HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE SEVEN

1.2K 81 2
                                    


Futowata daga exam kenan na nemi waje cikin kujerun da ke kafe a harabar makarantar mu na zauna. Tunani nakeyi akan zuwan Imamu gidanmu a yau wanda bansan yanda zai kasance ba. Wayata na zaro a hankali na boye daga cikin jakar nake dannawa na bude messages Imam da suka shigo yanzun nan! Sako ne akan fatan alkhairi da samun nasara a jarrabawata da kuma kalamai masu saka kwarin guiwa da kwantar da hankali. A rayuwa ban taba samun wanda zuciyata ta kamu da sonsa ta farat daya raina yake shaukin kaunarsa ba irin Imamu. Domin mutum ne shi mai tsananin kulawa da nuna so da kyautatawa ga abinda yaje kauna. Tunda muka hadu dashi yau sati biyu bai taba ko kusa da gayamun maganar da banji dadi ba. Mutum ne shi mai hakuri da juriya da kuma sanin ya kamata. Yasan darajar mutane fiye da tunani. Sau dayawa idan ya zauna yana gayamun kalamai akan yanda yake ji a kaina sai naga kamar a mafarki domin mutum ne shi wanda Allah yayi wa baiwa irin wadda zai iya kowacce irin isa da kasaita. Yana da kyau, kudi, ilmi, gata da duk wani abu da yake sa mutum yaji kansa amma sam Imam bai damu da wannan ba. Rayuwa yake da kowa cikin mutuntawa da darajawa.
Ya gayamun shine first born a gidan
Late. Eng.Mukhtar Jega da Dr. Sa'adatu Karaye. Mahaifinsa ya rasu ne a sakamakon hadarin jirgin sama tun yana shekaru sha biyar. Mahaifiyarsu ce ke dawainiya dasu.
Su uku ne shi kadai namiji sai kannensa yan mata Yusra da Yasmin. Duka suna kasar waje suna karatu.
A halin yanzu shi yake kula da duk wani harakar dukiyarsu musamman construction conpanies din mahaifinsu da ke da rassai a kasashen duniya. Har Eng.Mukhtar ya mutu mutum ne wadda aka sani da zuciya mai kyau da kuma kyautatawa iyali ga zafin nema ga tausayin da jin kan na kasa da shi da yawan alkhairi. don haka mutuwarsa ta girgiza zukata dayawa. Ashe kuwa Imam ba a kasa ya samo nagartattun halayensa ba. Zan iya cewa addu'ar Mamina da Ya Nuratu ta amsu a kaina na samun miji nagari idan har Allah yasa Imamu ya kasance miji a gareni.

Ji nayi wani lallausan hannu ya dafa kafadata wanda ya sanyani saurin juyowa. Aisha ce zaune a gefena tana murmushi "anya kuwa Juliet kinyi abun kirki a exam din nan?" Ta fada cike da tsokana! Harara na watsa mata nace "No sunan Romeo na cika paper dashi" ta kuwa kwashe da dariya harda rike ciki.
Sannan kuma ta dago kamar me tunanin wani abu idonta cike da hawaye tace "zara i'm surely going to miss you wallah.....i will miss every moment da muka yi tare a school din nan!"
Jikina ne yayi bala'in sanyi a sakamakon tunawar da nayi saura sati biyu ya rage mana mu kammala secondary school. Shikenan mun rabu da Aisha. Mun daina ganin juna kullum, musamman ma da ita babanta jira kawai yake ta gama ya kaita Harvard's. Shikenan rayuwa zata juya kowa ya kama gabanshi.
Nikam bansan meye makowamata ba. Zanci gaba ne da karatun? A ina? Dada zata hanani? Ko kowa aure zanyi? Wannnan tunanin da ma wasu ya sanyani hawaye shabe shabe. muka rungume juna muka shiga rera kukan tausayin junanmu.
"I will miss you more Aisha.. i will miss you sooo much!" Cikin kuka nake maganar. Rabuwa da junanmu ba abu ne mai sauki ba domin ni da Aisha kamar tagwaye muka taso. Bacci kadai ke rabamu. Tun daga playgroup muke tare da ita har kawo wannan lokaci. Islamiyyar mu daya komai tare mukeyi a rayuwa. Tuni muka kulla iyayenmu alaka mai karfi a dalilin shakuwar mu har ya kasance daya zaije gidan daya yayi kwanaki wani lokacin ma idan iyayenta sunyi tafiya muna cikin karatu gidanmu take dawowa mu dinga tafiya school tare. Babu abinda muke boyewa junanmu. Babu abinda bamu sani game da juna ba. Mun wuce kawaye mun zarce aminai mun zama yan'uwa na jiki! Don haka rabuwa lokaci daya baya abu ne mai sauki a garemu ba. Sai da mukayi mai isarmu sannan muka share hawaye kowa cikinsa a mace. Cikin low tone tace "yaune Imam zaizo din?" A sanyaye na daga mata kai sannan na dora da cewa "zaki zo da wuri dai ko?" Ta amsa "insha Allah ina komawa zan shirya na taho" haka muka rabu duk zuciyarmu babu dadi da alkawarin zatazo gida mu tarbi babban bako tare. Don na riga na gama cika shi da labarinta kamar yanda shima na cika shi da labarinta. Sai dai kowa ban gaya masa sunan kowa ba ban gaya masa komai na rayuwar kowa ba sai dai alakar da ke tsakaninmu nace sai ranar da muka hadu gabadaya za'ai wannan intro din.

