MASARAUTA ENDING

226 14 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA ƘARSHE*

JINJINAR BAN GIRMA GAREKI *RAMLAT MANGA MAI DAMBU* na ji daɗin kulawa da halarcin ki, Allah ya bar abinda ya haɗa.

YABO GAREKI: UMMYN YUSRA. Allah ya bar zuminci.

BAN MANTA DA KE BA: HAJARA AHMAD MAIDOYA OUM-NASS, ina godiya.

GODIYA GAREKA KAMAL MINNA.

SADAUKARWA GAREKU ƊAUKACIN MARUBUTAN ƘUNGIYAR EXQUISITE WRITER'S ASSOCIATION. Allah ya kara ɗaukaka.

🔚🔚🔚🔚

Ta haɗa hanta da ƙafafuwanshi tana kuka "Na san kana aikata afuwa ga mutanen da suke ƙarƙashin ka, duk da ban kasance daga jikin bayi masu ƙananun laifuka ba ina neman gafararka akan abinda na Aikata gareka da kuma ahalinka."

Sultan ya kasa ko motsi daga inda yake, Aymana kuwa wani tausayin Ayda ya shigeta, "Na san ban cancanci zama matarka ba Sultan, na san baka so na, ka yiwa Mai martaba biyayya ne akan aurena, bayan hakan bana tunanin zaka iya tarayyar Aure tare dani Sultan wannan dalilinne yasa na karɓi layu daga hannun Waziri na saka a makwancinka hakan ya sa ka iya tarawa da Ni a daren farkonm...

Wata iriyar tsawa Sultan ya daka mata tare da saka ƙarfinshi ya janye ƙafarshi, gaban shi yana wani irin lugude kamar ƙirjin shi zai tsage zuciyarshi ta fita.

Ayda ta ja baya tana kuka, Aymana lokacin ta tsorata ga tashin hankali da take tare da shi, Ayda ta ci gaba "Dama na sani Sultan, na san laifukana ba zasu samu afuwa ba, hakan yasa ba zan iya jero su ba, sai dai ina mai neman afuwa tare da alfarma a gareka."

Aymana ta durƙusa gabanta tana faɗin "Ayda na sani Sultan ya yafe maki haka...

"Aymana!"

Sultan ya kira sunanta, Ayda ta fashe da kuka, Aymana ta sunkuyar da kanta tare da faɗin "Lallai lamarin mai girma ne, sai dai babu wani lafin da babu afuwa akanshi Sultan, Ayda tayi laifi kuma ta tuba, ka amshi tubanta."

Ayda ta riƙe Aymana "Ke ɗin ta dabance Aymana, kina da halin kirki tabbas ke ce mata tagari a wajan Sultan, ke ce zaki zama uwa ga yaranshi."

Ta miƙe ta nufi Sultan "Yafiyarka nake nema, ba don son ƙara kasancewa tare da kai ba, ka gafarceni."

Ta yi maganar tana nufar kan tebur ɗin shi ta ɗauko takarda da abin rubutu "Wannan shine hukunci na, babu amfanin zaman na gari, da mugu, don Allah ka rubuta min s...

Aymana tayi saurin tararta tana fizge takardar tare da yin wurgi da ita "Wa ya ce miki Sultan baya son ki? Ke fa jinin sa ce, kin manta akwai jininki da yake yawo a nasa jinin, sam babu rabuwa tsakaninku, Sultan ya yafe maki Ayda."

Sultan ya fara yiwa Aymana wani kallo, wanda alokacin yanayinta ya fara sauyawa zuwa salon kishi, ta danne ne kawai, Aymana ta kalli Sultan "Ka ce wani abu mana Sultan."

Shiru na wani lokaci kafin ya ce "Duk hukuncin da kika zartar yayi Aymana, na yafewa Ayda, amma tunda tana buƙatar s...

Cikin sauri Aymana ta riƙeshi tana saka hannu a bakin shi, Ayda ta miƙe tana riƙe Aymana, ki barshi yayi na cancanta da hakan, Aymana tana riƙon shi, Ayda tana janye ta, suka kama kokori akanshi.

Kowanne da kuka a tare dashi Ayda ta ce "Me yasa zaki zaɓi zama dani, ina cutar daku."

Aymana ta ture Ayda tana ruƙon Sultan dake shirin ɗaukar biro, Ayda fizgeta Sultan yayi saurin riƙe Aymana dake shirin faɗawa kan kujera.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 25, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MASARAUTAWhere stories live. Discover now