MASARAUTA 42

118 18 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA ARBA'IN DA BIYU. 42*

*SIYYA COLLECTION* 07033111950

Ki na buƙatar HUMRA mai ƙamshi? *Nemi Siyya collection.*

Ki na neman TURAREN WUTA, Na jiki, kaya, da na tsugunno, kina son zama ƴar gayu saboda ƙamshi mai sanyi ? Nemi *Siyya collection*

Ina Amarya da uwayen gida dake son dawo da martabar Auren su *Siyya collection* na da ingantatun kayan gyaran jikin amare. Akwai kayan mata masu ciko da jiki da kuma saukar da ni'ima.

Kina son fatar ki tayi laushi da santsi tare da haske mai kyau? *Siyya collection* ta tanadar maku, light cream, whiterning cream da Glowing cream kala-kala.

Sabulun wanka masu saka fata haske, ingantattu da basu da illa. ki nemi *Siyya collection*

Supplement domin ciko da inganta Breast da hips, akwai na kyaran fata xalla, ba sa da illa ga lafiyar ku.

Don gyaran gidanku da tsabtar shi *Siyya collection* tana siyar da turaren mopping.

Ku dai ku Tuntuɓeta akwai sauƙin kuɗi, haka kuma muna tura kayanmu duk garin da kuke. *Siyya collection*
Call:-09136159778
Whatsapp 07033111950.

*Page 42*

Washe gari gidan komai ya lafa musu, hankalin kowane ɓangare ya kwanta musamman masoyan Aymana da Sultan, iya ɓangaren Ayda da Hajiya Mai gado ne suke nasu ƙumbiya ƙumbiyar.

Aymana kuwa a dakewar Izza ta fito, ta sha gaisuwa ga kowa, Farida kuwa murna kawai ta ke Uwar ɗakinta ta fito.

Aymana bata bawa kowa fuskar ta da zance ba, Sai dai kuma tana jin kunyar zuwa ɓangaren Gimbiya Ummi, lokacin da ta je tayi tunanin samun sauyi, amma saboda dattako irin na Ummi ko nuna hakan bata yi ba.

Bayan ya dawo ne ta shirya rubutun ban haƙuri zuwa ga Mai martaba, ya ji daɗi sosai kuma ya samu nutsuwa, sai dai bai mai da mata wata amsa ba iya soƙon gaisuwa ya faɗa mata.

Washe gari aka gabatar da Baba Haroun ga Masarautar Toro, ananne zai ƙarɓi hukuncin shi, na laifin abinda ya saka Aymana ta aikata.

***

Lokaci ya fara tafiya, komai ya dai-daita, watannin Haihuwar Ayda yayi, hakan yasa duk suke murnar Magajin Sultan.

Aymana kuwa cikinta yayi girma ya fito, har tana jin nauyin yawo a gidan.

Yau tana zaune akan kafet ta miƙe ƙafafuwanta da wani kwanon abinci gabanta, Sultan ya shigo da wasu fadawa bayan shi, da kayyayaki, suka ajiye tare da gaida ita suka juya.

Dariya ya zauna yana mata, Aymana ta juyar da kanta gefe, Sultan ya durƙusa gabanta ya saka hannu yana shafa cikinta, ta ture hannun tana faɗin "Ka barni kawai, ji fa yadda nake ta cin abinci kamai wata rugiya."

Zama yayi kusa da ita "Ni banga wani cin abincin da kike ba, har yanzu babu wata ƙiba da kika yi."

Aymana ta dafa zata miƙe, Sultan ya kamota, suna yin hanyar ciki, Jakadiyya ta turo cikin sauri, Sultan ya ja ya tsaya, yana ɗan sakin hannun Aymana daya riƙe.

"Barka da Wannan lokacin Sarkin sarakuna, na zo sanar da kai, Gimbiya Ayda ta sauka."

Cikin sauri Aymana ta juyo tare da faɗuwar gaba, Sultan ya daidaita nutsuwar shi yana nuna murnar shi, wanda bai nuna a lokacin haihuwar Abul na ya ce "Alhamdulillah Jakadiyya a sanar Sultan yana zuwa."

MASARAUTAWhere stories live. Discover now