HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE SIXTEEN

804 74 3
                                    

Safiyar Asabar ta kasance mai tsanani sosai gareni a sakamakon tunanin da sukai wa kwakwalwata rubdugun da yake shirin fasata. duk yanda nayi tunanin na kare Aisha ko Imamu daga mugun zargin da nakeyi na gaza domin manyan dalilan da ya kewaye kowanne hasashe nawa a garesu.
jiya akai dinner gidansu Ihsan amma sam Imam baizo ba. na fahimci kwana biyu ko son haduwa dani bayayi idan kuma har mun hadu waje daya bashi da aiki illa ya tsura mun idanu yana kallona yana faman tunani. idan na tambayeshi dalili yace babu komai. ita kanta Aisha na rasa gane kanta domin rabin walwalar da nishadin dana santa dashi sun tafi. kawai yake takeyi amma sanin da nayi mata na tabbatar akwai dankareriyar damuwa a kwance acikin zuciyarta. Da ada ne bazan samu nutsuwa ba idan ba zaunar da ita nayi ba naji matsalarta. ko yanzun ma ina tunanin nasan mecece matsalar ne shiyasa na kyaleta amma duk da haka ba karamun rashin jindadin ganinta a haka nake ba. wannan wacce irin kaddara ce haka take shirin fado mana? nida Aisha muna neman komawa juna complete strangers!! duk sanda muke tare kowa kokarin aro expression din kan fuskarshi yake duk da dukanmu munsan kanmu ba sanin shanu ba kuma kowa yasan akwai abinda yake kokarin boyewa dan'uwansa sai dai tsoron sanin hakan ya hana dukanmu tuhumar junanmu! This is fucking painfull wallah!! i hate this situation! idan akwai wanda nake enjoying bankadawa asirin zuciyata bai wuce Aisha ba domin duk duniya babu wanda yake fahimta ta kamarta! kafin nayi magana take karanta abinda yake kan fuskata harda na cikin zuciyata ta kuma bani shawarar yanda zan warware koma wacce matsala ce take damuna! Aisha bata taba bari na zauna da damuwa ba. sau da yawa takan salwantar da nata farincikin domin nawa. ita kadai nake zama nayi kuka a gabanta banji awkwardness ba kasancewata mutum wadda bata kaunar aga lagonta. Idan akwai abinda na tsana a duniya bai wuce a ganni ina kuka ba. don haka kafin wani yaga kukana ana daukar lokaci  sai dai nayi shi a daki ko toilet na wanke fuskata nasa kwalli na futo kamar banyi ba. babu wanda yasan weakness dina irin Aisha babu wanda yasan iya level din patience dina irinta! ku gayamun tayaya zan iya jure rashin wannan mutum mai matukar muhimmanci a rayuwata? tayaya zanyi manejin raba hanya da Aisha? wannan shine abu mafi tada hankali a gareni. na yarda na rasa Imamu duk da son da nake masa duk da halin da nake tunanin zan fada idan babu shi saboda nasan akwai Aisha a gefena wadda zata tsayamun tsayin daka wajen korar bakinciki da sabon da nayi da Imamu daga raina! bana ko tantama babu wani abu da zai shigomun Aisha bata tayani tsayuwa na kare kaina ba. How on earth am i going to manage living this life without my other half?? it's soo difficult accepting this change!! wallahil azeem am not enjoying what i'm going through with my best friend!! hakan ya kara mun babbar damuwa daga cikin damuwoyin dake damuna har yayi affecting dabi'una da aka sanni dasu! na manta rabon da nayi nishadi da walwala kamar sauran mutane! na manta rabon da na kwanta a gadona nayi bacci peacefully na manta rabon da na tashi daga bacci da karfina da kwazo da kwanciyar hankali. zuwa yanzu wallahi na fara regretting sanin Imamu a rayuwata domin sanin nashi bai amfaneni da komai ba sai tarin matsaloli da ya sakani ciki! ga buki da ya shigo ya takurawa kadaicina. dole na daure na boye abinda yake damuna na mayar komai ba komai ba na shiga cikin jama'a  ayi budiri da shagulguna dani. idan akwai abinda yafi cinye damuwar dake ranka cikin duniya toh basu dayawa! it is one of the most difficult situation wallah!
