MASARAUTA 48

145 21 1
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).

*SHAFI NA ARBA'IN DA TAKWAS. 48*

Ya kuma mayar da kanshi a ƙasa tare da fara magana "Allah shi taimakeka, na yi hakan ganin cancanta da jajircewa da Aymana take yi akan kowa da ke ƙarƙashin ta, a yanayin hamayya da ake akan takobin hakanne ya sa nake ganin shi ne abu mai daraja da zan sadaukar mata, na nuna ƙauna akanta da kuma wanda take tare da shi." Ya sauke maganar da sanyin murya.

Mai martaba ya kalle shi, zai fara magana Sultan ya fara murza yatsun hannuwan shi "A iya sanin misalta soyayyar da nake wa Aymana ba ta musaltuwa, idan har ba zan iya bata abinda ta saka aranta ba ina ganin babu cikar soyayyar, sannan kuma hakan zai sa ta rasa kwanciyar hankalin zaman takewarta."

Ajiyar zuciya Mai martaba yayi ya miƙe tsaye tare da fara tattaki, hakan ya sa su duka suka bi shi da kallo, wani yanayin farin ciki yake shigar shi, duk kawaici irin na Sultan yau gashi gaban shi yana faɗar yana son Aymana.

"Aymana!"

"Allah ya baka nasara."

"Sultan!"

"Allah ya ja zamanin ka."

"Na yi shirin sanar da ku tarihin masarautar Bilyam, amma ina ga kamar ba ku da lokaci, za ku iya tafiya wani dawowar sai na gaya mu ku idan ran...

"Don Allah Baba ka sanar damu ka ga ..."

Sultan ya katse ta tare da faɗin "Allah shi taimakeka muna da lokaci."

Mai martaba yayi murmushi, ya san dole za su zaƙu akan son jin tarihin.

Hakan ya sa ya zauna ya kalle su tare da fara magana " Asalin masautar Bilyam tana ɗaya daga cikin manyan masarautun da suka riƙe mulkin dauloli da wasu yankuna na Nahiyarmu.

Masarautar ta riƙe mulki na tsawon ƙarni biyu zuwa Ukku, Masarautar Bilyam tana da ƙarfin mulki da iko akan duk masarautun Nahiyarmu, hakan ya sa babu wata masarautar da ta isa ta girgizata ko ta ja da ita akan yaƙi ko wasu al'adun sarautar da ake gabatarwa a Nahiyar.

Izza, ƙarfin mulki da ikon Masarautar hakan ya sa duk cikin al'ƙaryoyi da dauloli babu daular da ake tsoro da shakku kamar ta, Saboda aduk lokacin da aka ce za a yi yaƙi ko wani fito na fito, babu masarautar da ta kai Darul-Bilyam.

Domin kuwa idan aka ce za a yi yaƙin to masarautar ta kan fita da Dakaru sama da milyan arba'in da ɗoriya, idan kuwa Dakarun suka fara yaƙi za ku yi mamakin domin ba sa ji ba sa gani, su kan yi tsawon awannin Arba'in da takwas zuwa saba'in da biyu suna fafatawa.

Wannan dalilinne ya ƙarawa masarautar ƙarfin mulki da ƙarfin Izza, Sai ya zama mafi girman Takobin da take tasiri a masarautar a wajen yaƙin ita ce takobin da Sarki Bilyaminul Anwaruddin ya ƙirƙireta."

Mai martaba ya ja dogon numfashi, tare da yin shiru na wani lokaci, Sultan ya ƙara matsawa gaban shi cikin zaƙuwa da kuma son jin abinda zai zo a gaba.

Aymana ta ce "Allah ya ba ka nasara, waye Bilyaminul Anwaruddin?"

Ya yi Murmushi jin yadda ta ke sauri, Sultan ya miƙe ya nufi kan wani teburi ya tsiyaya ruwa a kofi yazo ya ba Mai martaba, Mai martaba ya kurɓi ruwan tare da aje kofin.

A hankali ya ɗaga baki ya ci gaba "Takobin an ƙorƙireta da sinari wanda a lokacin da turawa suka azata a mizani tare da duba farashin Takobin ta kai darajar Dalolin Miliyoyin kuɗin na amurka.

Wannan darajar Tokobin, yasa ake ganin takobin tana da wani ƙarfin sihiri na musamman, sai dai kuma ba haka bane, Sarki Bilyaminul Anwaruddin ya ƙirƙira takobin ne saboda fuskantar abokan gaba.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now