*MASARAUTA.*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA ARBA'IN DA TARA 49*
*SIYYA COLLECTION* 07033111950
Ki na buƙatar HUMRA mai ƙamshi? *Nemi Siyya collection.*
Ki na neman TURAREN WUTA, Na jiki, kaya, da na tsugunno, kina son zama ƴar gayu saboda ƙamshi mai sanyi ? Nemi *Siyya collection*
Ina Amarya da uwayen gida dake son dawo da martabar Auren su *Siyya collection* na da ingantatun kayan gyaran jikin amare. Akwai kayan mata masu ciko da jiki da kuma saukar da ni'ima.
Kina son fatar ki tayi laushi da santsi tare da haske mai kyau? *Siyya collection* ta tanadar maku, light cream, whiterning cream da Glowing cream kala-kala.
Sabulun wanka masu saka fata haske, ingantattu da basu da illa. ki nemi *Siyya collection*
Supplement domin ciko da inganta Breast da hips, akwai na kyaran fata xalla, ba sa da illa ga lafiyar ku.
Don gyaran gidanku da tsabtar shi *Siyya collection* tana siyar da turaren mopping.
Ku dai ku Tuntuɓeta akwai sauƙin kuɗi, haka kuma muna tura kayanmu duk garin da kuke. *Siyya collection*
Call:-09136159778
Whatsapp 07033111950.*Page 49*
Shigewa yayi yana yin shirin bacci, don akwai gajiya sosai a tare da shi.
Aymana kuwa mutanen da ke shigar wajanta ma ba zasu barta baccin ba, tana magana da Farida ta fara jin sanarwar taron da Sultan zaiyi, ta kalli Farida tare da ɗaga mata hannu akan tayi shiru tana son gane abinda ake sanarwa akai.
Da sauri ta miƙe tsaye tana dafe ƙirji Farida ta miƙe tana faɗin "Fatan na sara uwar ɗakina."
Da mmurmushi Aymana ta nufota, ta riƙe mata hannu "Me hakan ya ke nufi Farida."
"Ina ganin Sultan yana so ya ramawa kura aniyarta."
Ajiyar zuciya tayi sai dai kafin ta ƙara magana Farida ta ci gaba "Ina ganin Sultan yana son yin amfani da damarnan ne, ya gabatar da duk wani shagali da bai yi ba akan ki."
Aymana ta koma ta zauna "Lallai ina so shirina na gobe ya sha banban da kowace rana."
Ta kuma miƙewa tare da nufa sashen shi ta baya "Zan gana da Sultan yanzu."
A kwance ta same shi yana kallon sama, ya aza hannuwanshi a kirji, ta jima a tsaye a tunaninta bai san da zuwanta ba, hakan yasa ta ke ƙare mashi kallo cikin farinciki.
"Ko Gimbiya ta zaɓi tsayuwa akan kusantar Sultan."
Cikin dabarbarcewa ta shiga tare da zama bakin gado "Ni bansan me zance ba Sultan, akan dawowa ta har sai an yi wani tar...
Zaune ya tashi "Ba na buƙatar jin komai daga gare ki, ina so ki halarci taron ne?"
"Shi ne buƙatar ka?"
Ya ɗaga mata kai, Aymana ta matsa ta riƙo hannun shi "Na gode Allah ya taimakeka."
Ya saka hannu yana janye ɗankwalin kanta, ya fara shafa gashin kanta "Ko mai za a yi domin ki, Sarauniyar matan Nahiya, 'yar Sarki a Masarautar Bilyam, ke ɗin matace ga sarkin Babbar masarauta, duk da yanzu a zuciyata ina ƙasƙantar da masarautar san...
Hannunta ta sa tana rufe bakin shi "Kar ka fara haka sultan, Babu wata masarautar kamar ta ka, komai na kane Sultan, kai ne mai masarautar da ke da Takobi."
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.