💙💙💙💙💙💙💙💙
*MASARAUTA.**EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA SHIDDA. 6*
Tunani kawai yake, gyaran muryar da Sarki yayi shi ne sanadiyar dawowar Yarima Amin cikin hankalin sa"Ina jin ka ko kana ganin na baka lokaci don yin nazari akan magana ta?"
"A'a Baba ai wannan hukunci ne ka yanke akaina,wane tunani kuma bayan naka?Na Amince,kuma zan bi umarninka kamar yadda zanbi umarnin Sarkin Toro."
Wani farin ciki ya ziyarci zuciyar Sarki"Naji daɗi Aminu,Allah yayi maka Albarka,zan nemi Babanka na sanar mashi da kaina."
Sunkuyar da kai yayi,sosai ya ƙarajin nauyin Maimartaba yanzu"Za ka iya tafiya,Allah yayi mana jagora."
Yarima ya kuma sunkuyawa cikin ladabi"Na gode Baba"
Murmushi kawai Maimartaba yake yi,shi kuwa da kyal ya iya miƙewa yana ɗan dafe ƙirjin shi dake bugawa da ƙarfi,yana fita ɗakin yayi cikin gidan.
A mamakin shi anan ya fara ganin gungun mutane sosai ranshi ya bashi maganganun da suke akan auren shi ne da Aymana.
Yarima kasa wucewa ɓangaren Kaka yayi don ba shi da wani kuzarin hakan.
Akan kujera ya samu Bilal ya ɗan fara bacci ajiyar zuciyar shi ce ta tashi Bilal ɗin.
"Wai ka dawo ban sani ba?"
Bai bashi ansa ba ya cire rigar Jabbar dake saman kayan,kan kujera ya faɗa yana dafe kai.
"Me ke faruwa naganka kamar a hargitse?"
"Kama ce ma?"
"Na ga ka fita lafiya lau amma ka dawo a haka."
Yarima ya rufe ido yana buɗewa"dole ne,taya zan ɓullowa lamarin auren Aymana a lokacin da mutanan gidan nan..."
Bai jira ya ida ba"Auren Aymana?"
"Maimartaba ne ya ce ya bani aurenta,tare da zaɓi idan bana ra'ayi na faɗa mashi"
"To me ka ce mashi."
"Kana tunanin zan iya musu da shi,na ce na amince amma wal..."
"Amma me? Ai shi kenan zance ya ƙare sai mu shirya biki domin kuwa..."
"Bilal kasan kuwa mutanen gidan nan yadda suke."
"Mutanen gidanne zaka aura ko Aymana?"
"Ita ɗin ma nasani,kuma nasan ba zata amince ba."
"Ni fa tun zuwanta naga dacewar ku"
Yarima ya kauda kai yana miƙewa tsaye"Matsala ta da kai ana maganar gaske kana sako wasa"yayi maganar yana shigewa ciki.
****
Aymana bata san abinda ke faruwa ba,sai washe gari kuma duk gidan an rasa wanda zai tunkare ta da maganar,har ta gama shirya kayan karin Yarima.
Bata same shi a falon ba sai fadawan shi da sukace ya na shiryawa ne.
Fitowa tayi ta nufi ɗakin Kaka,Kaka ta rangwaɗa guɗa"Na kusa aurar dake in huta da zuwa kwasar min abin..."
"Waye za kiyiwa auren?"
"Ke mana,ba ki da labari?"
"Kaka kenan yau kuma da wannan tsokanar kika tashi,bari inje in dawo mu ida maganar"tana maganar tana yin hanyar fita.
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.