Hausa💫💫 Arab by Cutyfantasia page2

1.6K 91 10
                                    

Halittar da na gani tsaye a bakin kofar  kai tsaye bazan ita tantance nationality dinsa ba amma idan akace nayi kiyasi toh zan iya cewa ya bullo ne daga Sudan ko kuma halfcast of Arab and Africa

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.


Halittar da na gani tsaye a bakin kofar kai tsaye bazan ita tantance nationality dinsa ba amma idan akace nayi kiyasi toh zan iya cewa ya bullo ne daga Sudan ko kuma halfcast of Arab and Africa. Wani dogon balarabe ne mai duhun fata wato ba fari tas ba amma ya zarce layin bakake wata irin kala me bayyana hutu da kwanciyar hankali da cikakkiyar samun kulawa ta kowanne bangare. Dogon gaske ne kamar reshen bishiya mai wata irin structure ta mazan da suka amsa sunansu. Kansa kamar an kifa kwando da wata irin yala yalan suma baka wul ta kanannade sai sheki take. Hakana wannan gashin ya biyo kyakykyawar doguwar fuskarsa ta kewaye ta dira a habarsa kamar an zana da biro. Hancinsa kamar kasa hannu ka dauke saboda tsini..idanunsa kuwa dara dara ne farare sol masu lumshe kansu ba tare da umarni ba. Yana sanye cikin coffee jeans da farar shirt ya ratayo wuyansa da scalf din "burberry" yayinda yake rataye da jakar laptop dinsa a kafadarsa. Nidai sandarewa nayi ina kallon wannan beautiful creature of Allah!! Kamar wata doluwa.
"Hey give me way and stop staring at me like an alien" Ya Ilahi!! Da wani irin accent yayi amfani wanda zai sake jefaka tunanin nationality dinsa domin harshen a harde yake da yarika dayawa wanda suka kasa barin yare guda daya yayi aikinsa. Is he an Arab? French? Sudanese? Indian? Black american? Oho!
A guje Amal ta taho tana ihu kamar zata fadi "welcome Uncle" ya tare ta da wani wide smile duka kumatunsa suka koma ciki(dimple)!! fatabarakallahu ahsanul khaliqeena.! Nidai tunda nake ban taba ganin halitta me kyau kwarjini da daukar hankali irin wannan bawan Allah ba. Mutum kamar aljani? Kaurin girkina ne ya sanyani dawowa daga hayyacina nayi kitchen din a guje. Na bar Auwal na shigo da akwatina designers bakake wul.a raina nace "wannan wanene?? Kuma ya akai Amal ta sanshi? Ko dai irin yayan abokan Daddy ne? Da alama dai wani babban mutum ne don naga yanda Auwal yake girmama shi kamar zai masa sujjada.
Ina girkin ina tunane tunane har na kammala tuka lafiyayyen tuwon shinkafa na nade shi cikin leda nasa a warmers. Sannan na hada miyar busashshiyar kubewa na burge mata kaji suka ragargaje aciki. Gefe guda kuma soup din naman rago ne da dankali. Ga kunun gyada sai kamshi yake. Idan muna wannan gidan yanda kasan a Nigeria domin komai muna taho dashi na amfani irin na gida hakana Hajiya mai abinci tana aje komai. girki ake kaman ana Nigeria a kullum saidai idan ka gaji da ci kaje ka siyo na larabawa a wuraren abincinsu. Ko kuma na kamfani irinsu mc Donalds da KFC.
Bayan na kammala na gyara kitchen din tsaf sannan nan na kai kayan abincin sama na shimfida ledar cin abinci na jera komai yanda ya kamata kafin na shiga toilet na watsa ruwa saboda kamshin abincin da ya likemun a jiki. Wata purple silk gown na zura na dora hijab na futo jin shigowarsu Dada.