LIVER POOL LONDON

A hankali yake tukin cike da gajiya ya ware heater cikin motar duk da cewa lokacin summer ne amma ruwan da aka kusan wuni ana yi ya sauya garin gabadaya ya dau wani irin sanyi mai ratsa kashi. Musamman ga mutane irinshi da basa shiri da sanyin ko kadan. Sautin kira'ar sheik Abdurrahman Sudaith ne cikin Surat Maryam yake tashi a hankali cikin motar yana saukar masa da wata irin nutsuwa.
Bayan ya isa gidan ya zagaya gareji yayi parking motar sai ya kwantar da kujerar baya yana sauraren karatun har zuwa karshen surar. Sannan ya balle murfin ya futo. Ya bude kofar baya ya kwaso wasu files da kuma jakar laptop dinshi ya soma takowa cikin gidan a hankali kamar me tausayin taka kasar don tsananin gajiya.
A kitchen ya samu Sherifah tana ta goge goge. "Good evening sir" ta fada cikin ladabi. Ba tare da ya dubeta ba ya amsa sannan ya dora da cewa "you do not have to cook dinner ..." ta sake amsawa cikin ladabi "yes sir" daga nan ya karasa falon ya aje tarkacen hannunsa ya wuce daki. A hankali ya soma cire boturan fara kal din labcoat din da ke jikinshi daya bayan daya sannan ya zare ta. nan da nan bakar suit din da ke jikinsa samfurin Armani ta bayyana. Sai da ya zare komai a aje sannan ya shiga toilet ya sakarwa kansa warm and relaxing shower.
Mintina talatin ya kammala wankan ya futo yana kamshin designers mayukan wankan da yayi amfani dasu a jikinsa da sumar kansa.
Bacci ne fal a idonsa wanda ya hanashi ko shiryawa ya haye english royal bed din nashi ya soma bacci peacefully.
Bai bude idanu ba sai karfe shida da rabi bakinsa dauke da addu'ar farkawa daga bacci. "Ya salam! Ya fada lokacin da ya duba agogon wayarsa. Yayi missing sallar la'asar . Toilet ya fada ya watsa ruwa cikin sauri tare da alwala ya futo ya shinfida sallaya yayi sallah. Mintina ashirin da biyu yana azkar dinsa da addu'o'i kafin ya nade kayan sallar ya mike. Alarm din wayarshi ne ya soma kara ya karasa ya duba. Reminder din da ya saka ke tuna mishi yau ne ranar da Eng.Garba Galadanci ya gayyace shi dinner a gidanshi. Wani mugun tsaki yayi tare da dafe kansa. Iya gajiya ya gaji wani stressful meeting sukai da yayi exhausting dinshi. Gashi gidan ba kusa ba. can cikin garin London ne. Sai dai ba yanda zaiyi ya saba alkawari musamman ga mutum irin Eng. Mai karamci da sanin kimar dan'adam. Gaban mudubin ya isa ya bude drower ya zaro hand drayer ya soma busar da jikakken gashin da ya kwanta yalo yalo a kansa tare da shafe shi da mai ya dauki wani irin kyalli da sheki.
Mintina goma ya kammala shiryawa cikin shedda hilton blue black wadda ta dauki dinkin hannu irin na mutanen kasar Senegal. Daga kasan rigar ya saka sweater mara nauyi ya daure hannunsa da ruwan sarkar agogon "Dior" silver. Bai saka hula ba sai scarf din burberry ruwan toka. da yayi amfashi dashi wajen nade wuyansa. Wanda ya maida shi unique. A bakin gadon ya zauna yana sinkife kafarsa da covered shoe dai dai kalar sheddar sannan ya feshe jikinsa da turarensa na yau da kullum wato LA NUIT na LV ya kara da SAFARI na Ralph Lauren. .
Ya kwashi wayoyinsa ya zuba a aljihu da wallet dinshi ya futo. Tuni Sherifah ta tafi don haka ya kulle gidan ta baya da gaba ya futo. Motar kamfani da yayi kira ya tsaya jira minti uku ta iso ya shiga don bazai iya driving ba.
Yana shiga motar ya ciro wayarsa ya soma danna lambobin Nigeria. Bugu biyu wanda yake kiran ya dauka "Hello Hausa Arab ina ka shiga ne?"
