kwalalo idon da nayi ne ya baiwa Ya Mahmud dariya ya girgiza kai kawai ya ciro katinsa aka zare kudaden daga ciki! sannan nayi wata ajiyar zuciya ta relief! mun dade muna yawo da siye siye kafin Mami ta taso mu a gaba da waya lallai mu dawo saboda Ya Mahmud bai gama warwarewa ba!
Nan muka shigo mota muka taho a gajiye! muna isa Safna tai mana sallama ta wuce gidansu cikin murnar siyayyar da Ya Mahmud yayi mata kamar yar karamar yarinya! mu kuma driver ya tayamu kwasar namu kayan zuwa kofar gida! Na daga hannuna zan danna kararrawa kenan Ya Mahmud yayi gyaran murya tare da kiran sunana!
juyowa nayi ina kallonshi sai naci karo da wata serious face mai kwarjini har naji na kasa jure kallonshi! cikin nutsuwa yake cewa "Zara kiyi hakuri kiyi zamanki kar kice zaki bi Daddy kinji? Mami ba zataso ki tafi ba! ke kike ganin kamar bata damu da ke ba amma can kasan ranta komai naki a lissafe take dashi! Mami tana da kawaici sosai kuma ba saboda nine take miki haka ba saboda Dada ne! tana ganin idan ta cika shiga lamarinki tana kulawa da ke Dada zatace tayi rashin kunya kingane? but your Mami loves you soo much! more than anyone can ever explain to you Zara! nida kike kishi is your blood brother Zara! Mami bata fi sona ba akanki! tana kulawa dani ne saboda halin da nake ciki kingane?"
jikina ne yayi mugun sanyi domin kalamansa sunyi bala'in tasiri a zuciya da gangar jikina! sosai tausayinshi ya kamani da kuma kunyar abinda nayi idan nayi la'akari da cewa Mamin fa tawa ce,mahaifiyata mai tsayuwa akan duk lamurana! shi kuwa fa? a rashin soyayyar uwar ya sanya Mami rungumarshi ta bashi kulawar da yake bukata! shin banyi son kai ba kuwa? har na iya kallon idon Daddy na gaya mishi haka? sai naji kunya da rashin kyautatuwar abinda nayi ta kamani! kaina a kasa nace "kayi hakuri Ya Mahmud! i was so selfish! banyi tunani mai nisa ba na yanke hukunci! kayi hakuri!"
murmushi yayi tare da dafa kafadata! "na fahimceki! i just want you to put something at the back of your mind cewa Nidin ba stranger bane a wajenki Yayanki ne blood brother dinki who is ready to protect you and make you the happiest sister in the world, who will always give you support and a shoulder to cry on! so ignore kowanne feeling dake tare dake a kaina ki mayar da kanki aminiyata kinji?"
ya karashe maganan yana daga gira! nayi murmushi! hannunshi ya cire daga kafadata ya miko mun yana murmushi "friends?" ya fada! na mika mishi nawa hannun mukai musabaha nace "friends" duka mukai dariya kafin na danna kararrawa mu shiga cikin gidan!
Daddy ya dawo yana zaune yana cin Tuwon da akaiwa Ya Mahmud! muka dinga shigo da kaya! duka kallonmu suke har muka kammala jera kayan muka dawo muka zauna muna amsa Sannu da gajiyar Dada! Daddy ne yace "toh Zara yi maza kiyi parking wadannan kayan in less than 2hours nake so muna cikim jirgi!"
Kallon Ya Mahmud nayi shima ya kalleni tare da mun magana da ido!
sai na gyara zama nace "ahhmm! Daddy ai tafiyar nan......" na sake kallon Ya Mahmud muka kyalkyale da dariya! da mamaki duka suke kallonmu! Daddy yace "ah ah!! tafiyar nan me? wanne sabon al'amari ne kuma wannan?" Dada ta shanye ragowar kunun ta ta dubi Daddy tace "nima dai abinda nake son ganewa kenan! wacce gulmar ce kuma ta tashi tsakaninsu?" cikin dariya nace "Dada gulma kuma?" tace "toh meye in ba gulma ba? kun tashi zaku tafi ya biku yanzu kuma kun dawo kuna magana da ido kuna dariya bayan rikicin tafiyar da bada kudin siyayyar duka akan Mahmud din kikayi!"
tabe baki nayi nace "toh Dada daman dai so kike kiga muna fada ko? toh kwantar da hankalinki mun shirya kuma na fasa tafiya" Dariya suka sa gabadaya! cikin jindadi Daddy yace "wato hakane Zara? toh ni bari nayi ta kaina kan gulmar ta dawo wajena!" duka mukai dariya! daga nan Daddy yayi mana sallama muka rakashi har bakin mota muka dawo!
wannan shine tushen shirina da Ya Mahmud! ya kasance daga wannan rana muna zama muyi hira muyi wasa da dariya! mu fita tare muje cinema muje park! acikin satin Ya Sadik da Ya Omar suka sauka a London tare da matansu Ya sofiya da Ya Anis!! Nan gidan fa ya kacame da farin ciki da annashuwa da nishadi! tuni na manta damuwar da ke damuna na shiga cikin yan'uwana muna shagali! sati daya muka kara a London muka wuce Dubai gabadaya!
ko kwana bamuyi ba Ya Nuratu ta iso itama! wai Allah! i was soooo happy! mun dade rabonda muyi tafiya mai dadin wannan! duk wanda ka duba cikinmu nishadi yakeyi! bamu aiki da sai zaman hira da wasa da dariya idan rana tayi sanyi kowanne ya shirya mu shiga mota mu futa! watarana gabadayanmu wataran kuma kowa ya hade kai da wanda yake ganin ra'ayinsu yazo daya suyi tafiyarsu!
YOU ARE READING
HAUSA ARAB PART 1
General FictionAlqalamin qaddara yana aiki akan kowa ba tare da zabin wance ko wane ba. Kowanne bawa da irin na shi salon rubutun, na wani ba irin na wani bane.