Bayan sunyi sallah ne na daga wayar falon na kira dakin Daddy nace masa angama. Sannan na zauna na fara serving din su Dada. Minti biyar Daddy ya murda kofa ya shigo cikin sallama duka muka amsa a ladabce tare da mishi sannu. Yanayin saukin kai da sanin darajar dan'adam na Daddy yana matukar bani mamaki da sha'awa. Duk iya dukiyar da ya tara bai sanya shi rage biyayya ga mahaifiyarsa ba. Kamar zai mata sujjada idan yana gabanta. Ya baro duka ayyukansa da harkokinsa ya dauko ta a jirginsa musamman don a duba lafiyarta. Duk sanda za'a kai Dada asibiti toh da Daddy ne saidai idan munje munga likita ya tafi ya barmu ko kuma mu mu soma tafiya ya same mu acan. Hakanan garemu wani irin mutum ne mai kulawa da karamci da kyautatawa da wuya kaji kalmar da zata bata maka rai daga bakinsa sai dai nasiha da rarrashi kai ba zakace Dada ce ta haife shi ba.
Yana zama aka sake murda kofar a hankali. Santalelen balaraben dazu ne ya shigo sanye cikin jallabiyya fara sol wadda ta bayyana broad figure dinshi. Sumar nan kamar an kufa masa ita ta dan cukurkude alamar ba'a bata kulawar da aka saba bata ba .hannunsa rike da dogon farin tasbih. Sai ya koma kamar balaraben madina.
Yana sallama Dada ta wancakalar da plate din abincinta ta mike tsaye dakyar kamar zata fadi har Daddy yana tayi a hankali. Ai bata ma bi ta kansa ba ta soma rangadawa matashin kirari cikin tsananin murna da dokin ganinshi. Da sauri ya isa gareta ya rungumeta yana cewa "i miss you soo much granny" dakyar ta bambare daga jikinsa tana hawayen murya sannan ya zaunar da ita ya wuce wajen Daddy shima ya rungume shi ya dawo gaban kujerar Dada ya zauna ya soma gayar dasu cikin ladabi. Sannan ya dubi Ya Nuratu yace "sister ya kike?" Da wani wawakeken smile dinta ta sauya maganar da gaisuwa cike da ladabi da so da kauna. Sai na koma bare a cikinsu.
Kaina ne ya daure tamau tun lokacin da mutumin ya shigo Dada ta barar da abincin da take ta zuzuta dadinsa ta mike kan kafafun da ake lallabawa dakyar don murnar ganinsa. Sannan Daddy expression din da ke kan fuskarsa ya nuna zallar so da kauna mara gauraye akan wannan bawan Allah. Toh ita kuma Nuratu ina tasan shi har yayi sabo da diyarta Amal haka? Duka wadannan tambayoyin ne suka ta yawo a kaina ban ankara ba naji Dada tana cewa "ke Zara bakiga Yayanku ba ki gaishe shi?" (A gidan wa ya zama Yayana kuma) a fili kam kasa nayi da kai na gayar da shi ya amsa a gwasale kamar bayaso. Daddy ne yace "Zaran marigayi ce fah" da wani irin mamaki ya zubo mun duka idanunsa da dafin da ke dake cikinsu wanda suka sanya ni kasa da tawa kwayar idon. Cikin hardadden yaren shi yace "what? Daddy Zaran Mami? She's all grown up!..Daddy bangane ta ba" kafin Daddyn yace wani abu Dada ta soma zazzaga masifa kamar ba ita ce me runguma da kirarin dazu ba.
"To dama ina zaka ganeta? Zaka soma yi mana turancin banza da wofi?.Ina zaka santa ka tsame kanka daga dangi? Ina bakin halinka zai bari ka gane wani bayan zumuncin ba damunka yayi ba? Ka mayar da kanka baturen karfi da yaji ka zubar da yan'uwa ka rungumi masu jajayen kunnuwa wadanda basu san Allah da Annabi ba sai hauka da sakarci................ta inda ta shiga ba tanan take futa ba.
A hankali na sulale na bar falon ina tausayin wannan bawan Allah domin babu wanda ya kaini sanin zafin fadan Dada. Akan Dada tayi ma fada gara a gayyato karti a basu dorina suyima dan iskan duka domin idan zata yima fada ko zata zageka sai ta je ta nemo kakan kakan kakanka ta lalubo aibunsa ta hadashi da kai ta zage ku tass.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now