HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE T8HIRTY-TWO

734 61 9
                                    

Jikina a bala'in sanyaye nake kallon Aisha wadda tunda ta fara magana ta dukar da kai bata dago ba. sai jikinta da yake rawa a hankali.

"Ina dawowa gida Zara na tuna cewa na bar diary dina a motar Imamu. Nayi ta buga wayarshi bai dauka ba shine nayi masa text ina rokonsa akan kar ya budemun diary din nan! bai saurareni ba har bayan kwana biyu, sannan ya shigo mun da wani salon da ya gigitani ya tsundumani a fargaba da tashin hankali. Zara ya budemun sirrina ya karanta komai na cikin diary din har da abubuwan da basu shafe shi ba duka ya gani. Anan artabu ya balle a tsakaninmu, nayi masa kaca kaca don har lokacin bai bani littafin ba. tun ina masa ihu da barazana har na sauko na dinga bashi hakuri cikin lallami amma Imam bai saurareni ba. Rannan sai kawai ya turamun text akan cewa kamar yanda nake sonshi haka shima tunda ya fara ganina na shiga ransa don haka duk yanda za'ai sai ya sameni ta kowanne hali. hankalina yayi masifar tashi sai naga magana a waya ma bata da amfani a take na mayar masa da amsa cewa mu hadu a park and zoo.
A ranar nayi masa magiya nayi kuka nayi masa nasiha nayi masa wa'azi na fahimtar da shi alakar da ke tsakanina da ke, na kuma tabbatar masa da cewa na daina sonsa tun lokacin na ganshi a matsayin saurayin aminiyata! Zara wallahi idan da ace Imamu yana da Imani ko na kwayar zarra ne da ya saurareni kuma ya yarda da abinda na gaya masa ya girmama amincinmu amma sai yayi mun lamfo kamar ya amince a dai dai wannan lokacin ne kuma Jidda ta soma mummunan takunta a kaina tunda na bayyana mata sirrina. ita ta dinga bani shawara akan abubuwa masu yawa, akan na kwantar da hankalina komai zaiyi dai dai! sannan ta bani shawarar lallai babu abinda ya kamata irin na sameki nayi miki bayani mu warware komai. sosai na gamsu da ita da bayanin da tayi mun kuma na saka a raina ana kammala bikin su Ihsan zan warware miki komai.Ban taba tunanin bakinsu daya da Imam ba kuma bansan ta hanyar daya bi ya hade kai da ita ba, ni dai kawai nasan Jidda babu abinda ba zatayi saboda kudi ba.
A ranar dinner idan ba zaki manta ba zakiga na sakar miki fuska kuma na ware muna walwalarmu. na samu wannan nishadin ne a tunanin da nayi kan cewa zan fuskance ki mu warware matsalarmu.
Jidda ce ta dinga kirana a waya, ban dauka ba nayi mata text akan ina wajen biki akwai hayaniya. sai ta mun text cewa tana wajen bukin na futo.
Nayi mamaki kwarai domin ta tace mun ba zata samu damar halartar bikin ba don haka na futo da sauri.
ganinta ya bani mamaki don babu shirin biki a tare da ita. cewa tayi mun "Aisha taimakon zakiyi don girman Allah kizo muje" cikin rashin fahimta nace mata "ina zamuje bakiga ina cikin hidimar biki bane ya za'ai na tafi yanzu?" halin da ta nuna mun tana ciki ya sanyani tilas na hakura na bita. Anan muka hadu da Mami tana shigo da baki tace mun tafiya zanyi? sai kawai Jidda tace mata eh! ita kanta Mamin bakin da suke tare da ita ne suka dauke mata hankalin tsayawa bincikar mu dalilin tafiya. wajen motarta mukaje muka shiga ina kullo murfin motar na juyo nai mata magana kenan ta kadamun wani handkerchief a fuskata daga nan ban sake sanin inda nake ba sai farkawa nayi na ganni akan gado cikin wani dakin da ko a mafarki ban taba zuwa ba. a zabure na mike tsaye ina waige waige. sai naga rana gabadaya ta keto ta cikin fararen curtain din dakin wanda ya nuna mun cewa safiya ce. Anan nagane cewa kwana nayi a wajen....domin tunda muka shiga mota da Jidda ni dai ban sake tuna komai ba.
hankalina yayi masifar tashi nayi kofa da sauri zan bude sai naga ana kokarin murda kofar a shigo da alama da key aka kulleta daga waje. tsayawa nayi cak ina sauraren abinda zai biyo baya. Babu zato babu tsammani naga Imam ya shigo hannunshi dauke da tray wanda aka hada kayan abinci akai!"
********************************
zuwa wannan lokacin nidai na zama mutum mutumi ko yau na kasa samu a bakina na hadiye naji dadi. kawai kallon Aisha nake baki bude kamar sokuwa ita kuma idanunta banda aikin hawaye babu abinda suke ta kafawa yatsunta ido kamar ta cikinsu take karanto labarin! cigaba tayi cikin rawar murya:

