MASARAUTA 20

126 16 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA ASHIRIN. 20*

Tana ficewa Yarima ya kalli Aymana sai dai bai yi magana ba amma ta gane nufinshi na zai barta, shi kuma ya tafi amsa kiran Mai martaba.

***

Kwana biyu kowa ya ɗan nutsu a gidan, sai dai ko wane ɓangare da kalar abinda yake shiryawa.

A ɓangaren Gimbiya Mai gado sun tabbatarwa kansu Mai martaba ba zai taɓa janye ƙudirin shi ba na zaman Yarima Amin sarki, hakan ya sa suka kauda baƙin cikin su a fili yayin da zukatan su babu yalwar farinciki a ciki.

Jakadiyya ta gyara zama, ta maida hankalinta kan Gimbiya Mai gado "Allah shi taimake ki ni kaina bana farin cikin komawar mulki hannun Aminu."

"Yanzu miye abin yi?"

Shiru na tsawon lokaci, kafin Jakadiyya tace "ki yi tunani uwar ɗakina."

Ajiyar zuciya ta yi "Ba na so Aminu ya taɓa jin daɗin mulkin shi, bana so ya san farin ciki dangane da mulkin da zai gudanar, ina so ya ji baƙin ciki ta yadda da kan shi zai sauka mulki abaiwa Saifu."

"Hakan yayi komai zai gudana kamar yadda kika buƙata."

***
Tunda aka sanar ranar naɗin sarautar Yarima Amin, ranar zai zama ranar da za a bashi sandar girma, suke ta murna kowa na gidan yasan lokacin gyara yazo a masarautar.

Waziri ne zaune gaban Mai martaba wannan lokacin akwai nuna sanyin jiki da kuma miƙa wuya "Allah shi taimake ka, dama mun riga mun amince da duk hukuncin daka yanke akanmu, kuma muna masu biyayya a gareka."

Mai martaba ya kalle shi sai dai bai yi magana ba Waziri ya cigaba "A karo na babu adadi nake roƙarwa Mai sunan manya (Ayda) alfarmar aurenta da Sarki Amin."

Mai martaba ya kalleshi, sai kuma ya soma tunanin, lallai ya san Waziri shi ne kan gaba a cikin mutanen da  za su shiga hassadar Aminu, haka yasa tun bayan da yace zai ɗaura shi a matsayin Sarki yake ta tunanin hanyar da zai yi don kawar da cuta a tsakaninsu.

Dogon numfashi ya ja, wata zuciyar ta sanar da shi Auren Yarima da Ayda shi ne zai sa ya toshe cutarwa daga Waziri zuwa ga Yarima Amin.

Ɗagowa yayi ya kalli Waziri "Zan zauna da Sultan Amin."

"Na gode ranka shi daɗe." Ya faɗa tare da miƙewa ya sunkuya "Na barka lafiya."

***

Gimbiya Ummi tana gefen Maimartaba ta amsa kiran da yayi mata na gaggawa, sai dai ta soma gundira tare da ƙagaran jin kiran da yayi mata.

"Wace hanya kike gani za mubi don kange Sultan Amin daga Makircin Waziri da magoya bayan shi."

Shiru tayi na tsayin lokaci, maganar ta shige ta, ta san akwai cutarwa mai tsanani "Allah ja kwananka, babu zance a baki na, amma nasan akwai lauje cikin naɗi!"

Miƙewa yayi tsaye "Na yanke shawarar haɗa auren Sultan Amin da Ayda."

Razana Ummi tayi cikin kaɗuwa "Amma Mai mar..."

Ɗaga mata hannu yayi "Na gama hukunci na, hakan shi ne zai ba Sultan kariya, ki yi nazari akan maganar."

Sam Gimbiya Ummi bata son haɗa wani abu da mutanen gidan Waziri balle yaronta ɗaya tilo, shiru tayi na daƙiƙu, ta tabbatar haɗa aurenne kawai mafita, idan ma zata ƙi amincewa babu wata hanya ta yin gardama da hukuncin Mai martaba.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now