MASARAUTA 40

98 15 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA ARBA'IN. 40*

Kuka Aymana ta sakar mashi, Sultan ya ɗagota ya zaunar da ita akan kujera, tare da raɓata a jikin shi, tsawon lokaci tana sauke ajiyar zuciya, sunkai daƙiƙu goma sha biyar babu wanda ya kuma magana.

Sultan kuwa a zuciyar shi ya gama ƙaryata ta akan cewar tayi abinda ta yi don cikinta, tabbas yasan tun kafin cikin  tana son aikata hakan, tayi amfani da cikinne ta hanyar kare kanta.

Ɗago kanta yayi daga kafaɗar shi, a bisa mamakin shi sai yaga bacci take yi, hakan yasa ya barta, don yasan tabbas bata yi bacci ba duk daren ranar.

Sallar la'asar aka fara kira hakan yasa ya fara ƙoƙarin janyeta, Sai lokacin take ƙoƙarin gyara kwanciyarta, cikin mamaki take kallon shi tare da murza idanuwanta.

Ta gane anan tayi bacci, hakan yasa ta kai hannunta akan kafaɗar shi, lokacin ta ga har ya cire rawanin kanshi "An fara kiran Salla fa."

"Duk yau ban yi wanka ba, tun da zan fita Asuba."

Aymana ta kalli jikinta, ya gane abinda take nufi, hakan yasa ya ja hannunta suka shige ciki.

Lokacin da Sultan ya fito kowa ya kama gulma, wai tun ɗazu yake ciki amma har yanzu bai fito ba.

A ƙofa ya samu Jakadiyya ya ƙara bata umarnin kar wanda ya shiga wajan Aymana, a tunanin su yana ƙara mata wani hukuncine, shi kuwa yayi hakan ne don kar wani ya shiga ya gaya mata babu daɗi.

Lokacin Da aka fito salla, Mai martaba yake sanar da shi Waziri ya kawo mashi zancen wani bafade da yace an bashi  wasiƙa daga Bilyam ya kawowa Aymana, ya sanar da abinda ke cikin takardai.

Wannan lokacin a tsaye suka tattauna, Sultan yana son zuwa wajanta dan tabbatarwa, amma kuma Mahukunta sun zo don zama da shi, haka ya hakura, yaje sukayi wannan zaman, shi dai kawai yana amsawa amma yana cikin tashin hankali akan cewar an yi Aike  ana son ganin Sarkin Bilyam.

Sai dare ya samu kanshi, hakan yasa ya nufi sashen ta, ya samu jakadiyya ta shigar mata da abinci.

Wannan lokacin jakadiyya bata jira Sultan ya bata umarnin fita, Sultan ya nufi Aymana "Bana da idanuwan kallon Mai martaba gobe, ba na jin zan iya kallon shi akan ina tuhumar shi da Aikata laifi."

Aymana ta ji mugun tashin hankali da tsoron mahaifin ta,  hawaye suka fara gangaro nata, Sultan ya duƙa yace "Ina takardar da aka kawo maki lokacin da Tsohon Sarki yaje..."

Aymana ta zaro ido, Sultan ya ɗaga mata kai "Nifa ba a kawo min komai ba."

Yasan hakan zai faru, ita kuwa tasan idan har Sultan ya ga takardai, zai tabbatar ba don cikinta tayi hakan ba.

Ya san ba zata taɓa nunawa ba, haka ya miƙe ya fara shiga ɗakinta, Aymana ta bishi baya, ta samu yana ta neme neme, ganin ya ɗauko akwatin da ta aje takardai hakan ya sa ta riƙe shi.

Sultan ya juyo "Wai ba zaki bar ni ba, wallahi zan hukunta ki Aymana!"

"Kar ka buɗe Sultan."

Har ya riƙe ta zai tureta sai kuma yayi tunanin ba ita ɗaya bace, ajiyar zuciya yayi ya ce "Sakar ni na ce."

Kuka ya saka mashi tana maƙale shi, sam bai taɓa ganinta cikin ruɗani irin hakanba, ya fara ƙoƙarin buɗewa, Aymana ta kama turashi suka kama kokoyi, karo yayi da gado, hakan yasa Aymana ta tura shi ya saki akwatin ƙasa marfin akwatin ya ɓalle abubuwan ciki suka zube.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now