HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE FOUR

1.1K 78 2
                                    

Bayan na kammala shiryawa ne na tsaya a gaban full size mirror ina kallon kaina. A kowanne lokaci idan na kalli kaina a mudubi nakan godewa Ubangijin da Ya kawata mun surata. Zaka iya kirana fara idan babu fararen mutane a waje amma kuma acikinsu ni ba farar bace wata irin kala ce kamar an cakuda furanto da madara. "Chocolate colour" kenan inji bature. I am moderate in height da wata irin body
madara. Chocolate colour kenan inji bature. Kalar Irin ta asalin ethopians amma wannan ta sake samun armashi da samun ingantacciyar kulawa da sanin abinda ya dace da ita.
I am moderate in height da wani irin body structure mai tsada. Bani da jiki ko rama saidai shape mai tsari. A fuska kuwa me kyau ce domin ban taba jin wanda ya kushe fuskata ba musamman dara daran idanuna masu haske da dogon gashin da yai musu rumfa ga kananun lips dina masu taushi da sulbi. I am cute! Very cute!! Lolz!
Atamfa ce yar holland a jikina koriya shar mai zanen ganye an dan ratsa mata orange. Dinkin simple and elegant straight gown sai akabi duka pattern din da swarosvki stones sai walwali take. Nayi dauri mai sauki fuskata babu komai sai powder da chapet. yanayin kalar fatata bata bukatar sai nayi kwalliya zanyi kyau. Da siraran saitin diamond nayi amfani a kunne da wuya da hannayena. Sannan na yafa gyale Orange na "kashka" na feshe kwalliyar da turaren body shop mai suna "smokey rose" na zura flat shoe orange samfurin "chloe" na futo parlour.
"Kai! kai!! kai!!! cancadi! Wannan wacce irin atamfa ce?" Cewar Dada tana kallona. Murmushi nayi na karaso na zauna sannan nace "kai Dada irin taki ce fa wadda kika saka ranar da zamu taho daga Abuja" cikin mamaki tace "kai yar nan! Qarya ne Ba irin wannan bace wannan tafi kyau" dariya ta bani nace "Dada wallahi irinta ce sak kala ce kawai ba daya ba. taki ruwan kasa da ratsin pink" cewa tayi "amma wannan tafi kyau ai da na ganta ita zan dauka kamar ba iri daya da tawa ba" dariya na sake yi nace "ke dai Dada kawai kice kwalliyata tai miki kyau ba wata atamfa kyawun ai daga jikina ne" dariya tayi irin ta manya sannan tace "kayya! ina wani kyau anan mutum kamar a kife shi da kwando? A layin kyawawa ai babu gajere?! Nan da nan na cika nayi fam kamar zan fashe domin na tsani ace mun gajeriya koda bani da tsayi mai yawa amma ai babu yanda za'a kirani gajeriya. Ya Nuratu dai tana gefe tana yi mana dariya ni da Dada. Karar kararrawa ne ya tashe ni na tafi da sauri na bude kofar. Daddy ne a gaba sai manyan aminansa irinsu Ambasada Ahmad Kibiya da Dr Ilyas da engineer Nuhu salihi tsohon kakakin majalisa Alaji Ibrahim kurmi mai atamfa da Dr Haruna Madugu tsohon gwamnan Taraba. Dukansu aminai ne na gaske makaranta daya sukayi amma duk duniya Daddy bashi da kamar ambasada aminai ne na gani kasheni sannan Dr Mansur mijin Ya Nuratu kanin ambasada ne uwa daya uba daya. Shi da Daddy suka kulla auren a lokacin Ya Nuratu ta kammala secondary school Dada tayi tsallen albarka tace sam ba zata ci gaba ba sai dai a dakinta. Dada ta tsani ilmin boko kuma tayi masa mummunan fahimta don hakane bata goyon bayan mace tayi karatu mai zurfi ko mazan ma sai da akayi dagaske ta hakura ta kyale su. Biyayya ce kawai tasa Ya Nuratu ta auri Dr.Mansur amma a hankali ta gano qualities dinshi da kyawawan dabi'unshi da uwa uba kyautatawa da kulawarshi a gareta wanda suka sanya mata soyayyar mai karfi. Haihuwar ta daya ta samu ya mace aka sanya mata sunan Dada wato Fatima suke ce mata Amal! Shekarunta shida suna zaune cikin kwanciyar hankali da kaunar juna. Duk lokacin da mukazo Ya Nuratu tattarowa take ta dawo wajenmu sai zamu koma take tafiya.

