MASARAUTA 28

128 29 11
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI ASHIRIN DA TAKWAS. 28*

Anan suka yi karo da Farida tana fitowa, zubewa tayi tana gaishe ta, Aymana ta saki fuska tana Amsawa suka yi ciki abin su.

Sannu Farida tayi mata Aymana ta ce "Kowa ya na gaishe ki."

Farida ta zauna tana tambayar Mutanen gidan da kuma sauran ƴan uwan ta bayi.

Sun jima Aymana ta miƙe ta shiga ciki don watsa ruwa ta yi salla.

***

Sultan kuwa suna shiga ya saki hannun Ayda ya yi hanyar ɗakin shi, Ayda ta bi shi baya tana tsaye a ɗakin har ya gama cire rawani da alkebbar shi babu alamar taimako daga wajen ta, sai ma tambayoyi marasa amfani dake mata yawo a zuciya.

"Da ma tafiyar da aka sanar zuwa ɗaukar Aymana ne?"

Cikin sauri ya juyo ya kalleta yana mai ƙare mata kallo, har saida ta ɗan tsorata ya jire babbar rigar shi, fuska ɗaure ya yi shirin wanka.

Yana faɗawa ɓanɗaki Ayda ta miƙe ta fice, lokacin da ya fito, ganin bata nan hakan ya sa yayi kwafa tare da kaɗa kai.

Bayan kwana biyu da dawowar Aymana hankalinsu ya kwanta, sun ci gaba da gudanar da rayuwarsu babu yabo ba fallasa tsakaninta da Sultan musamman a gaban Al'umma yana darajata da bata matsayi.

***

Ayda ce yau gaban Sultan tana zuba mashi abinci, binta yayi da kallo, abin ko kyau baiyi mata ba saboda rashin sabo.

Ya sauko yana fara cin abincin da ta zuba maganin da Waziri ya bata, ganin ya ci ta miƙe ta na ficewa ba tare da bankwana ba.

Da da daddare Aymana ta shigo ɓangaren kasancewar itace take da amsar ɗaki, yana zaune ta shigo da wasu kayan sarauta a hannunta.

Ta kalleshi "Barka da dare."

Baiyi saurin amsa mata ba, sai da ya ɗauki lokaci ya ce "Kin wuni lafiya?"

"Alhamdulillah ina za ki je da kaya haka?"

"Zan ajiye ne anan."

Murmushi yayi mata ita kuma ta shige ciki.

***

Aymana ta samu ta daidaita komai na dangane da Sultan da magautan shi, Abubuwa sun ɗan lafa hakan yasa ta kwantar da hankalinta.

Wannan lokacin tayi watsi da Ayda ko da sun haɗu tayi habaicinta bata kulawa, gaya cikinta ya fito sosai, a yanzu ta gane ba itace abokiyar yin ta ba Waziri ne abokin yinta tunda har ya cigaba da jifarta da kalamai idan sun haɗu.

***
Suna zaune ɗakin Gimbiya Ummi Sultan ya shigo yana ɗan zama tare da Ajiyar zuciya mai ƙarfi, Gimbiya Ummi ta kalle shi "Me ke damun Sultan a ƴan kwanakin nan?"

Shiru yayi na ɗan lokaci kafin ya ce "Babu komai Gimbiya."

Aymana ta matsa kusa dashi "Amma idan ba komai Me ya sa a lokuttan nan kowa ya rasa gane kanka."

Dama Aymana tana neman hanyar faɗa mashi abinda take fahimta a tare da shi, Gimbiya Ummi tace "Faɗamin Sultan."

Ajiyar zuciya ya kuma saukewa, gaba ɗaya ya rasa sanin matsalar shi komai yana neman taɓarɓare mashi, musamman a ɓangaren Fadar shi da ba ya son aiwatar da komai.

Shiru Aymana tayi ta miƙe ta kawo mashi ruwa, Ummi ta kuma tambaya ya ce "A'a babu komai fa Gimbiya."

Yayi maganar tare da miƙewa, Kallo suka bishi da shi. Jikin Gimbiya Ummi yayi sanyi ta kalli Aymana, ita ɗin ma ita take kallo, Sai kowa da abinda yake saƙawa a ranshi.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now