                Tun safe naje Office din Mami na karbi kayana da aka rage mun a dalilin ramar da nayi bayan dinka kayan aka sake gogewa sannan na taho gidansu Ihsan! zuwa karfe shida tuni an soma haramar kimtsawa da yin kwalliya domin karfe 8 suka saka a jikin katin bukin kuma ba'a bukatar African time a dalilin manya manyan mutanen da aka gayyata.
zaku so ganina cikin kwalliyata ta yau domin tafi ta kowacce rana a bukin kyau da kuma tsada. wani rantsatstsen luxury lace ne mai nauyi. kalarshi jajawur yayinda roses din da aka shirya pattern din jikinsa da shi suka zama zallar gold! ba'a baiwa leshin wuya wurin dinki ba domin buba and iro ne sai gaban rigar da aka kawata da pattern din lace din aka dora embroidery akai. cif kayan sukai fitting figure dina kamar a jikina aka zana. Mamza ta kawata kwalliyar tawa da make up na ban sha'awa musamman da ya kasance ban cika sa kaya mai kala mai nauyi ba (I am afraid of colours) nafi ganewa brown, peach da kaloli marasa hayaniya! hakana lipstcik kullum nude nafi amfani dashi sabanin yau da ta sakamun Red mai sheki kamar a ciro lips dina don kyau.
ashoke na gold colour ne. zanso ku kalli tafkekiyar sarkar wuyana samfurin Bahrain. hannuna na dama cika nayi da wara warai sirara guda goma yan Dubai. na hagu kuma agogon Rolex da sarkarsa! takalmin kafata ma chanel ja ne mai igiyoyi da tsinin dunduniya.
banajin na taba kyau irin wanda nayi yau cikin traditional attire!
Amarya kuwa tun daga sama har kasa daga kan rigar ta zuwa accessories duka gold ne wanda ya hadu da farar fatarta ya fiddo da wata Arabian queen da ba zaka kaso ka cire idonka akanta ba! Duka bridemaids ashobin red organza lace sukai da gold head.
A bluevelvetmarque. lokacin da muka isa karfe takwas da minti uku tuni marque din ya cika da jama'ar da aka gayyato sai tashin sautin kida mai sanyi daga bakin zabiya Celine Dion ne ke amo a hankali da tausasa zuciya.
abokan ango duka farar shedda suka saka da gold din hula. tare mukayi layi mikakke muka shiga hall din cikin class muna dan takawa a hankali. daga nan couple din suka iso suna haska wajen kamar taurari don kyau da dacewa da juna. Mc na da kwarzanta kyawu da tsarin halittarsu da kwalliyarsu har suka isa wajen da aka tanada domin su suka zauna.
BigH yace dawa aka hadashi ba da mu ba? kewaye su mukai akai ta daukar hotuna kafin kowa ya sauka mu koma barin da aka ware mana a matsayin manyan abokan ango da kwayen amarya!
sannan aka ci gaba da gabatar da taro inda aka bukaci limamin masallacin juma'a da yazo ya bude taro da addu'a. bayanshi Uncle din ango Hashim Dala ya futo yayi jawabin lale maraba daga nan akaci gaba da gabatar da taro yanda ya kamata.
Gefe guda masu rabon abinci na aikin su.
Na kai semosa bakina zan gutsira naji muryar MC ta karade wajen yana neman babbar aminiyar amarya tazo ta bada tarihin amarya cikin mintina biyar.

