MASARAUTA 47

131 15 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA ARBA'IN DA BAKWAI. 47*

*SIYYA COLLECTION* 07033111950

Ki na buƙatar HUMRA mai ƙamshi? *Nemi Siyya collection.*

Ki na neman TURAREN WUTA, Na jiki, kaya, da na tsugunno, kina son zama ƴar gayu saboda ƙamshi mai sanyi ? Nemi *Siyya collection*

Ina Amarya da uwayen gida dake son dawo da martabar Auren su *Siyya collection* na da ingantatun kayan gyaran jikin amare. Akwai kayan mata masu ciko da jiki da kuma saukar da ni'ima.

Kina son fatar ki tayi laushi da santsi tare da haske mai kyau? *Siyya collection* ta tanadar maku, light cream, whiterning cream da Glowing cream kala-kala.

Sabulun wanka masu saka fata haske, ingantattu da basu da illa. ki nemi *Siyya collection*

Supplement domin ciko da inganta Breast da hips, akwai na kyaran fata xalla, ba sa da illa ga lafiyar ku.

Don gyaran gidanku da tsabtar shi *Siyya collection* tana siyar da turaren mopping.

Ku dai ku Tuntuɓeta akwai sauƙin kuɗi, haka kuma muna tura kayanmu duk garin da kuke. *Siyya collection*
Call:-09136159778
Whatsapp 07033111950.

*Page 47*

Ta rufe idanuwanta, tana jin daɗi yadda Sultan ya ke sonta, domin kuwa sanin kanta ne idan ba soyayyar ba, babu abinda zai tado shi a irin wannan lokacin.

Cikin sauri ta faɗa banɗaki tayi wanka ta ta fito ta hau shiryawa cikin tsadaddun kaya da Farida ta aje mata, Sauri kawai take, sai dai kafin ta gama shiri aka fara kiraye kirayen sallar magriba, haka ya sa ta yi salla.

Shima Sultan ɗin a tare suka tafi masallaci da Mai martaba, kowa yayi mamaki yadda Sultan ya mayar da masarautar kamar gidansu, hakan ya sa kowa yake girmamashi.

Aymana tana ta zaman jira ayi sallar isha ta fita don min ta san ba zai dawo ba sai ya gama sallolin shi.

Kaka ta shigo ɗakin a dudduƙe tana gyayar ɗaurin zaninta "Shi ke nan ashe kin san zuwa zaiyi ba zaki sanar da ni ba."

"To kaka ai ƙara na barki da tseguminki."

"Haka ki ka ce?"

"Wasa nake, Kaka ni ma fa ban san da zuwan shi ba."

Riƙe baki ta yi "Ka jini da ja'irin yaro, yana fama da ƙaton rawani akai, amma ba kunya."

Aymana tana dariya Farida ta  turo ƙofa, Aymana ta ce "Mu je ko?"

Sultan da Mai martaba suka jero zuwa fada, Sai dai Sultan yana ɗan duƙar da kaine alamar girmamawa.

"Kar na jaka ciki Sultan, ka je masauki ka huta, na sa an gyara wurin zamanku, zuwa safe sai mu sake zama."

"Ah! Baba na tanaji masauki a waje sun kafin zuwa na, Ayi min Afuwa."

"Dama kana da masaukin da ya fi nan ne?"

"Ayi gafarce ni." Ya faɗa yana rusunawa, Mai martaba ya kira wani bafade ya sa ya kai shi masauki, da shi da mutanen shi."

Haka Sultan ya haƙura don ya san babu gardamar da zai iya yi, ɓangaren fadawan shi daban haka shima na shi ɓangaren.

Aymana ta fito aka sanar da ita wajan da Sultan yake, daga ita sai Farida suka tafi, a ƙofa ya juyo fadawanshi suna gaida ita, ta ɗan tsaya ta amsa masu.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now