Cikin ladabi muka gayar dasu sannan muka shimfida katuwar ledar cin abinci muka soma hada musu kayan da muka tanadar musu. Nan da nan muka cika gabansu da kayan abinci iri iri. Dukansu nishadi suke da murna mai yawa domin sun dade rabon da su hadu gabadayansu lokaci daya. Na dauko katon flask din bakin shayi ne naji karar kararrawa don haka na ajiye shi a gaba Daddy na mike da sauri na nufi kofar.
Gabana yayi mugun faduwa da ganin Ya Mahmud! Inaga bayan tsanarsa da nayi har tsoronsa nakeji. Da sauri nayi baya har da sassarfa na koma kitchen.
Ya Mahmud ne akan gaba cikin shigar manyan kaya ta fara sol din getzner an kawata ta da dinkin hannu da zare coffee. Ya dora hula coffee akan gyararriyar sumarsa wadda ta kwanta lambau har keyarsa. Hannunsa ma lafiyayyen agogon fata ne samfurin "Calvin Klein" shima coffee. Ya sinkife kafarsa da covered shoe dan gidan Luis Vuitton(LV) shima coffee. "He is the most classy guy ive ever seen in my life!" Biye da shi matasa ne guda shida masu shekarunsa da wadanda suka zarta shi kadan kowanne cikin shiga ta alfarma kana ganinsu kasan sunci sun tada kai a boko, da kudi, exposure!
Gaban su Daddy suka zube suna diban gaisuwa kafin su hau dinning kamar yanda Ya Nuratu tayi insisting.
Suma kamar yanda muka hadawa su Daddy abincin haka muka yi musu. Na dauko plates nazo na ajiye sannan nayi musu gaisuwa guda daya ba tare da na dube su ba. "Designer Guy wannan sister dinka ce?" Maimaita sunan nayi a raina "lallai kam yaci designer guy din domin ko handkerchief ka gani a hannunsa akwai brand din shi" kafin ya bashi amsa na shige kitchen don haka banji abinda yace masa ba.
Bayan sun kammala cin abincin Dada ta futo sukayi sallama da aminan Daddy. Nan fa suka cikamu da kudi ni da Ya Nuratu da Amal.
Na kulle kofar na dawo ne na hango su Ya Mahmud suma sun taso zasu tafi. Rabewa nayi ta gefensa na wuce. Ji nayi an kira sunana na juya da sauri a dalilin gane muryar me kiran da nayi. A hankali na isa gabansu. Wani kyakykywan saurayi ne fari sol a gefensa ya watso mun murmushi sannan ya sanya hannu cikin aljihu ya futo da sankararrun dollars ya miko mun yana cewa "sister ga barka da sallah" wani irin kallo nayi masa sannan nace "ka barshi nagode" na juya da sauri na wuce yana ta kwallamun kira naki tsayawa na shige daki. "Mtsew ina ruwana da abokanka da wani kudinku? Me kuma zai sake hadani da kai? Aikin banza" abinda nake a zuciya kenan na kulle kofar dakin na shige toilet don kar a dameni.

Washe garin sallah muka koma Jeddah. ranar litinin muka je asibiti da Dada likita ya sake dubata tare da sallamarta sai bayan watanni shida. Ban sake ganin Ya Mahmud ba ashe tun ranar sallah ya tafi. Ran talata da yamma tuni muna cikin jirgi bayan munyi sallama da Ya Nuratu tana ta kuka abun dariya. Nima na tabbatar zanyi missing su ita da Amal. Amma ya muka iya? Kowa da yanda Allah ya aje shi.
We are finally Home!! An dawo daga wannan tafiya saura wata kuma in ta taso. Don kadan daga cikin aikin Daddy bayan sati hudu yace muje Dubai ko Cairo Dada ta huta. Kwanan mu biyu da dawowa Mami tazo tayiwa Dada sannu da zuwa murna kamar ta kasheni. Na kwaso mata duka tsarabar da na jibgo mata Dada tana yimun dariya.

Lokacin da muka dawo ana cikin hutu sai bayan sati daya muka koma school. Duk inda nake tunanin abubuwan da nayi missing sun wuce haka don haka karatu na dukufa yi bani da time din kaina domin muna gab da zana finals dinmu.

