*MASARAUTA.*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA TALATIN DA TARA. 39*
Tun daga ƙafafuwanshi zuwa fuska ta ke kallo tayi saurin ɗagowa ta sauke idanuwanta akan fuskar shi.
Wata iriyar razana ya shigeta ganin Baba Maga yaƙi, zaro ido ta yi za ta fara ja baya ya daka mata tsawa, hakan ya yi sanadiyar tashin sauran masu tsaron wajan.
Gaba ɗaya su ka zare makaman su suna yo kan su, Baba Magayaki ya fara magana "Me ya kawo ki nan? Ba ni abinda ya ke hannunki."
Aymana ta tsaya cak tana kallon shi "Na ce ki bani Takobin, Lallai ashe da gaske abinda kika zo ɗauka ne da gaske?"
Wani daga cikin mutanan wajan ya fara salati zai fara maganganu Aymana ta ɗaga mashi Hannu "Kar na ji bakin ka, Takobin taku ce ko tamu?" Tayi maganar tana foddo Takobin ta riƙe hannunta.
Baba Maga yaƙi ya juya yana salati shima "Ke kuwa kin san darajar Takobin nan a masarautar nan."
Yana maganar aka kama hayaniya kowane yayo ca da maganganu, gaban Aymana ya fara dukan tara-tara far gaba ya shigeta, ta fara waigawa tana gudun kar wani na gidan ya ji su.
"Tabbas kin Aikata babban kuskure, ya zama dole a ɗau mataki akan ki, yanzu da ban farka na fito ba haka zaki fitar da ita..." Yana maganar ya kalli wani tare da faɗin "Maza-maza ka sanar da Tsohon Sarki."
Gaban Aymana ya faɗi ji take kamar ta tsaga kasa ta shige ƙarfin haline kawai ya tsayar da ita, yanzu ta fara tunanin lallai abin kunya ne asameta da aikata hakan, wane hali zata shiga idan mutanen gidan nan suka ji.
Mai martaba ya farka lokacin yana son yin shirin fita masallacin Asuba, ɗan Aiken bai jira ba ya shiga yana son a barshi don ganin Sarki.
Hayaniya aka fara ana sanar dashi sai ya jira idan za ya tafi masallacin, yana faɗar dalilin shi, za a shiga sai gashi ya fito yana tambayar "Lafiyar ku? Me ya ke faruwa ne?"
"A gafarceni Ranka shi daɗe, daga wajan Maga yaƙi ne, yana son ganin ka a babban ɓangaren..."
"A wannan lokacin?"
"Tabbas wani abu ya faru, An kaiwa takobin gidannan hari har an fito da it..."
Kafin ya ida Mai martaba yayi saurin faɗin "Me?" Yayi hanyar fita da sauri.
Samu yayi an kunna hasken wajen cikin tashin hankali ya je, yana faɗin "Me ya ke faruwa?"
"Allah ya taimakeka Aymana ce muka kama tana ƙoƙarin fitar da Takobi zuwa..."
Tattaki Mai martaba yayi yana kallon ta, don sam bai kula da ita ba saboda hayaniyar da ake, takobi ya gani hannun Aymana.
Wata razananniyar tsawa ya daka mata "Waye ya saka ki?"
Ya nufeta cikin sauri, Baba Maga yaƙi ya ce "Ai zance ya ƙare lokacin da muka sanar dakai akwai munafunci a zancen Auren Sultan da ita gani kayi kamar..."
Bai sauka ga maganar ba Sai ga Waziri ya fito da riga 'yar shara, yana mummurza ido alamar bacci ya ke ya fito, tsayawa yayi yana bin kowa da kallo, lokacin ya fahimci abinda ke faruwa.
Aymana ta fara zubar da hawaye, ta sunkuyar da kanta ƙasa Waziri yace "Karshen tukakuki tuk! Manufar ki da mahaifinki ta fito."
Mai martaba ya miƙa hannu zai amshi takobin Waziri yace "Allah ya taimake ka, dole a sanar da Sultan don..."
Mai martaba ya ci gaba da fitar da huci, da wani irin zarewar lamari, ya kalli wani bafade yace "Maza ka sanar da Sultan ina neman shi."
"Tabbas yanzu na yarda da maganar ku, Sarkin Bilyam ya haɗa wannan aurenne don samun damar mallakar Takobi, ya turo Aymana zuwa masarautar mu don satar takobi ta mayar da ita."
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.