💙💙💙💙💙💙💙💙
*MASARAUTA.**EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).Are you guys looking for where to buy ur skincare product @ mg's skincare is the best plug for you🤗
Do you wish to have that flawless skin that's free of all skin prblm
Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads wherever you go😉
Try mg's product nd I assure you you'll never use any other product except mg's product✅
Mg's will gv you the best out of all
With mg's product ur skin is 💯 clear,fresh,smooth nd ur skin will absolutely glow all day💃
We have herbal whitening black soap now nd halfcast set available
Just gv it a try now nd see wonders✅
Chat:08062991549
Call:08064532391
Soap price:3k
Halfcast set:11kFollow us on
Instagram@glow_with_mgs
Facebook:mg's skincareNew product alert🎤
While pampering ur skin,do not forget that ur kid/children deserve to be moisturized with products made from the best things on earth👍@ mg's skincare now will be having perfect organic soap for children💃
The soap will be available within 2weeks🤗
You can start placing ur orders now or you can wait until the soap landed🥰
08062991549Do not forget to follow us👆
Like nd comment pls dearies😘
Patronize us🙏
mg's always serve you the best✅❤️*SHAFI NA SHAƊAYA. 11*
Aymana bata ƙarasa ba ganin Yarima Amin dake tunkarosu,hakan ya ba Ayda damar juyawa tana kallon Yarima,ja tayi da baya kaɗan,don akwai shakkun Yarima sosai agunta,fuskokinsu kawai yake kallo,duk maganganunsu babu wanda bai ji ba.
Sai dai bai yi magana ba yasa hannu ya riƙo hannun Aymana,har sun fara tafiya sai kuma ya juyo"Ko ki ji,ko ki yarda,ko ki bi koma akasin haka,ba zan lamunci yin abinda ba daidai ba ga matata,ki kiyaye?"
Cigaba da tafiya su ka yi,sai dai Aymana binshi kawai take,har ƙofar ɗakin Hajiya maigado suka tsaya,sai anan ya cire hannun shi daga nata.
Sannan ya fuskanceta"Ayda kenan 'yar gidan Waziri,Yaya a gun Maimartaba,shi ne yaso zama sarki,saboda wasu halayya nashi marasa kyau hakan yasa al'umma suka juya baya a gare shi."
"Har yanzu Waziri yana mai soyuwa ga mulkin mahaifinka..."cewar Aymana da ke kallon shi.
"Ni ne zan maki wannan bayanin"
"Ya zama dole Ayda tabar shirgina,babu ruwana da tana son auren ka,in zata aureka ni ban hana ba,ƙofa a buɗe take agunta,amma na rantse da ƙarfin mulkin mahaifina idan ta cika shiga damuwata ba zata ji ni da daɗi ba,aka ce mata mulkin miji wani mulkin tunƙaho ne?"
Yarima ya harɗe hannuwa"Da ni kike magana ba Ayda ba ki tsabtace kalaman ki"
Juyawa tayi tana shirin shigewa Amin ya ce"Kar naji wani ya fahimci bakyason aure na"
Da karfi ta juyo"Zan yaudari kai na ne?"
Baiyi magana ba ya juya don ya gama faɗan abinda zai faɗa.
Ƙofar ɗakin da aka sauketa ta shiga akan gado ta samu Bilkisu tana jiranta.
Mai martaba ne zaune a cikin turakarshi,Ummi tana gefen shi"Takobin nan itace ƙarfin mulkinmu,haka kuma auren Yarima ya zama wani ginshiƙi a garemu,mallakar mulkin gidannan sai wanda ya shirya ganin mutanen da suke harin karagata,amma nasan yarinyar zata zama kariya sannan zata zamarwa Yarima sulke,saboda tana gadon Takobin,ƙarfin mulkin gidannan duk a ƙarƙashin mulkin su ne."
Ummi tayi ajiyar zuciya,ita kanta tasan akwai aiki babba agaban ɗan nata, soyayyar da Sarki yake mashi hakan ya ƙara saka ƙiyayyar shi a zuciyoyin mutanen gidan"Ina tsoro ina maijin tsoron ranar da za a nemi wanda zai gaji gidannan."
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.