Cikin taushin murya yace "kyaleni Faisal wallahi I'm stuck cikin ayyuka dayawa sai da na dawo nake ganin miscalls dinka" cikin tausayawa Faisal yace "kaga ka raba kanka da wannan matsanancin aikin in ba haka wallahi ka tsufa da wuri." Murmushi yayi duka kumatunsa suka lotsa yace "tohh naji...yanzu dai me ya faru?" Cikin tsananin farinciki Faisal yace "su Abba sunje gidansu Ihsan an tambaya an bani an saka rana watanni shida" fadada murmushinsa yayi yace "Alhamdulillah Allahumma barik. Allah ya sanya albarka Friend i'm so happy for you" Faisal yace "thank you aboki..Allah ubangiji ya kawo mana ranar da wata zata sace mana zuciyarka kaima muzo musha shagali" dariya sosai ya dinga yi "you are not serious" ya fada da hardadden harshensa. Faisal ya sake cewa "ohk... joke aside my wedding is in six months and you are my best friend my favourite brother....dont say ban gaya maka ba billahil azeem kaki tahowa Nigeria aurena kar ka sake tunanin ma kasanni" cikin dariya yace "wait...calm down! Ka bar rantsuwar mana sai kaga lokacin yayi banzo ba." Faisal cikin nutsuwa ya sake cewa "ina gaya maka ne don kasani. Rabonka da Nigeria shekara goma duk abinda ya faru kace aiki kamar inji sai angama kayi ta baiwa mutum hakuri toh wallahi ba dai a wannan lokacin ba i am telling you this from the bottom of my heart rashin zuwanka wajen bikina zai iya lalata duk wata alaka dake tsakaninmu" yana kaiwa nan ya katse wayarsa.
Wata irin iska ya furzar mai zafi zuciyarsa tana azalzala. Duk lokacin da ya tuna gida sai yaji wani irin faduwar gaba da tashin hankali. Toh amma this time shi kansa yasan bazai iya dojewa ba he cant escape this. Ba zai iya yiwa Faisal haka ba. Mutumin da ya tsaya masa a rayuwarsa a kowanne lokaci a kowanne yanayi wanda yake karanta zuciyarsa ba tare da yayi magana ba. Wanda yasha shiga damuwa da masifa iri iri a dalilinsa wanda yake tasowa takanas ya zo wajenshi ya ganshi yaji damuwarshi. Ba zai disappointing dinshi a wannan babbar ranar ba. Dole ya soma shirin tafiya Nigeria saboda mutane biyu masu muhimmanci a rayuwarshi.
Wannan tunanin ya sauya mishi mood gabadaya ransa ya jagule kirjinsa yayi nauyi kansa ya dau zafi. A hankali ya jingina kansa jikin kujerar motar ya dinga maimaita "lahaula wala kuwwata illa billahil aliyyul azeem" har suka isa gidan Eng.Garba da ke Sussex Garden. Gidan yana opposite gidan Daddy na garin London. Cikin nutsuwa ya isa kofar ya taka steps din guda uku sannan ya danna kararrawa.
Minti daya akazo aka bude kofar!
Take idanunsa sukai arangama da santaleleliyar black beauty mai wani irin tsayi da za kai mamaki mace ce ta mallakeshi. Duk da tsayin ne kawai babu structure mai kyau. Tana sanye cikin suit din "George" na mata jajaye.
Dogon gashinta cikin pony tail. Kana ganinta kaga rainon turai.
Gabadaya kyawun da take tunanin tana da shi ta matso tana blushing.
Mamaki ya kamashi ..me take nufi da yi mishi irin wannan tarbar? Oho! Ya baiwa kansa answer. Ganin bata da niyyar matsawa ya sanya ya kunna radion bakinsa ya murdo tashar CNN yace "hello! gimme way" sai lokacin ta farga da kataborar da takeyi ta matsa mishi a hankali ya kutsa kai cikin falon..



Hello my people!! Eid Mubarak!!💞💞
From Hausa Arab to your Family.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now