Ran saturday da la'asar na idar na sallah kenan Dada ta shigo dakina tana cewa "Zara yi maza ki karasa ki shirya kizo zan aike ki" gyaran murya nayi mata a sakamakon azkar din da nake yi. Ina kammawala na shiga toilet na ware warm shower nayi wankan cikin sauri na futo. Sannan na shirya cikin embellished super mint green mai ratsin baby pink. Dinkin skirt and blouse babu komai na kwalliya sai fitting da yayi kamar a jikina aka kera kayan. Na sauya barimar kunnena daga gold zuwa silver hakana bracelet din hannuna da anklet. Fuskata babu komai ruwan hodar merrycay da pink jambakin "mac" wanda ya mayar da kwalliyar tawa abun sha'awa. Ina cikin daura sandal dina samfurin "Chanel" naji kiran Dada don haka nayi maza na yafa gyalena dan siriri pink na ciro babbar jakar "ALDo" domin ina tunanin kila aiken na kudi ne. Da daya daga cikin turaren "Ralph Lauren" da ke kan mudubina na feshe kwalliyar tawa sannan na futo ina daure hannuna da agogo silver dan gidan "Armani". I sometimes call myself designer baby! Kamar yanda naji ana kiran Ya Mahmud domun Daddy da Mami na matukar kulawa da bangaren gayuna komai tsadar jaka ko takalmi Daddy zai siyo ya kawo mun bai taba yin tafiya bai mun tsaraba ba. And you know? Mutum like Daddy bai shiga karamin kanti. Ga Mami daga gefe duka abinda tagani na sha'awa ni take tunowa komai siyemun take komai tsadarshi musamman da ta gane ina matukar son classy abubuwa don hakane na hada wani karamun designer room.
Kamar yanda nayi tunanin hakane! Kudi Dada tabani rafar yan dubu dubu guda biyar guda goma 500k kenan. Ta miko mun envelop na saka aciki na like.
"Gidan Hajiya Maryam zakije ki kai mata kice gashinan injini ba yawa a siye wa Amarya tsintsiya" dariya nayi sosai nace "Dada manya 500k dince na siyan tsintsiya?" Itama dariyar tayi tace "ke kamar ba bahaushiya ba haka ake cewa idan za'a kai gudunmuwar buki komai yawan kudi sai ace a siya tsintsiya" dariya na sake yi ina sarawa Malam Bahaushe da tunaninsa masu wuyar fahimta. Bayan nayi mata sallama na futo. Idona ne ya kai kan sabuwar Range rover red colour tasha wanki sai kyalli take. Tuni yawuna ya tsinke! Cikin sanda na dawo parlour na duba kan side table na dau mukullin motar Ya Omar wadda yake ji a ita kamar ransa a zuciyata ina cewa "nima yau sai na dana wallahi sai dai komai zai faru ya faru"
Ina shiga wani kamshi ya doki hancina. Ya Omar is crazy har turaren wuta yake yi acikin motarsa don tayi kamshi unique! Kunna motar nayi na ware AC sannan na duba cds dinshi na zabo na mutuminshi "chris brown" ma saka nan da nan wakar "with you" ta soma tashi na baiwa motar wuta malam Lawan ya bankade mun gate na futa a guje ina dariyar mugunta ni kadai tare da tunanin yanda zamu kare da mai motar.
Gidan Hajiya Maryam da ke Maitama na dau hanya. Ina isa na tarar da ita cikin mota zata futa don haka na bata sakon anan babu yanda bata yi dani ba nazo mu shiga ciki nace mata babu komai nima sauri nake. Ta debo kudi ta bani nayi mata godiya mukai sallama ta futa nima na koma motata na futo! In gaskiya ne na dawo gida mana? Amma saboda dokin motar aro sai na dau waya na kira Aisha. "Hello bestie " cewa nayi "kina ina Aisha gani hanyar gidanku? Da sauri tace "No bana gida ina Maitama park da yaran A.saudah sunzo gidanmu" cewa nayi mata gani nan zuwa don ji nake idan banyi yawo da motar nan ba na bar banza.
Lokacin da na isa dakyar na samu wajen parking a dalilin weekend ne. Ina cikin tafiya naji alamun mutum a bayana sai na juyo.
Wani kyakykywan saurayi nayi tozali da shi fari ne sol har farin yaso ya mishi a yawa a sakamakon hutu da jindadi da ilmi da danshin naira da sukai mata rubdugu. Kyakykywan karshe ne domin ba don shigar da take jikinsa ta farin voil ba cewa zanyi ba'indiye ne. Hannunsa dama da hagu rike da yaro mai kama da shi sak. A take na gano yaran twins ne an musu kwalliya mai kyau kamar ka sure su ka gudu "Hello beautiful" ya fada a lokacin da na juyar da kaina daga garesu. Kirjina na bada wani sautuka "dum!dum!! Sai bugawa yake! Yayinda Kafata ta soma rawa kamar ba zata daukeni ba.!Kunsan "love at first sight?" Shine abinda ya faru dani a yau.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now