https://chat.whatsapp.com/F74uYH31PsM7qUyc1CbZvV
💙💙💙💙💙💙💙💙
*MASARAUTA.**EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA SHABIYU. 12*
Yarima ya ɗan tsaya yana kallon Aymana"Fatan babu baƙunta a tare da ke?"
"Sam ina jin kamar ina gidanmu,saboda kusanci da na ƙarayi da wani mallaki nawa."
Yarima ya girgiza kai,azuciyar shi yayi tunanin ba zata daina maganar mallakar Takobi ba kenan.
"Shi kenan,ki huta lafiya,na zo ganin lafiyar ki ne"yana maganar yana miƙewa don barin ɗakin,Aymana ta bi bayan shi da kallo har ya ɓace kafin ta koma ta kwanta.
****
Ƙarfe goma na safe kuyangi suke kai kawo a harabar ɓangaren,Farida tana binsu da idanuwa,sai maganganun su dake ɗaukar hankalinta,duk akan Yarima Amin ya shiga ɗaki yau,musamman masu shekarun cikinsu,wanda ta fahimci suna jiran umarnin shi don bada shedi ga al'ummar gida.
Ta hanyar nuna zanin gadon da suka ɓata kokuma duba lafiyar Gimbiya Aymana.
An ɗauki lokaci Farida ta shiga ciki a tsaye ta samu Aymana tana kimtsa kanta"Ya ke Uwar ɗakina ina son sanar dake jiran bayyanar wani abu na shirri da mutanen gidan nan suke jira tsakanin ki da Yarima."
Da sauri ta ɗago"Har yanzu suna bayyanar da hakanne?"
"Gaskiya domin jira suke kawai suji."
"Babu wani abun baiyyanarwa,kar in ji ko kalma ɗaya daga bakinki akan mu,ki gyaraman ɗaki ki fice kawai."
"To ranki ya daɗe"
Abin ya daɗe a zuciyar Aymana haka nan kawai ta kauda maganar,don tasan hakan ma bazai faru tsakanin ta da Yarima ba,irin wannan lokacin da Babu wata soyayyar juna a tsakanin su.
****
Ummi ce zaune a ɗakinta,ita kanta son jin sanarwar Yarima ya fasa kwai a gidan take,domin kuwa wannan shine nasarar su,hakan shine tabbacin zasu ɗau hanyar kawo Magaji a gidan.
"Aje a haɗa kayan karin kumallo ga Yarima da Gimbiya."ta ba wata Baiwa dake yi mata tausa umarni.
"An riga anyi komai tun ɗazu,na bar wajan ana shirin kai masu abincin."
Ummi ta kaɗakai alamar gamsuwa.
****
"Nace kije kema ki zama a cikin bayinta,ina son jin duk wani bayani nata,idan kika kuskura naji wani abun da baki sanar dani ba to lallai zaki haɗu da fushina."maganar Ayda kenan ga Kuyangar dake mata hidima.
Hassatu ta miƙe"Da yardar Allah komai za ki ji daga gareni."
Ɓangaren Aymana yarinyar ta shiga itama tana son jin komai daga wajan sauran ƴan'uwanta bayi.
Farida ta fito a falon fa samu bayi suna rige wajan shigowa jera abinci hakan ya faru don ganin kwam.
Tsaye tayi tana kallonsu,Hassatu ta zo taja hannun Fadima suka fice."Ke me faru nifa Ayda ce tace nazo naga komai."
"Har yanzu babu wani bayani,nima Hajiya Mai gado ce ta sani jiye mata komai na gidan"
Hassatu ta ja tsaki"Muje kawai"
Sai ƙarfe goma shaɗaya Yarima Amin ya fito anan ya samu Farida zaune,ita da Hassatu,zubewa sukayi gaban shi"Barka da safiya Ranka ya daɗe."
Bai amsaba ya samu waje ya zaune saman kujera,yana kallon abinci da aka jera ya maida hankalin shi kan Farida"Uwar ɗakin ki ta tashi ne?"
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.