MASARAUTA 34

144 22 4
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA TALATIN DA HUƊU. 34*

Ta riƙe hannunshi suna zama kan kujera, binta yayi da ido sosai kyawun jikinta ya ƙara fitowa hasken fatarta ya ƙara bayyana, jikinta ya ƙara laushi, ta ƙara mulmulewa abinta, hakan yasa ya tabbatar ƙasar ta amshe ta.

Ana zuwa ɗaukar su suka nufi Jedda tun a hanyar zuwa masauki Aymana take kallon yana yin garin ta gilashin mota.

Sultan yasa hannu yana riƙo hannunta, Aymana ta kalle shi tana riƙe nashi hannun itama, ko wanne da abunda yake saƙawa a ranshi.

Daga zuwansu wanka sukayi, tare da cin Abinci, Marece nayi Sultan yana shirin zama don hutawa Aymana ta hana shi don dole ya tashi suka fice.

*Dhaban marine park* suka nufa, wani babban wajan shaƙatawa wajen yana da kyau sosai, akwai ɓangaren wasanni da kuma wajan wasan yara, sosai Sultan ya maida hankali wajan kallon motocin wasan yara da kuma   yadda iska yake sanyaya wajen.

Aymana ta ja hannun shi zuwa wajan wata kujera, suka zauna, Sultan ya kalleta "Sam wajen nan yafi dacewa da suwa da yara, kasancewar komai na wajen don jin daɗin yara ne."

Murmushi Aymana tayi, ta maida kanta akan kafaɗar shi tare da saka wani abin motsa baki tana sha "Hakan yana nufin wata rana Sultan zai so da Yaran shi."

Hannu yasa yana shafa kafaɗarta, sai dai baiyi magana ba, haka sukayi hotuna sosai.

Washe gari a *Masjid Al Rahama* sukayi sallar la'asar, Masallaci ne da ke tsakiyar  wani kogi wanda wajan yana da sanyi da kuma daɗin zama.

Gewayawa suka yi wajan ruwan bayan sun fito daga masallacin. Aymana ta tsugunna tana saka hannuwanta a cikin ruwan, Sultan ya kalli yadda rigarta take shiga ruwan ya duƙa tare da saka hannu yana fitar mata "Kin ga zaki jiƙa kayan ki."

Ɗagowa tayi tana kallon shi taɗebo ruwan sosai tana watsa mashi tana dariya, Sultan ya kalli yadda ta jiƙa mashi kaya yace "Ni kika yiwa Haka ko."

Yana maganar yana ɗibar ruwan Aymana ta miƙe tana ɗan gudunta Sultan ya bita baya, Sai dai lokacin da ya kamata ruwan da ya ɗiba a hannun shi sun zube.

Dariya tayi mashi, Sultan ya harareta iska yana ƙaɗa mayafin dake jikinta har gashin kanta yana fitowa.

Hannu yasa yana gyara mata gashin tare da rungumeta "Yauwa yanzu ne dai-dai lokacin da zan rama."

Numfashi take saukewa sosai "Allah ka barni, ko gudun da ka saka ni ai ka ram..."

Kafin ta ida Sultan ya haɗe bakinsu, yana harɗe hannuwanshi bayanta, gaba ɗaya ya kashe musu jiki, ta saka hannunta tana riƙe shi jin kamar ƙafafun ta ba zasu iya ɗaukarta ba.

Sai da suka kwana biyu suna yawon shakatawa a Jedda. Yanzu ma shiri take yi sosai lokacin marece yayi lis, samun shi tayi falo zaune da wasu kaya marasa nauri, wandon iyakar shi guiwa, sumar kanshi tasha gyara sosai.

Aymana ta zauna tare da shafa sumar ta ce "Allah ya baka nasara, na ga baka shirya ba."

Maido hankalin shi yayi akanta, doguwar riga ce mara nauri, tana da maɗauri a tsakiya, sai wani siririn mayafi data ɗora, ta mashi kyau  sosai "Ki canza kaya dai, ba zanje dake a haka ba."

"Au ni na fita da kai jiya da wando iyakar shi ƙasan guiwa."

Dariya yayi ya kama hannunta suna miƙewa "Yau ina so mu huta a gida."

MASARAUTAWhere stories live. Discover now