MASARAUTA 30

140 20 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).

*SHAFI NA TALATIN. 30*

Shirun da su ka ji Mai martaba yayi hakan ya sa kowanne ya ɗan yi shiru, suna jiran kalaman shi.

Sai da ya fara gyran murya kafin ya ce "Ina taya ku murnar samun Magaji Allah ya raya mana shi akan daidai."

Aymana ce ta amsa da "Ameen" Yayin da Sultan kan shi ya ke a ƙasa.

Ya kalli Aymana "Inshallah wannan lokacin iyayen ku za su yo tattaki don zuwa taron suna."

Cikin jin daɗi Aymana ta ce "Muna godiya."

"Allah ya baka nasara! Allah ya sa zuwan ya zama har da Kaka." Cewar Sultan

Sai da yayi dariya kafin ya ce "Lallai kam ina tunanin har da ita."

"Allah ya kawo mana su lafiya."

Mai martaba ya numfasa "Sai kuma magana ta gaba."

Sai da gaban su ya faɗi cikin sauri suka ɗago suka kalli Mai martaba, ya kalle su tare da cewar "Akan ka ne Sarki Sultan."

Sultan Amin ya ƙara matsawa yana sunkuyawa ya ce "Allah ya ja zamanin ka."

"Me ke faruwa a masarautar ka? Me ke damunka? Ina jin maganganu suna rewaɗe nahiyoyinmu, shin Sarkin masarautar Toro yana da matsala da mulkin shi ne?"

Ajiyar zuciya Sultan ya yi, lallai ya san dole za a ringa yawo da zancen shi a cikin masarautun.

"Allah ya baka nasara! Babu komai."

Cikin sauri Aymana ta ce "A'a Sultan, Bab..." Sai kuma ta yi shiru ta kasa ida maganar.

Shi kam Sultan har lokacin kan shi a sunkuye ya ke. "Ina jinki Aymana."

Gyara zama tayi tare da faɗawa mahaifinta halin da magauta suka fara saka Sultan, shiru na wani lokaci kafin Mai martaba ya fara Addu'o'i ya kalli Sultan "Dama dole sai ka tashi tsaye da addu'a Sultan ganin yadda mulkin gidanku ya zo maka a lokacin da ba a yi tunani ba, kuma akwai masoya karagar bayan kai."

"Haka ne Baba, mun ƙara dagewa fiye da da, yanzu haka muna amfani da Addu'o'in kariya da Kaka ta aiko mana."

Shawarwari ya ci gaba da ba Sultan tare da faɗa mashi matakan da sarakuna su ke ɗauka don gudun maƙiya su cin musu.

"Sannan kuma ka kiyaye fitar da takalmin ka a ko ina, kar ka kuma cire takalmi a fada, in da so samune ma ya kasance har karagar ka, kana zama da takalmin kane."

Aymana ta ɗago da sauri "Me amfanin hakan Baba?"

"Takalmin wani babbar hanyace, ta amfani dashi don ganin an karya Sarki, ana iya saka wani sihiri aciki, Sarakuna su taka ba tare da sanin su ba."

"Zamu kiyaye Inshallah" cewar Sultan.

Kuyangi suka fara shigo da abinci da kayan motsa baki, sun jima kafin Mai martaba ya dawo suka ci gaba da tattaunawa akan lamarin Sultan, Yayin da Aymana tayi bankwana da mahaifinta ta shiga ciki.

Ba ƙaramin daɗi Mai martaba ya ji ba da ziyarar da Sarkin Bilyam ya kawo masu, tabbas yasan yanzu sun riga sun zama ɗaya sun kawar da duk wata gaba a tsakanin su.

Bayan shigar Aymana aka fara shiga da kayayyakin da Mahaifinta ya kawo ma masarautar don murnar samun Magaji.

Kowa yayi mamaki, to amma daga yanayin Aymana sun fahimci ta fito daga Babbar masarauta da suke taƙama da dukiya fiye da sauran masarautun nahiyoyin.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now