"Cikin mamaki nake kallonsa tare da tsabar kaduwa da bacin rai! da wani irin fushi nace masa 'Daman Imamu kai ka kawo ni nan? me kake nufi dani? kai ka kawo nan tun daren jiya? me nayi maka?' cikin wannan murmushin nasa na yaudara yace 'calm down Aisha! zauna muyi magana ta fahimta a nutse' da hargagi da masifa na soma ce mishi "wacce irin magana ce ta fahimta tsakanina da kai? meye kake tunanin zaka yaudare ni da shi? angaya maka ni sakarya ce dakikiya irinka da zan saurare ka?" murmushi ya sake yi tare da aje abincin sannan ya mike yace 'Ashe kuwa baki shirya barin dakin nan ba kuwa. don idan har baki bari munyi magana ba toh ko shekara daya zakiyi anan gidan babu inda zaki leka! babu kuma wanda zai gano ki. ga abinci nan kici ki huta zuwa lokacin da kikaga kin shirya saurarata kwankwasa kofa kawai zakiyi mai gadinki zai sanar dani!' yana gama fadin haka ya juya zai futa.
a take na gane cewa masifa da ihu da fada ba shine mafuta a gareni ba, mafuta daya na bar gidan nan kafin a soma nemana. don haka nace masa "ka dawo muyi magana" dariya sosai yayi yace "ban dauka zaki saurin karaya da wuri haka ba, well fara cin abincin sai kifi samun kwarin guiwar jin maganar sosai!" harara na zabga masa nace "ko yunwa zata kasheni ba zanci abincin da ya futo daga hannunka ba! wacce magana ce muyi ta ta kare na bar wannan bakin gidan"
cikin rashin damuwa yace 'well, tunda haka kikace zauna!' a kagauce na zauna bakin gadon kafin ya yi gyaran murya wani katon mutum ya shigo. cewa yayi masa "ka dauko mun laptop da envelope akan dinning a kasa" ya amsa tare da juyawa. ji nayi wani matsanancin tsoron Imamu ya kamani, hankalina ya ninka na dazu tashi na gigice don na tabbatar idan har wannan mutum aka baiwa tsarona to na kade har ganyena banga ta yanda zan iya guduwa ba! ban ankara ba ya dawo da abinda Imam ya umarce shi ya dauko! sannan ya janyo study table ya dora masa akai ya juya ya futa! Envelopes din ya dauko ya miko mun sannan ya shiga sarrafa system din.
A hankali na bude envelope din inda naci karo da mummunan ganin da bazan manta ba! Zara hotona a dakin aka dauka har guda shida tare da wani a gefenan a zaune. hoton was soo real da ni kaina sai da na shiga rudani akansa. juyowa yayi yana murmushi tare da turomun screen din laptop din gabana. Anan naji yan hanjina sun tsinke. Zara vedio ne na dakin nayi bacci, shi wancan mutumin yana ta aikace aikacenshi da waya da computer da takardu nikuma ina kwance ina sharar bacci Zara ko ke kika ga wannan vedio ba zaki yarda dani ba wallahi. "

Innalillahi kawai na dinga maimatawa ina hawaye tare da wani irin firgici da tsoro da fargaba, ban iya samun kalmar da zan bude baki nayi mishi magan ba!
sai da ya gama kallon yanayin da na shiga tsab sannan ya soma magana with serious tone! 'Kada ki daga hankalinki, idan har zaki bi dokar da zan dora miki, kuma zaki kiyaye toh babu mahalukin da zaiga wannan hotunan da vedio har lokacin da zan baki su da hannunki ki kona su ki kuma goge na cikin system din! Nasan zuwa yanzu kin fara tunanin wanne irin mutum ne ni ko? kuma ya za'ai ki hana kawarki aurena? kin soma shirin gaya mata halina da boyayyun siririn da kika sani a kaina! hakan ya sanya na tilastawa kawarki yin dabarar dauko mun ke daga inda kike domin na hada wannan plan din.
warning kawai zan miki da wadannan hotunan da vedio wanda duk wanda na turawa babu makawa babu tantama zai gano bakin halinki da boyayyen bakin sirrinki! kidan yi tunanin yanda zakiji idan na linke envelope din nan na turawa mahaifinki office dinsa. ko kuma nasa yaro yayi sallama ya kai gidanku? ko kuwa a wayi gari hotunan sun bazu a social network? wanne bayani zaki yiwa wadanda suka yarda dake su fahimceki?
kallon horror kawai nake ma Imam a wannan lokacin jikina yana wani irin rawa kamar mazari yayinda yayan cikina suke kuwwa suna kugin tsoro.

