Announcement!

918 55 24
                                    

Assalamu Alaikum beautiful readers of Hausa Arab! Dafatan kuna cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.

I want to thank you for your love and support, ina godiya mara iyaka akan goyan bayanku da kwarin guiwa da kuke bani da kuma kauna ga rubutuna.
I can't thank you enough! I'm highly indebted and no word can express my sincere gratitude! Allah ya bar so da kauna.

Bayan haka, i am sorry to tell you Hausa Arab zai dakata daga nan a matsayin part1 saboda wasu dalilai bazan ci gaba da rubuta shi ba.
Idan kun tuna na gaya muku cewa ba'a rubuce yake ba, sai zanyi posting idea take zuwa mun, a yanzu labarin yazo gabar da yake bukatar nutsuwa da research da zuzzurfan nazari, rubutu babu bincike babu ilmi ba zai samu amfanin da ake bukata a cikinsa ba. Don haka zan dakata daga nan sai lokacin da na kammala rubuta part 2 din shi sannan zan sanar da ku na fara yi muku posting akai akai har zuwa karshen labarin.

Nasan ba zakuso hakan ba kuma ba zakuji dadi ba, amma zaku fi jin rashin dadi idan na soma yi muku shirme da Kwan-gaba Kwan-baya a cikin labarin. Yanda ya dauko daga farko zuwa yanzu  kuma yabawa haka nakeso na kare shi bai gundireku ba. Sannan inaso sakon ciki ya futo sosai tushen labari ya bayyana cikin tsari labarin ya kai karshe ba tare da ma'anarsa ta sauka ba.

Ina fatan zakuyi mun afuwa da rashin jindadin da hakan zai haifar a gare ku.
Sannan ina yi muku albishir da sabon littafina mai suna RAI DAI Wanda zai maye gurbin HAUSA ARAB. Na tabbatar zai fi HAUSA ARAB karbuwa a gare ku.

RAI DAI shine littafi na biyu da na rubuta shekaru 3 da suka wuce kuma nake sa ran zai nishadantar da ku ya fadakar ya kuma kayatar. Labari ne mai ratsa zuciya da tsuma rai.

Ina fatan zaku ci gaba da goya mun baya da bani kwarin guiwa kamar yanda kukayi mun a HAUSA ARAB. yana nan a saman shafina kuma insha Allah cikin kankanin lokaci zai soma sauka akan shafin.

Wani albishir kuma shine zaku dinga samun post akai akai ba jinkiri kamar Hausa Arab. Insha Allahu.

Ma'assalam
Cutyfantasiaa.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now