Hausa Arab by CutyFantasia page1

4.6K 147 7
                                    

A hankali tattausan sauti me dadi na ringtone din iphone ya dinga shiga kunnena

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.


A hankali tattausan sauti me dadi na ringtone din iphone ya dinga shiga kunnena......juyawa nayi daya gefen naci gaba da baccina me dadi peacefully saidai sam mai kiran yaki hakura domin tana katsewa wani kiran zai sake shigowa. Dakyar na bude idanuna da nannauyan bacci ya risinar na kai kwayar idanuna kan side drower inda wayar ke aje na saka hannu na dauko ina danasanin rashin sa wayar a silent. Saidai ganin sunan da ke kan screen din wayar ya sanyani swiping wayar da sauri cikin doki. Da muryar da bacci ya harde nace "Mamina good morning" can bangaren Mamin kuwa cewa tayi "wanne irin bacci kike zara? Na kira ya kai sau goma fa?" Tausasa murya nayi nace "Mami i slept very late wallahi shiyasa baccin yayi nauyi.i'm sorry" cikin sanyi tace "issokay cewa zanyi ki tambayi Dada ki shigo da yamma inason ganinki" murmushi nayi me sauti na amsa da "ok Mami zan gaya mata sai nazo" da haka mukai sallama na aje wayar. Agogon wayar na duba 11:00am. nayi maza na mike na shige toilet ina mamakin yanda rana tayi ina ta bacci. Brush kawai nayi da alwala na futo sannan na zura katon hijab fari sol na shimfida sallaya na gabatar da sallar walha raka'a hudu wadda bana iya fashinta komai tsanani. Ina idarwa na ninke kayan sallar na futo parlour. Dada na samu zaune akan kujera Daddy na kasan kujerar yana danna mata kafafunta da suka kumbura a hankali cikin tausasawa.
Cikin nustuwa na iso na zauna na soma gayar da Dada ta amsa cike da kulawa sannan na gayar da Daddy. "Sai yanzu kika tashi Zara?" Inji Daddy. Dada ce tace ai yau babu makaranta bacci ake a more...sai an biya bashin na kwanaki biyar din da ba'ai ba." Murmushi yayi yace "Dada weekend din kenan" har na mike zan tafi Daddy yace "ahmm Zara ran Monday ki shirya da wuri babu zuwa makaranta zakuje da Omar kiyi renewing passport dinki don inaga a satin nan zamu tafi Jedda da Dada kafar nan ta matsa mata" duk da gabana yayi mugun faduwa da jin zancen tafiyar ban kasa risinawa nace "toh" ba. Sannan na wuce kitchen na samu Baba Rabi tana goge goge. Da murmushi tace "zahra'u an taso?" Nima murmushin na maida mata sannan na gayar da ita. Na dora da cewa "me aka yi mana ina bude warmers din dake kan table. "Lalala..wow" Baba Rabi moimoi?" Na fada ina murmushi domin ina matukar son naci moi moi da kunu da safe fiye da komai. "Ai naga yau ba makaranta nasan ba da wuri zaki tashi ba har na kammala kulelen. Cikin jin dadi nace "nagode sosai Baba rabi... kawo plate da yaji yanzu na tashe shi aiki" dariya take sosai taje ta dauko mun plate da cup tayi serving dina delish dinta na alalen da aka nannade cikin ganye yaji kwai da kifi da kuma kunun tsamiya mai dan karen dadi. Inaci ina santi tana yimun dariya har na kammala na mike na koma dakina. A gado na fada ina tunanin wannan tafiya da ake jajibowa kullum ba'a la'akari da karatuna...tun ina sha'awar tafiyar har na daina. Na zama jelar Dada duk inda zata je sai an hada dani. Ya ilahil arshi ya zanyi da karatuna da ya dau zafi wanda muke dab da kammalawa. Mtsweeew. .gaba daya raina ya gama baci wataran saura kiris ayimun repeating a school sai da Daddy yaje yayi bayani da kansa.
Karfe biyar na kammala shirina cikin sassaukar shiga na dau key nayiwa Dada sallama na futo harabar gidan wajen adana motoci na isa na bude motata na shiga ina kiran sunan Allah. Bayan na kunna motar na saka CD nan da nan sautin muryar Maher zain ta soma tashi cikin wakar "Madeena Madeena" sannan na ja motar na futa daga cikin gidan ina bin wakar a hankali nutsuwa tana saukarmun da nishadi me yawa a dalilin son da nakewa wannan mawaki da wakokinsa.... har na isa Ministers hill.
A bedroom na samu Mami ta baza kaya a tsakar dakin kamar hauka. Atamfofi,laces,voils da sauransu.
A comfy bed din Mami na kwanta ina "wash Allah i missed this bed" kallona kawai ta tsaya tana yi har ma ta bani dariya. Cewa nayi "Mami me nayi ne?" Girgiza kai tai tace "babu Allah ya shirya" na kyalkyale da dariya. Sannan na soma gaisheta. Sake bararrajewa nayi a gadon ina sinsinar sassanyan turaren da ya like a jikin bedsheet din.
Cewa tayi "kinga ba dadin gado na kiraki kiji ba kayan sallarki zaki zaba zan kai shago kafin aiki yayi mana yawa. Tsalle na buga na tashi ina cewa "wow...that's my mami" "ah ah karki balla mun gado...meye hakane Zara?kamar wata yarinya zakimun tsalle a gado? Sauka ki duba kiyi maza kizo ki tafi banason kina driving da dare. Tare muka shiga duddubawa tana tayani na zaba duk wanda nakeso muka zuba a leda.
Sannan na dubeta cikin soyayya mara misaltuwa nace "Mami nagode Allah ya kara arziki" murmushi kawai tayi tace amin. Na sake cewa "Mami kinsan wai nextweek zamu tafi Jeddah da Dada? Wai meyasa akemun haka? Karatuna ya dau zafi gashi muna shirye shiryen grad duk ba'a dubawa kawai sai a daukeni asani a gaba mu tafi." Na karasa maganar cikin bacin rai.
Dafani Mami tayi cike da kulawa tace "haba Zara Dada ce fa? You are the only female grandchild acikin jikokinta ku 25 bayan Nuratu....she worths kowanne kulawa da taimako Zara kiyi hakuri zama da manya sai an yi hakuri an daure kinji? Kafar tata ce?" A sanyaye na amsa "eh duk sun kumbura ko waje bata iya takawa ta futa." Cikin tausayawa Mami tace "ayyah wannan kafa ta takura mata Allah ya sauwake" nace "amin." Sannan ta sake cewa "yauwa Zara plaease karki bata rai har ta gane bakyason tafiyar kinji? Kici gaba da yi mata biyayya. Dada tana da matukar girma a wajena ta nunamun so da kauna irin wanda bazan manta ba. Zanje school dinku nayi reporting tun kafin tafiyar za'asan yanda za'ai" cikin jindadi na rungumeta ina cewa "yauwa Mamina....zanyi duk yanda kikace..i love you" kankameni tayi a jikinta tace "i love my baby too" duk yanda naso muyi hira sosai Mami ki tayi ta koroni gida wai batason magrib tayimun a waje batason tukin dare. Haka na dawo cike da kewar Mamin tawa.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now