*MASARAUTA.*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA ASHIRIN DA ƊAYA. 21*
*NA SADAUKAR DA WANNAN FEJI GABA ƊAYAN SHI GAREKI, RAMLAT A MANGA (MAI - DAMBU).*
*MARUBUCIYAR ƘWARƘWARA, UWAR ƊAKIN MAGAJIN IZZA, FARIN CIKIN BOROROJI, ABIN FAHARIN MATAR MALAM, CIKARKIYAR BAHAUSHIYA, MAZAUNIYAR DAULA BIYU, YAYAR ƳAR GIDAN YADIKKO, KAWA A WAJAN MRS AMIDUD, DA CIWO A RAYUWA SAI DAI RUWA BIYU DA YAKANA YA KAUDA KISHI A TSAKANIN ZUBDA JINI, INA DA BURU A MASARAUTAR JODAN, INA SO YA ZAMA DA'IMAN ABADAN A CIKIN ALHUBBU FIHI MARARATUN.🥰🥰*Ta ɗan jinkirta ba tare da ta ƙarashe maganar ba, ta duƙa kan teburin data aza kofin shayinta ta ɗauki kofin tana mai fizzar kai don nufa cikin ɗakinta.
Lokaci kaɗan ran Yarima Amin ya ɓaci zuciyar shi ta ɗugunzuma da jin kalamanta, hannu yasa tare da fizgo hannunta da ƙarfin shi.
Kofin shayin ya faɗi tare da fashewa, hakan yasa ta ɗago ta kalle shi, sosai ya matse hannunta cikin zafin rai, tare da kallon ƙwayar idanuwanta yace "Mai-maita abinda kika faɗa!"
Jim ta yi batare da ko motsi ba, wani zafin izza take ji, ganin shima Izzar tashi ne take tasiri a jikin shi.
Yarima ya ce"Na ce ki mai-maita abinda kika faɗa!" Yayi maganar tare da sakin hannunta.
Aymana ta girgiza kai, cikin cikar izza tace "Ai na fito daga gidan da magana ɗaya ake, ba a magana biyu!"
Tana faɗar haka ta yi ciki abinta don canza kaya saboda shayin daya ɓata jikinsu.
Yarima ya dafe kai tare da komawa sashen shi, sai dai ya kasa canza kayan sai ma faɗawa da yayi kan kujera yana huci.
***
Bayan kwana biyu Aymana ta ƙara ɗan janye jikinta a gare shi, saninta ne Amin baya son Ayda to amma miye zai sa ya nuna farin cikin shi akan lamarin.
Yau Mama ce ta shigo sashenta su ka ɗanyi fira Mama tace "Ni kuwa Gimbiya me kike shiryawa na ranar naɗin sarautar Sultan Amin?"
"Ban fara wani shiri ba kum..."
"Yana da kyau kiyi hakan Aymana, mijinki fa zai karɓi mulki, ai ko don kar ayi maki dariya a gidannan kin jajirce."
Aymana ta ɗan yi shiru "Shi kenan Mama me kike ganin zan shirya?"
"Lokaci ya ƙure amma bari zan duba."
"Ko mi za a yi, ki sanar dani zanyi komai kika ce Mama."
***
Yau Ayda tana gidan Baba Maga yaƙi shine ƙanin Mai martaba, duk wani shirye-shiryen hidimar bikinta a gidan ne suke yi.
Goggo itace uwar gidan Maga yaƙi kuma itace ta zama kamar uwar ɗakin Ayda da yaranta.
Ayda ta aje kayan da ta amsa hannun Kuyangarta, ta ajiye Goggo ta kalleta "Zauna nan, ni ban fahimci komai ba."
"Wajan mi fa Goggo?"
"Har yanzu ba a turo daga cikin gida Mai martaba na nemanki bane?"
Shiru Ayda tayi don dama tana jimawa bata saka Sultan a ido ba balle yanzu da ya zama Sarki tasan zai mata wahalar gani.
"Gaskiya da sake Ayda, sai kin dage, ki jifa yadda yayi ta rawar jiki lokacin da akayi auren shi amma ke ko alamar hakan babu."
"Miye abin yi Goggo?"
Goggo ta miƙe zuwa ɗakin Mijinta, yana ɗan kishingiɗe ta zauna gefe Baba Maga yaƙi ya kalleta, kafin ta fara magana "Na zo akan maganar Ayda ne, har yanzu fa Sultan Amin bai nemi ganinta ba."
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.