Murmushi ya saki kafin yaci gaba da magana cikin sanyin murya da kwanciyar hankali wadda take nuna samun galaba akan wanda zakaiwa maganar 'cool down my dear! Duk wadannan abubuwan sai kinso zasu faru idan kin dauki sharadin da zan gaya miki. sharadin kuwa shine ko da wasa, ko da subutar baki, kika yarda kika sanar da Zahra wani abu mara kyau game dani toh wallahi babu abinda zai hana abubuwan da na gaya miki faruwa! Idan kuwa kika janyo matsalar da Aisha tace ta fasa aurena toh wallahi sai na saka ki cikin bala'in da mutuwa ce kadai zata rabaki da shi! Duk wata hanya da kikasan Zara zata gano illata ki tosheta har zuwa ranar da za'a daura aurenmu da ita! idan kika cika wannan alkawarin toh kingama aikinki. ke da kanki zaki kona wadannan hotunan ki goge vedios dinnan shikenan an wuce wajen! sabawa daya cikin dokata na nufin kin shirya shiga gararin sa zan sanya ki a ciki. Karki damu bana bukatar amsarki a yanzu. kije gida ki nutsu kiyi tunani, kafin ki yanke zabin da zaki yi wa kanki.' yana kaiwa nan ya hada laptop din da hotunan da suka tarwatse a hannuna ya mayar da su cikin envelope din ya futa. kawai jinayi kafafuwana na binsa don burina a lokacin bai wuce na ganni na futa daga wannan bakin gida ba kila ace mafarki nakeyi, idan na futa waje zan farka. motarsa na shiga ya kawoni har gida ba tare da wani yayi magana ba a cikin mu. Muna isowa na balle murfin motar na futa na. shigo gida. Da Umma naci karo a parlour sai dai duk yanda naso aro nutsuwa a jikina na gaza, hankali tashe ta shiga tambayata me ya faru, dakyar nace mata kaina ke ciwo na shigo dakina na kwanta. sai lokacin na tuna duka abubuwan da suka faru na kuma tabbatar ba mafarki bane, a zahiri komai yake faruwa. nayi kuka kamar raina zai futa, kaina yana wani irin dagargazar ciwo kamar zai tarwatse har bansan me yake faruwa dani ba. inaga a lokacin ne Umma ta nemi wayarki ta tambayeki me ya sameni!....Lokacin da kikazo babu yanda banyi da zuciyata na gaya miki komai ba amma tsananin tsoro da firgicin barazanar Imam ta sage mun guiwa. naji bazan iya yi miki maganar ba, sai dai in ba zaki manta ba abinda nace miki shine "nayi alkawari komai wuya komai rintsi bazan sauya daga yanda kika sanni ba" Daga ranar Zara ban sake sukuni ba wallahi, ban sake bacci me dadi ba domin tunanina naci amanar ki

sai wannan lokacin Aisha ta dago jikakkun idanunta da suka rine kamar garwashin wuta. ta kamo hannayena taci gaba da magana!
"Zara nasan cewa ban cancanci a kirani aminiya tagari ba, domin boye miki maganar da nayi har zuwa yanzu da kullum shirin aurenki da Imam yake kusantowa, kullum da wannan tunanin nake kwana nake tashi? ta ya zan zuba idanu na barki ki auri mutum irin Imam? kawai saboda ni na kubutar da kaina daga sharrinsa. ban kyauta ba idan nayi haka, nayi son kai da zalinci, Zara bazan bari ki auri Imam alhalin ina da yanda zanyi na kubutar da ke ba. ko da hakan na nufin faruwar duka abubuwan da ya lissafa zasu faru gareni. i am ready to face them to protect you! Zara fatana kawai idan haka ta faru ki zama wadda zata yarda dani, kada ki juya mun baya please zara! ki zama mutum guda da zata tsaya a gefena a lokacin da zan fuskanci wadannan kalubalen....Duk runtsi duk wuya kada ki barni Zara"
wani matsanancin kuka ta fashe da shi mai bayyanar da zallar tashin hankali da tsoro da fargaba da kuma sadaukarwa!



Helooooooo! it's been soo long🙈
Did you miss me?
ok...we are back again and here is a nice chapter for you!
Another one will be coming nextweek In Sha Allah!

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now