MASARAUTA 51

116 15 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA HAMSIN DA ƊAYA. 51*

Aymana tana kallon fitar Ayda ta soma wani murmushin mugunta ko ba komai dai yanzu ta san ta gama fahimtar Sultan na ta ne, ita ce yake so.

Wani tunani yazo wa Aymana ta fara magana akan Baba Maga yaƙi, akan jajircewa da yake wajan tsoro ta ɗora da cewar "Saboda jajircewar shi na akwai kyaututtuka da za a gabatar gare shi, da kambun girmamawa, haka kuma a ƙarƙashin sarautar Gimbiya zai rinƙa amsar wani kaso bayan wanda yake amsa a yanzu." Aymana ta yi hakanne sanin kewar lallai mutanen masarauta kamar kaji suke sai ana watsa musu tsaba. Wani daɗi Baba Maga yaƙi yaji jin yadda Aymana take kambamashi a wajan taron.

Ta cigaba da jawabi, ta kuma yin godiya  daga ƙarshe ta nemi Mai martaba da yayi magana ko akwai wani ƙarin haske a jawabinta.

Mai martaba kuwa maganganun shi kaf na kwarin guiwa ne, tare da tabbatar da matsayin Aymana a gidan da kuma nahiyar su.

Hakan ya ƙara ɗaga hankalin su Yarima Saifu, Baba Maga yaƙi kam wannan lokacin ya saduda akan komai, yana da tabbacin Aymana tana akan gaskiyarta ne, ko da can ba wai yana gudunta ba ne a'a yana goyon bayan 'yan uwanshi ne, amma wannan lokacin ta riga ta gama dashi ba zai taɓa barin a haɗe kai dashi a aikata wani mugun abu ga takobin ta ba.

Haka aka tashi taro masu farin ciki sunayi masu baƙin ciki suna kwasar ɓacin zuciya.

***

Gimbiya Ummi ce zaune gaban Maimartaba magana suke akan Aymana da yanayin yarinyar Mai martaba ya ce "Tun yaushe na sanar da ke zata zamar ma Sultan bango, kina ganin yadda ta tabbatar bai zauna kujerar da suka aje mishi ba."

Murmushi ta yi "Tabbas na yarda, na kuma yarda da hakan, Allah ya kara tsare mana su."

Sultan ya yi sallama yana shigowa falon, Ya yi saurin durƙusawa "Allah ya taimakeki na je wajan ki, aka ce kina wajan Mai martaba."

"Allah ya ja da ran Sultan bari Mai martaba ya baka waje ka gana da ita." Yayi maganar cikin salon zolaya.

Sultan yayi saurin matsawa gaban shi "Ayi min Afuwa, ina mai tuba gareka."

Mai martaba yayi dariya "Fatan komai lafiya."

"Lafiya kalau Gimbiya"

"Muna nan muna firarku, Ban taɓa tunanin Aymana zata fita da takobin ta dawo da shi  nan gidan ba."

Sultan ya ja dogon numfashi "Ni nasan zata dawo dashi, amma nayi tunani kala-kala, hakan ya tabbatar yanzu zata kwantar da hankalinta ta gane babu wata masarauta da tafi ta Sultan ɗin ta." Yayi maganar da cijewar Fuska, Gimbiya Ummi ta ce "Haka ne."

Mai martaba ya ce "Zuwa yanzu hankali na ya kwanta, burina ya cika akanka Sultan, ko yanzu na rasa rayuwata bana da wata damuwa akan mulkinka, sai dai na maka fatan nasara har ƙarshen ta ka rayuwar."

Sultan ya riƙo hannun Mai martaba "Tabbas ka zamo mahaifi na gari ga yaranka, ka nuna ƙauna ga kowa sai wanda ya bijire maka, Mai martaba na gode da soyayyarka garemu, insha Allah muna tare har...

Dariya Yayi yana kaɗa kai, Gimbiya Ummi ta goge 'yar kwallar dake zubar mata, Sultan ya ce "Ba lokacin kuka bane Gimbiya, wannan lokacin farin ciki ne."

Haka suka cigaba da firar su cikin jin daɗi da fahimtar juna.

***

Baba Waziri ne yake rabka uwar sallama a bakin ƙyauran gidan Baba Maga yaƙi, ya fito tare da faɗin shigo mana.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now