HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE FIFTY-TWO

796 52 7
                                    

Cikin matsanancin mamaki lebbana suka motsa a hankali.
"IMAMU"
Yaushe ya koma hayyacinsa da kuzarinsa da gayunsa da nutsuwarsa bayan haukacewar da yayi akan warwarewar maganar auren mu. Ni tunda nayi blocking shi na kuma daina daga bakuwar number sai na samu nutsuwa. A hankali ya dauke kafa daga zuwa kofar gidanmu da bibiyar al'amurana har ma na manta gabadaya da labarinsa sai da mikin da ya barmun  wanda ba ba zai gogu lokaci daya ba.
Toh duk ma ba wannan ba! Me ya kawo shi gidanmu? Da wacce yazo? Me zan masa?

Cikin sauri na daure fuskata tamau kamar bansan garin da ake dariya ba. Na sake gyara tsayuwata cikin jarumta da rashin barin ko ta kwana.
A hankali ya karaso dai dai inda nake tsaye sannan yace "Good day beautiful!"
Na dago na kalle shi a banzace. Ya rame sosai amma ya kara fari sannan babu wannan mayaudarin murmushin akan fuskarsa. Hakan ya sanya masa wani kwarjini na musamman!
Cikin muguwar daurewar fuska nace "Me ya kawo ka gidanmu?"
Guntun murmushi yayi yace "hmmm Zara wannan ne sannu da zuwan da zaki mun?" Wata muguwar harara na zuba masa sannan nace "kai kana mafarkin zaka samu sannu daga wajena a cikin wannan duniyar? Wanda ake maraba da shi ake wa sannu da zuwa ba wanda ba'a bukatar gani ba! Bana son dogon zance don haka ka fadi abinda ya kawo ka ka juya ka futa don babu wani abu a gidan nan da yake maraba da kai balle ya karbi bakuncinka "
Sosai ranshi ya baci matuka da kalamaina har sai da launin idanunsa suka sauya. Ya koma wani serious babban mutum. Tabe baki nayi na juya masa keya ina sauraren abinda zai fada.
Cikin karyewar sauti da tsananin sanyin jiki ya soma magana.
"Zara ba anan naso muyi wannan maganar ba saboda muhimmancin ta but I have no option tunda kin daina yi mun kallon mutum na koma miki kamar wani dabba abun kyama.
Zara nasan bani da hali kuma bani da dabi'a bani da kirki kuma na aikata manya manyan laifuka da kura-kurai masu yawa a rayuwata. Na zalunci mata dayawa ba yaudare su, na bata musu suna, nayi abinda nake so a rayuwa ba tare da tunanin cewa dama Allah ya ara mun ba, ba tare da tunanin akwai makomar abubuwan da nake aikatawa ba. Ni kaina idan ina tuna wasu abubuwan nakan kwana ban runtsa ba saboda tsananin tashin hankali da tunanin illar da abubuwan da nayi zasu haifar mun a gaba. But trust me Zara! Billahil azeem daga lokacin da kika shigo rayuwata nagane so na hakika na bambamce son gaskiya da na yaudara. A lokacin na soma tunanin nima zanyi aure nayi building rayuwata na aje rayuwar da nake yi duk da nasan ba abu ne mai sauki ba.
Zara Allah ya jarabce ni da sonki jarabta mafi azabtuwa da radadi. Ban taba sanin menene tashin hankali ko bakin ciki ba a rayuwa sai ranar da aka janye maganar aurena da ke. Daga lokacin na tabbatar hakkin mutanen da na zalinta ne zai tambayeni domin na san cewa rashinki a rayuwata wata muguwar masifa ce da zata tarwatsa ni da duk abinda na gina a rayuwata. Daga ranar na koma ga Allah, na tuba, nayi nadama mai tsananin gaske tare da daukar aniyar cewa akan ki sai inda karfina ya kare. Sai dai hakan bai samu ba, domin laifuka na gare ki masu tsananin girma ne wadanda ba kowanne mahaluki za'aiwa ya yafe ba. Ganin ba zan taba samunki ba ya sanya na saduda na koma ga Allah na tafi Saudiyya tsayin watanni biyu ina bautar Allah tare da jinyar zuciyata har Allah ya bani hakuri da dangana da nutsuwa. Sau biyu ina haduwa dake a Haram a wannan zuwan da kuka yi amma bani da kwarin guiwar da zan iya fuskantar ki a wannan waje ko dan gudun kar na tuna miki abinda nayi miki ki kai kara ta a wannan wuri mai tsarki da daraja kila ma addu'ar da nazo yi a dawo mun da ita."

Dakatawa yayi da maganar yana lashe lebbansa da suka bushe tare da gyara tsayuwa. Nikam jikina ne ya soma sanyi duk yanda na dau zafin ganinshi da haushin sa da nake ji sai da naji nayi rauni. A hankali yaci gaba da cewa "a yau Zara nazo wajen ki ne ba don na dame ki ba, ko na bata miki rai akan neman alfarmar soyayyarki! Nazo ne nayi miki godiya Zara godiyar da babu mahalukin da ya cancanci irinta bayan ke a rayuwata."

Cikin mamaki na juyo gabadaya ina kallon shi. Kallon rashin fahimta da tuhuma. Hade hannuwanshi yayi waje guda yace  "yes Zara! I want to thank you! Saboda Kece silar shiriyata! You have changed my life! Kin sauyani daga batacce zuwa mutum nagari. Kin ceto ni daga halaka kafin lokaci ya kure mun kuma kin dawo dani hayyacina kin koyar dani darasi kafin duniya ta koya min. Gayamun ta ya zan iya gode wannan alkhairin naki a gareni? Wallahi ko da ban aure ki ba shigowar ki rayuwata shine alkhairi mafi girma da na ci karo da shi. Don haka nazo wajenki domin na tabbatar miki da cewa a duk lokacin da kike tunanin aikin da kikai na lada a duniya, abinda zaki fara lissafawa shine kin samu nasarar shiryar da babban lalatacce irina zuwa hanya mai kyau. Na tabbatar Allah will reward you for this. Ba zan iya nemar alfarmar yafiyarki a yanzu ba, sai dai kiyi mun lamuni ki yafe mun kafin Allah ya dau numfashina. Don ina tsoron Allah ya kamani da hakkin ki Zara.

HAUSA ARAB PART 1Onde histórias criam vida. Descubra agora