*MASARAUTA.*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA ASHIRIN DA UKKU. 23*
Farida ta miƙe tana bin umarnin uwar ɗakinta, Gimbiya Aymana ta miƙe tsaye tana dafe ƙirjinta jin yadda yake harba mata, ta koma ta faɗa kan gado, a zuciyarta ta fara tunanin miye dalilinta na ciga tsanani irin kaga "Kishi" wani ɓangaren zuciyarta ya amsa mata.
Girgiza kai tayi alamar ƙaryata zuciya a fili kuwa ta ce "Babu dalilin hakan." cikin sauri ta dai daita nutsuwarta, ta hanyar sauke ajiyar zuciya.
Hanyar ban ɗaki ta yi don shiga wanka, bata ɗauki lokaci ba ta shirya ta na fito babban falonta, anan ta samu an ajiye mata kayan kari, sam bata buƙatar komai, fita take son yi, amma sam ba ta son ganin duk mutanen gidan don tasan kowa da abinda zai yi tunani akan ta da kuma Yarima.
Tana zaune dai babu wani tsayayyar shawara a tare da ita, har rana ta take sosai, dole ne ta je gaida Sultan don ita kanta tasan ƙa'ida ne hakan, ko don matsayin da yake da shi a yanzu.
Mayafi ta ɗauka ta yane kanta, ta yi sa a babu kowa a farfajiyar hakan ya bata damar kwankwasawa tare da jira, babu amsa hakan yasa ta jima kafin ta murɗa tare da tura ƙofa.
Babu kowa a falon sai ƙarar na'urar sanyaya ɗaki dake fita a hankali, wai gawa tayi tana yin hanyar ɗakin shi.
Abinda bata sani ba, Sultan Amin yana gefen kujeru kishingiɗe saman kafet, binta yake da idanuwa ganin zata shige hakan ya sa yace "Aymana!"
Cikin sauri ta juyo ta kalli inda taji sautin, wani kallo ta ɗan bishi da shi, har ta isa wajan da yake sam ta kasa ko kyabtawa zuciyarta take raya mata wai Yarima ne har ya kusanci Ayda.
Zaune ya tashi shima ɗin ita yake kallo yana son tantance kallon da take ma shi.
"Barka da Safiya Sultan!" Ta ce tana zama gefen kafet ɗin.
"Baki duba lokaci ba kafin ki fito!"
Aymana tayi jim, Yarima ya ce "Ba yanzu bane lokacin gaisuwa zuwa ga Sultan."
Aymana ta gane yana nufin bata zo gaishe shi ba har wannan lokacin, shi kuwa Yarima Allah ya sani tun Asuba ya ƙagara ya ganta, in da yana da damar zuwa dubata da zai yi hakan ne.
"Allah ya huci zuciyar..."
Bata ida ba ya katseta "Kin yi bacci kuwa?"
Don shi sam hakan ya ƙauracewa idanuwan shi, musamman kusantar Ayda da ya farayi kafin Aymana, hakan ya ɗan taɓa zuciyar shi. Aymana ta ce "Bacci sosai! Bacci mai nauyi kuwa Sultan."
Ƙurr ya ƙura mata ido ya miƙe, ya yi kan kujera ya zauna hakan ya bata damar tashi ta bi shi.
"Ni nake da lokacin bacci saɓanin wasu! Ta yaya kura da shan bugu gardi da anshe kuɗi!"
Shiru yayi ya fahimci maganarta amma ba ya ra'ayin maganar "Kun gana da Gimbiya Ummi?"
Hankalinta ta maida kanshi, don tana ba iyaye muhimmanci "Tun jiya rabo na da ita, lokacin data ja kunne, amma yanzu daga nan can zan nufa."
"A miƙa gaisuwata kafin in fito."
Aymana ta miƙe ta ɗan sunkuya "Na barka lafiya."
***
Tun da jakadiyya ta baiyana tsakanin Ayda da Yarima Hakan ya raunana zuciyar Ummi, anan ta fara tunanin yadda har Yarima ya ɓoye tsakanin shi da Aymana amma gashi ya baiyana akan Ayda.
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.