MASARAUTA 25

125 19 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA ASHIRIN DA BIYAR. 25*

Daidaita nutsuwarta tayi ta hanyar sakin murmushi tare da basarwa, domin ba ta son yasan me ya faru tsakanin ta da Ayda.

Haka kuma tun shigowar ta, shakku ya shigeta tare da tsoron fuskantar Sarki Amin da maganar Takobin da  ta yi niyar yi ma shi.

Ta zauna gefen shi tare da bashi amsar tambayar da ya yi mata na dalilin damuwar fuskarta  "Na samu ɓacin zuciya ne daga Farida, amm..."

"Yau me ya shiga tsakanin ki da Kuyangar da ki ka fifita fiye da sauran hadimanki?"

"Allah ya huci zuciyar Sultan, kuskure aka samu, amma hakan ba zai sake faruwa ba, a tunanina na hukuntata daidai da laifinta." Ta ba shi ansa cikin salon kissa.

Sultan ya yi murmushi, ba tare da ya ƙara magana ba, Aymana ta sunkuya tare da sakin murmushi mai sauti, wanda har sai da Sarki Amin ya ɗago ya kuma kallonta.

Cikin salo take son ɗaga baki tayi magana, amma farin cikin data saka a fuskarta yana neman hana ta faɗar maganar bakinta.

Ta kuma murmusawa tare da faɗin "Allah ya taimakeka Ina jin kamar babu kalaman da zanyi amfani dasu wajen shigar da taya murnar samun Magaji da ake shirin yi a gidan nan."

Shiru na wani lokaci, Sarki Amin ya fara nazarinta ta ɗago a karo na biyu tare da faɗin "Na yo tattaki ne don taya murnar samun Magaji, ina taya ka murna!"

Bai yi magana ba amma yaji daɗin hakan daga ɓangarenta, wata zuciyar tana mai raya mashi ina ma wannan Juna biyu dake tare da Ayda akan Aymana ne.

Ganin bai yi magana ba ya sata yin shiru Sarki Amin ya kuma tambayar ta "ko da wata buƙata ne?"

Jim tayi ba tare da tace komai ba sai kuma ta tuna da son zuwa gidansu da take son yi tace "Ina mai neman umarnin zuwa Darul-Bilyam don ganawa da ahalina, na kuma gaishe da Mai Martaba."

Ya daɗe bai motsa ba, tabbas ta yi juriya na daɗewar da tayi ba tare da taje masarautar su ba, ya san lallai tana da buƙatar ganawa da su.

"Yaushe ki ke son tafiyar ne?"

Aymana ta ƙara muskutawa cikin girmama tambayar  ta ce "Da izinin ka komai zai gudana."

Ita har kullum tana nuna daraja ga Sarki, tana ba shi muhimmanci da girmamawa a wajen kalamai, tana amfani da salon maganar da sam Ayda bata da hakan.

"Na ba ki zaɓi."

Ta ɗago "Ina son tafiyar gobe."

Shiru yayi kafin ya ce "Zan sa a shirya tafiyar ku da mutanen ki, Allah ya dawo da ku lafiya."

"Amin, na gode!"

***

Fitar Aymana da ga turakar Sarki Amin tayi ɓangarenta, tare da zama tana tunanin miye abinyi don bayyana murnarta na samun cikin Ayda.

Wasu akwatinan ajiyar ta ta fara jawowa, ya zama dole ta ƙara rikita mutanen gidan.

Wasu kaya ta kuma fiddowa na sarauta, Awarwaron zinari da sarƙar su, abin ƙafa da kuma ɗankunnan su.

Ta miƙe ta jawo wani akwati ta fiddo wani munduwar zinari, ta ɗauko wani tsadadden farin Yadin Karan-miski, ta ɗaga karan-miskin ta na murmushi sanin darajar shi a masarauta, yana da daraja sosai domin kuwa sai sarakuna ne su ke amfani da shi ada.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now