu daga gidansu suka san zai yi Auren ba lallai ne hakan ya faru ba,don Sarkin TORO ya damu akan rashin Auren Yarima,gaya wasu daga ƙannan shi ko wanne da auren shi,hakan yasa hankalin mahaifiyarshi baya kwance,itama gurin ta yayi auren saboda shine Mai jiran gado.
Haka suka tashi a wannan zama, lokacin daya koma sashen shi anan ya bawa fadawanshi umarnin haɗa nasu kayan don sun kusa wucewa.
Kamar wasa Al'ummar Darul-Bilyam suka tsinkayi maganar ɗaurin auren Aymana da Yarima Amin.
Aranar kuka baya musaltuwa agun Aymana,Durƙushe take gaban mahaifiyarta,baki take bata akan Auren.
"Wannan shi ne asalin darajarki Aymana,kiyi biyayya kiyi aurenki,Ni ina mai alfahari zaki koma cikin Babbar masarautar nahiyarmu,masarautar da babu irinta a duk kusa damu,abin jin daɗin ma wata rana kece matar Maimartaba ga Masarautar TORO masarautar da suke da TAKOBI,ke kanki kinsan yadda masarautun dake kusa damu suke son mallakar wannan Mulki ya koma gunsu."
Aymana ta sauke ajiyar zuciya,ita kanta a zuciyarta bawai bataso bane,domin tana so taga ta ƙara samun daraja,amma kuma tana kishi tare da son mallakar TAKOBI,tana ganin babu wani muƙami daya wuce ta dawo itama taga masarautar mahaifinta ta zama ita ce babbar masarauta kamar TORO.
A take ta tuno maganganun Hajiya da Mama da kuma sauran Yayyenta akan tayi Auren Amma ta je da sharaɗin dawo da TAKOBIN da rashin shi yayi sanadiyar ƙanƙancin masarautar su.
Kaɗa kai Ayama tayi ta kamo hannun Ummanta"Umma tabbas ke uwa ce ta gari,har kullum zanyi alfahari dake,amma ni zan zama matar sarki da take da Izza da mulki,zan je Toro kamar yadda Mai martaba ya umarta,amma wata rana dole zan dawo da martabar mu."
***
A wani ƙaton mazaunin su,Mama,Nene,Hajiya,Yarima Shuraim da Yarima Faruk kowanne ranshi a ɓace yake jin kalamin da akace Yarima yayiwa Gimbiya.
A wannan lokacin ya zama dole su nuna isa akan Umma da Kaka,da suke goyon bayan Auren.
Kowa ya gama bayanin shi da kuma nuni akan darajar Takobin da suke rigima kanta.
"Idan har shi Yarima Amin zai nuna kishi akan masarautar su,Umma taya zaki goya baya Aymana ta aure shi tsakani ga Allah,ya zama dole muyi kishi mu dawo da mulkinmu"cewar Nene dake kallon Umma.Umma ta girgiza kai"canza ra'ayin Maimartaba ba ƙaramin abu ba ne a garemu,amma zancen Yarima ya firgitani,banyi tunanin zai nuna iko akan Aymana ba."
Taɓe baki Hajiya tayi"Dama ke ce kika ɗauka zai zama kariya a gare ta,amma ni nasan zata zama kamar baiwar da ba zata taɓa samun 'yanci ba a masarautar Toro"
Mama tace"Ni dai kishina akan yaran gidan nan ne,idan har TAKOBI ta dawo hannun mu,to fa babu wanda ya isa ya ja da Darul-Bilyam."
Yarima Shuraim yasan shine namiji mai jiran karagar hakan yasa ya tabbatar kamar shi ake shirin yiwa yaƙi"Dole Aymana ta je gidan kuma ta dawo mana da TAKOBIN mu"
Umma ta kalli Aymana"Na baki Umarnin dawo da masarautarku kamar Zinarin da aka tsuma wanda darajar shi zai linka darajar kowane,ta hanyar dawo da TaKOBI a gidan nan."
Bilkisu ta zaro ido jin Umma ta amince da zancen su"Haba Umma yanzu kin amince Aymana ta je Toro ba don Auren kirki ba sai don wata manufar ku ta...."
Wani wawan mari Umma takai mata"Daga lokacin da bamuda wata daraja,ba zaki taɓa kiran kanki yar sarkin data fito daga babbar masarauta ba."
Kaka ta kalleta"Yanzu marinta kikayi saboda ra'ayinki ya canza.Nice ya kamata na ji haushi,ni da na rasa Ɗana da nafi ji dashi lokacin da TaKOBI ta bar gidannan shine sanadiyar Rasuwar mahaifin Sarkin yanzu,saboda baƙin ciki."
"Amma kaka duk da bakin cikin rasa yaron ki hakan baisa kikaji kina son ganin dawowar Masarautar nan ba"
Kaka ta miƙe tana jan hannun Bilkisu"ki saka masu ido sunyi nisan da ba sa jin kira.
A ƙofa suka yi kiciɓus da Kawunsu Aymana wato ƙanin Maimarta ba,wanda shi ne yake binshi,saidai uba suka haɗa amma kowa da mahaifiyar shi.
Shima Kawu Harun ya so mulkin masarautar Bilyam wanda bayan baiwa Baban Aymana sai da sukayi gaba da shi,don shi yaso ya zama Sarki,kuma ko yanzu yana da ƙudurin zama sarkin hakan yasa yake goyon bayan Aymana ta dawo da TaKOBI,don yayi mulkin babbar masarauta.
Ciki ya shiga yana kallon su"Aymana ki tashi ki koma ciki ki fara shiri kuma ki saka a ranki lokacin ɗaukakar masarautarku yazo,kuma ke zaki ɗaga darajar gidannan."cewar Kawu Harun.
Aymana ta miƙe da ƙasaitacciyar tafiyar ta takon ta zuwa gaban iyayen nata"Na gode da goyon bayan ku in sha Allah nice sanadin farin cikin gidan nan...
*Muje zuwa yanzu muka fara*
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.