MASARAUTA 27

117 25 3
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI ASHIRIN DA BAKWAI. 27*

Kai tsaye ɓangaren Mai martaba Sarki Amin ya sauka, Mai martaba ya ji daɗin ganin shi sosai, Yarima ya saki ƙafa tare da zubewa gaban shi yana kwasar gaisuwa, Mai martaba ya miƙa mashi hannu, har yanzu Amin sam baya bari ya haɗa hannu da Mai martaba saboda girmammawa sai dai kawai ya duƙar da kai.

"Tafiyar rana haka Sultan?"

"Allah ya baka nasara muna son juyawa ne shi ya sa."

"Sannunku da hanya, bari na sa a sanar da zuwan ku cikin gida." Ya faɗa tare da fita.

Aymana tana ɗakin Kaka tana kwance kan kujera, lokaci zuwa lokaci sukan ɗan yi fira, Jakadiya ta shigo da sallama Kaka ce ta amsa.

Ta matsa wajan Aymana tare da durƙushewa "Allah ya ja zamanin ki! Mun samu baƙuncin mutanen Toro, Sultan yana tare da Mai martaba yanzu haka."

Wata iriyar razana Aymana tayi tare da miƙewa, sai kuma tayi ƙoƙarin kau da mamakinta ta hanyar faɗar "Har sun iso?"

"Hakane" Jakadiya ta faɗa tare da miƙewa.

Kaka ta ce "Iye shi ne zai zo ko sanar dani ba ki yi ba, to duk abin ki dai sai..."

Dariya Aymana tayi cikin sanyin murya ta ce "Kaka ko kin san nima bai sanar dani zuwan shi ba."

"Kina nufin baki sani ba."

Aymana ta duƙa tana bawa Kaka labarin yadda sukayi, Kaka tace "Oni ƴa su. Yi maza maza ki shirya."

Aymana ta fice daga ɗakin tayi ɗakin mahaifiyarta, ta shiga tana zuge mazagin rigarta, Umma ta kalleta "Lafiya kuwa?"

"Zan yi shiri ne, Sultan ne ya iso."

Umma ta bita da ido, Aymana ta yi hanyar ɓanɗaki, cikin sauri, ta jima kafin ta fito.

Zata hau shiri Umma ta ce "Kin sa akai mu su abinci kuwa?"

"Shi ya sa nake sauri don na shirya."

Tana maganar tana saka wasu tsadaddun turaruka, ɗakin ya ɗau ƙamshi, wata Atamfa Aymana ta jawo doguwar riga ce sai dai ɗinkin yabi jikinta sosai, har ya fitar da tsayuwar surar jikinta.

Juyowa tayi don Umma ta zuge mata mazagin, sai taga batanan sai Bilkisu dake tsaye tana ƙare mata kallo, ta matsa tana juya baya, Bilkisu ta bi ƙuginta da kallo.

"Gaskiya Gimbiya ɗinkin ya yi min kyau."

"Na gode ƙanwata" ta ɗan yi tattaki ahankali saboda rigar ba ta da walwala sauƙin ma akwai tsaga abayan rigar daga ƙasa.

Zata ɗaura ɗankwali, Bilkisu ta riƙe "Haba jira a ɗan saka maki ko janbaki."

Bata yi mata musu ba, hakan ya ba Bilkisu damar ja mata gira kalar zamani, ta saka mata kwalliya sosai wanann lokacin harda ado a ido sai dai batayi mata amfani da abubuwa masu kyalli ba, haka jammakin ta saka mai kama da fatar ta ne, sai ɗan sheƙi da leɓon yake yi.

Bilkisu ta ɗora mata ɗankwali, ta saka awarwaraye, da sarƙa masu kyau, Aymana ta miƙe tana jawo wata Alkebba ta ɗaga "Sam shigar Gimbiya ba Alƙebba ne daidai ita ba." Cewar Bilkisu

Ajewa kawai tayi ta ɗauko wani mayafi babba, da akai mashi adon duwatsu, sai dai ba shi da kauri sosai.

Aymana ta aza tare da zuwa gaban Mudubin, sai da ta runtse idanuwanta ganin yadda ta sauya da kyau.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now