MASARAUTA 31

149 23 1
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*Alhamdulillah jikina yayi sauƙi, Na gode sosai da Addu'o'in ku, Naji daɗin yadda kuke neman Littafin MASARAUTA sai yanzu ne na gane ana duba littafin, inshallah zaku ci gaba da ganin littafin kamar kullum.*

*SHAFI NA TALATIN DA ƊAYA. 31*

Aymana ta ji wani tashin hankali da maganganun Sultan "Wannan wace irin rayuwa ce Sultan?"

Shiru yayi tare da jingina jikin shi ga kujera "Wanann shi ne abinda ya faru, wanda na san ba kowa ne zai gane hakan ba Aymana. Allah ya gani ina tausayin Abul."

Hawaye ne suka gangaro daga idanuwanta, ta saka hannu tana gogewa, lallai ta san sun saka rayuwar yaron a cikin hatsari, ta juya ta kalli Sultan "Ba a jiye su, don Allah a fara nema mashi sauƙi tun kafin abun ya zama wata matsalar kuma."

"Zan saka shi a Addu'o'i na, ina sha Allah."

"Ameen" ta amsa tare da miƙewa ta matso mishi da kayan lambu, ta sa hannu ta ƙara gyara fuskarta, kafin ta yi hanyar barin wajen, ido kawai Sultan Ameen ta bita dashi.

***
Sai da aka ƙara ɗaukar lokaci, kafin maganar rashin lafiyar Abul ta baiyana a gidan, Ayda ce tsaye gaban Sultan tana kukanta, tsawon lokaci bai mata magana ba "Taya za a ɗau ciwo a ɗorawa yarona, wannan ai sharri ne."

"Ayda!"

Ta ɗago ta kalleshi "Ke baki kula da Abul ɗin bane ko me?"

Sarai ta sani amma bata san ta ina zata ɓullowa lamarin ba "Ai nasan dole sai Abul ya ga taskun rayuwa a gidan nan, musamman ga mutanen da suka zo don neman shiga da kuma..."

Wata irin tsawa Sultan ya daka mata, saboda ya fahimci tana so ta ce Aymana ce tayiwa yaronta sihiri, abun ya baki mamaki wai su ba zasu taɓa yin hankali ba. "Sai yaushe hankali zai shige ki ne, ba ki ta lalurar yaron ki, sai ma neman abin abun ki ke?"

"Amma ai..."

Kafin ta ida Sultan ya nuna mata ƙufa cikin zafin zuciya ba tare da yayi magana ba, ta gane ran shi ya ɓaci Ainun, hanyar fita tayi tana mai kuka.

Kuyangin dake wajen suka bita da kallo tare da fara gulamace-gulmace, ɓangaren  Waziri ta nufa ta same shi tsaye yana kai kawo Ayda ta fasa kuka mai tsuma zuciya, Waziri ya bita da kallo "Dama baƙin ciki ake kar yaro na ya gaji sarauta shi yasa aka yi mashi haka."

"Ayda ba da ke suke yi ba, wannan faɗan da ni suke wallahi, yanzu yaron da muka ɗaura burin mu akan shi shi ne sukayiwa haka."

Inna ta aje tire ɗin hannunta "Amma wallahi ban yafe ba, kuma idan har ba a ɗau mataki ba ..."

Gani tayi Waziri yayi zama dirshen a ƙasa ya dafe kai, yana karanto salatin da babu shi a zuciyar shi, wasu zafafan Hawaye suka biyo kuncin shi "Duk daɗewar da nayi cikin son ganin na jagoranci gidan nan har yau ban samu sa'a ba, wallahi wallahi wallahi na yi alƙawarin sai dai ayi biyu babu." Yayi maganar tare da miƙewa ya nufi cikin gida.

***

Jakadiyya ta yi shewa tana mai kallon Gimbiya Mai gado "Me na faɗa maki? Wannan kaɗan ma suka gani, ai sama tayiwa yaro nisa."

Gimbiya Mai gado ta buga cinya ciki tana sakin shu'umin murmushi "Sai dai abi wani sarki, amma nan dai zance ya ƙarare, ba ki ga Waziri har ya fara tada kafaɗa ba, wai shi jikanshi zai yi mulki duk daɗewa.

"Allah ya taimakeki ba zasu taɓa samun nasara ba."

***

Sultan Amin ne zaune kan kujera ɓangaren Gimbiya Ummi, Aymana kuwa tana daga gefen shi, shiru babu wanda yake magana har shigowar Gimbiya Ummi, gaisheta sukayi ta zauna tana amsawa tare da faɗin "Ko Sultan ya dubo jikin Gimbiya Ayda?"

MASARAUTAWhere stories live. Discover now