MASARAUTA 37

118 19 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA TALATIN DA BAKWAI. 37*

Washe gari haka Sultan ya fita don tarar baƙin shi da zasu zo don neman Auren ƙanwar shi Saratu, Aymana kuwa ta jima kwance jikinta babu kwari saboda ciwon kai da take jin ya rufeta sosai.

Lallaɓawa tayi ta koma nata ɓangaren, Farida ta samu tana mata goge goge a falo, don yin shara.

Ta zauna tana ɗan dafe kanta, Farida ta matso tare da dafa hannun kujerar da take tace "Lafiya kuwa Uwar ɗakina."

Ɗagowa tayi a hankali tana faɗin "Ciwon kai ne wallahi, amma yanzu zan sha magani."

Farida ta miƙe cikin rawar jiki zata fara magana, Sai ga Kuyanga Aisha ta shigo hannunta da turaren wuta zata saka wa falon.

Farida tace "Ki faɗa min inda maganin yake zan ɗauko maki."

Dai-dai lokacin turaren ya gauraye falon da ƙamshi, yana dokar hancin Aymana cikin sauri ta dafe hancin tana faɗin "A'a'a Me wannan."

Tana maganar tana miƙewa tsaye, Farida tace "Me ya faru?"

Aymana ta yi saurin nunawa Aysha hanya akan ta fita da turaren wutar, Aisha sam bata gane ba, sai ma nufarta da tayi don tambayar lafiya.

Cikin sauri Aymana ta dafe cikinta, tana kakarin amai, kafin Farida tazo har tayi ƙoƙarin shiga ciki amma takasa a hanya ta kama malaya amai mai ciwo, wanda dakyal ta ke iya yinshi.

Gaba ɗaya suka gigice, Sukayi kanta suna dafata tare da tambayar lafiyarta, kai kawai take ɗaga masu, Farida tayi saurin ɗaukar wasu ruwa ta balle marfin tana zuba mata a fuska.

Sai lokacin ta fara sauke ajiyar zuciya, ta matsa daga jikin aman ta dafe kanta, Farida tace "Sannu Allah ya baki lafiya."

Aisha tace "ko a kira likita ne?"

Kai ta kaɗa mata, ta dafa ta miƙe zuwa ciki Farida ta bita ta yi saurin shiga banɗaki ta haɗa mata ruwa.

Aymana tana watsa ruwan ta fito da kyal ta iya saka wata doguwar riga. ta faɗa kan gado zazzaɓi ne ya rufeta, ta kalli Farida tare da nuna mata maganin da zata bata.

Farida ta ɗauko ta ɓalle mata, sai dai kuma me, Aymana tana haɗe maganin tare da mai do shi, amai sosai ta ƙarayi a gefen gadon, hakan ya ɗaga hankalin su Farida.

Fadawa kan gadon tayi tana dafe kai, ga wasu hawayen azaba na binta, Farida ta ce "Don Allah ki bani izinin samo mai duba ki kin ga..."

Hannu ta kaɗa mata amma Farida bata saurareta ba, ta fice, rasa mafita tayi hakan yasa ta nufi wajan Gimbiya Ummi ta shaida mata halin da Aymana take ciki.

Cikin sauri ta biyota suka yo sashen tare da Jakadiyya, aikuwa a ƙofa suka sami Aymana ta jiri ya kwasheta a wajan, salati Gimbiya Ummi ta kamayi.

Tana durƙusawa kanta, ta ɗago tana yiwa jakadiyya magana, amma ina Jakadiyya ta nufi ɗakin maganin gidan don kiran likita.

Gimbiya Ummi da Farida ne suka kamota suka mayar da ita kan kujera, Farida tana shafa mata ruwa a fuska, Aymana tana jinsu amma ta kasa komai.

Sai hannu data ɗaga dakyal ta mayar saman cikinta da mararta, Sai lokacin ta ji muryar Gimbiya Ummi hakan ya sa ta buɗe ido dakyal, ta sa ɗayan hannunta tana riƙo Gimbiya Ummi.

"Yi haƙuri Aymana yanzu za a zo a duba ki."

Bata iya faɗar komai ba, sai ga Jakadiyya da sauri saurinta, tare da likita da akwatin aikin shi.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now