MASARAUTA 26

113 22 2
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA ASHIRIN DA SHIDDA. 26*

Ayda ta fito da ga ɓangaren ta, sashen Sultan ta shiga don ansa kiran shi.

Yana tsaye yana kai kawo a tsakar falon, jin motsinta hakan ya sa ya maido hankalin shi kanta, ya jima baiyi magana ba.

Ayda ta kawar da kai gefe "Na samu saƙon kir..."

"Ko baki san da tafiyar Gimbiya Aymana ba, Lallai kin ji motsin mutanen gidan nan, Me dalilinki na rashin yin rakiya gareta?" Ya faɗa yana ɗaga murya.

Wani zafi Ayda ta ji don bata raka Aymana ba shi ne yake faɗar hakan, juyar da kanta tayi "Bai zamar min dole yin hakan ba, ita me ya sa bata je ta min bankwan..."

"Ke!" ya kirata, tare da tattaki zuwa gabanta "Kalli ido na, na ce ki kalli ido na."

Ayda ta ɗan ji tsoho ta ja baya Sultan ya cigaba "A me kike da za ta zo maki bankwana, ya zama dole ki ki bata matsayinta, ki  Girmama ta, domin girmamata tamkar girmama Sultan ne, ina mai jan kunnan ki."

Ayda ta ɗaga baki za ta yi magana Sultan Amin ya nuna mata ƙofa "Akan Aymana zak..."

"Ki fita nace, ki bar min turaka !" Ya faɗa cikin daka mata tsawa.

Abin mamaki Ayda ficewa tayi ba tare da ta nemi afuwa da kuma sanyaya zuciyar shi ba, saɓanin Aymana ko yaushe ta na jifar shi da kalamin Allah ya huci zuciyar shi.

Ta na ficewa Ya faɗa kan kujera yana maida numfashi, anan ya fara tunani fal zuciyar shi, tafiyar Aymana ji yake ta saka ƙunci sosai a tare da shi. ya jima kafin ya shiga ciki don shiryawa zuwa fada.

***

Ɓangaren mahaifanta Ayda ta nufa sai dai wani irin kuka ta saka tana faɗawa kan cinyar Inna, Inna ta ɗagota "Lafiyar ki?"

"Wai ni Sultan ya kora daga turakar shi don kawai ban fito na raka Aymana ba."

Inna ta tafa hannu "Ni kam bani iyawa wallahi, abubuwa sai ƙara taɓarɓare mana suke."

Ayda ta buga hannu daidai shigowar Goggo "Banda kora har ya sanar dani, dole na bata matsayinta, na girmama ta"

Goggo ta buga sallallami "ita har ta isa a girmama ta da wane matsayin?"

Ayda ta kalli Goggo "To ya ma sanar dani Girmammata kamar girmamma shi ne."

"Karya yake wallahi." Cewar inna dake miƙewa tsaye.

A wannan lokacin sun gama tabbatarwa kansu lallai Aymana ta samu ƙafafuwan zama a gidan sai dai sun ɗauki alwashin ba zasu taɓa yin ƙasa a guiwa ba.

***

Aymana bata sanar da mutanen gidan su zuwanta ba, hakan ya sa sai dai suka ganta lokacin da sam ba sa  zato.

Kowa yayi murnar zuwanta, gun mahaifiyarta ta nufa tana mai faɗawa jikinta "Ummana nayi kewarki sosai"

Umma ta ɗagota tana ƙare mata kallo tabbas yarinyar tata ta sauya alamar ƙarin samun hutu ga fatar ta, amma sam babu alamun ƙara ƙiba a tare da ita.

Za ta yi magana Mama ta shigo, matar Mai martaba ta Ukku kenan "A maraba- maraba da Gimbiya Aymana."

Aymana ta ɗago "Sannu da gida Mama."

Mama ta  zauna "Allah sarki ƴata gaskiya munyi kewarki." Cikin salon makirci.

"Ni kaina hakanne, wai ina Bilkisu."

MASARAUTAWhere stories live. Discover now