Cousin din Ihsan ce Amna ta futa tayi bayani akan rayuwar Ihsan cikin harshen nasara me cike da iyayi da lankwasa kamar wata yartsana. ta kammala aka bita da tafi Mc ma shakiyanci yana sa mutane dariya. Sannan aka bukaci babban abokin ango. ya maimaita hakan yakai sau hudu kafin wanda ake nema ya mike.
Mutumin da ya taso don amsa wannan kira wani dogon matashi ne mai wata irin structure ta mazan da suka amsa sunansu. Fari zaka kirashi amma ba sol ba. Hancinsa ne zai matukar baka mamaki yanda ya taho ya dire kaman an dora saboda tsini. Hakana idanunsa farare sol an diga wasu ilhamomi aciki na kwarjini da kamala .wani irin gashi mai kauri gazar gazar baqi qirin yayi musu Rumfa hakanan idanun suke lumshewa su bude da kansu kamar masu jin bacci. "Ive never seen a beautiful creature like this man"
Sanye yake cikin wani irin yadin da nidai mutane kalilan na taba gani da shi domin tsadarsa da kyawunsa. Kalarsa purple me duhu sosai an cika gabar babbar rigar da wani irin aikin zare mai tsari da kayatarwa. Kai kana ganinsa dole ka bashi hanya domin ya daku ya sake dakuwa a kamala da kyau da tsari.
A lokacin da yake matsowa kusa ne gabana ya soma bada wani sauti dam! Dam! Me idona yake shirin gani ne? Ya ilahil arshi!! Ya rabbis samawati! Wannan ai arrogant jikan Dadan nan ne da suke kira Mahmud. A daidai lokacin kuwa naji MC din ya soma mishi kirari da "likita bokan turai likitan duniya likitan gayu likitan kwalisa wanda samarin zamani ke wa lakabi da Designer guy" gabadaya sai lokacin na tuno komai. To ai Faisal na daya daga cikin samarin da suka zo hotel dinmu a saudi ranar sallah. What a foolishness?? Meyasa bangane shi ba sai yau??tabdi.
Nidai ina can duniyar tunani naji an tabo ni...na juyo ina duban Aisha a kunnena ta radamun "Zara jiyemun wani accent don girman Allah" a lokacin ne na maida hankalina ga abinda yake gudana na kasa kunnena ina sauraren wannan murya da ta dasa mun tsanar mamallakinta da tsoro da fargabar jinta a kowanne lokaci. Murya mai sanyin amo da wani irin tone mai mintsinin zuciya da karkato da hankalin mai sauraro. Accent dinshi kadai zai iya ribatar zuciyar ka ka tsunduma kaunar bawan Allahn kafin ka gano mugunta da zalincinsa. No matter how much i hate him and the pain he has caused me i cant deny the fact that ban taba ganin mutum me kyawu da baiwa irin tashi ba. Allah ya yi masa baiwa saidai  ya butulcewa baiwar yana amfani da ita wajen zalinci da kaskantar da dan'adam yana mantawa cewa wannan kyakykywar sura da ya mallaka wataran a rami za'a haka a rufeta ta rube tsutsoci su cinye. Halin shi nagari da kyakykywar mu'amalar shi da mutane ita zata ceceshi a wannan lokaci. A jinsin mutane kakaf ni ban taba ganin mutum mai kasaita da jin kansa irin wannan gayen ba. Tantirin dan wulakancin karshe ne.
Nidai bansan lokacin da ya qari ragargazar hardadden turancin na shi ya koma ya zauna ba. Illa tafin da wurin ya dauka raf! Raf!! Raf!!! Ya dawo dani hayyacina. Na tabe baki ina cewa "rashin sanin waye wannan mutumin yasa yake birgeku".
Bayan an kammala wannan amarya da ango suka sauko stage domin taka rawa. nan da nan hankalin masu hoto da vedio da wayoyin al'ummar da ke wajen ya koma kansu. daganan mu ma muka shiga filin aka soma cashewa damu musamman da aka bayyana isowar shahararren Artist Davido sai filin ya rude da rawa da liki.
Nikuwa sulalewa nayi bayan na gama nawa likin na nemi hanyar futa ina amsa wayar Imamu. ina futowa na hango shi a parking space cikin kawatacciyar kwalliyarsa ta bakar sheddar da ta haska farar fatarshi. saidai ya dan rame sannan ya rage wannan murmushin da baka rabashi dashi mai futo da asalin kyawunsa.
"ya baka shigo ba? shine sai yanzu kazo ko?" abinda na soma gaya mishi kenan shikuma yana yunkurin daukana hoto da wayarshi!
Nasa hannu na kare fuskata ina cewa
"babu hoton da zakaimun sai mun shiga ciki" sai ya mayar da watar aljihu yana murmushi "toh muje your highness" ban tanka mishi ba na wuce gaba yana biye dani har can cikin wajen bukin gaban su Ihsan suka gaisa mukayi hoto sannan ya shiga yi mana liki harda Aisha. na fahimci duka mu ukun mun daure yau munyi abinda ya dace. sai wajen karfe daya saura kwata taro ya tashi. nida Imamu muka futo ina masa rakiya na hango Mami tsaye ita da Mahmud suna magana. Imamu ne yace "muje nayiwa Mami sallama sai na wuce" ba'a raina don banason haduwa da Ya Mahmud ko kadan! amma ba yanda zanyi nace masa "toh" muka tafi.
sai da muka karasa duka suka juyo suna dubanmu. har kasa Imam ya rissina ya rissina yana yiwa Mami sai da safe kafin ya dago su hada idanu da Ya Mahmud.  dukansu wani shock ne ya ziyarcesu na wasu dakiku kafin Imamu yai maza ya kawar da abinda yake ka fuskarshi ya mika masa hannu! amma saboda rashin M na Mahmud sai ya makale nashi hannun ya zura su a aljihu suka gaisa a haka. da sauri Imamu ya wuce nabi bayanshi cikin jin haushin abinda Ya Mahmud yayi masa. amma ga mamakina bai bari maganar ta hadamu ba sai ma wani murmushin yake da ya dinga yi har ya shiga motarsa ya bar wajen.

hello my people! how far?? me kuka gano game da Imamu? meyasa yake da matsala da kowa ne? meye hadinsa da Mahmud? shin kuna tunanin hasashen da Zara take akan Imamu da Aisha gaskiyane? meyasa zasu ci amanarta haka?

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now