HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE THIRTY-FOUR

784 61 7
                                    

A zaune cikin motar na same shi cikin shigar farin armani trouser, farar shirt, da wata irin blazer royal blue wadda ta fiddo da zallar fara sol din fatarshi mai kashe ido! the guy is handsome and stylish! ya samu duka wata sura mai kyau da duk dan'adam din da ya samu zai alfahari! amma kash! zuciyar baki kirin take kwatankwacin bakin duhun daren da bazai kwatantu ba! kaicon wannan sura da ta butulcewa ni'imar mahaliccinta ta zabi gode masa ta hanyar bijirewa kyakyawan koyarwar addininsa da gargadinsa! A sanyaye na karasa gefen hagu na bude motar na shiga cikin sallama!
"Good day beautiful!" ya fada kamar yanda ya saba! ada wannan yar guntuwar sentence din mai dauke da kalmomi uku cikin wani matsanancin farin ciki da nishadi take jefani, sabanin yanzu da idan naji ta nake jin wasu zafafan kibiyoyin bakin ciki na tsirar zuciyata! daurewa nayi muka gaisa tare da cigaba da hirar da shi yake ta faman zakulota har muka isa tulip bistro! my (new favourite spot in abuja!) ni kadai nake tahowa tea room na dauki lokacina ina shan shayi ina tunanin rayuwa, hakan na ragemun yawan tension din yake kaina sosai!
Bayan mun zauna an cika gabanmu da abubuwan da mukai ordering ne yake ce mun "It's really getting late beautiful, bamuyi prewedding shoots dinmu ba!" tabe baki nayi kafin na kai lomar cinyar crispy spicy chicken da na yago da hannuna! na tauna a nutse na hadiye. na kora da lemo kafin na dago na kalleshi! "Prewedding pictures baya daya daga cikin abinda yake burgeni! kuma bana fatan ka matsamun akan lallai sai munyi please!" sosai yanayin fuskarshi ya sauya wannan murmushin yaudarar na koda yaushe ya dauke! amma sai baiyi magana ba yaci gaba da cin nashi abincin! sai da muka kammala sannan yace " for the first time nace ga abinda za'ayi a bikin nan kikayi rejecting why? na miki laifi ne?" da ina da iko a wannan lokacin mari zan sharara mishi akan wannan tambayar rainin hankalin toh yabi duk wata kafa da zata bani damar yin hakan ya tsoshe da bakaken plans dinsa na zalinci da mugunta! sai kawai nayi murmushi nace "Babu laifin da kamun! ra'ayi ne bani da shi akan hakan! Duka hotunan da za'ayi a hakura zuwa ranar bikin mana" numfashi ya sauke kafin yace "As You wish my beautiful bride! I can't wait wallahi i just can't wait for our big day " sannan ya saki wani shu'umin murmushin da zaki rantse da Allah daga cikin zuciyarsa yake futowa! kai!! anya akwai mutum mayaudari a duniya irin Imamu? Idan yayi playing wani role din soyayya sai kice daya daga cikin jaruman bollyhood director ya dorawa camera, irinsu ShahruKhan da Shahid Kapoor! in kuwa yana rausayar da kai yana rangaji to ko Ali Nuhun kannyhood albarka.

Muna hanya wayata ta dinga ringing! a tunanina Aisha ce, don haka naki dauka domin har yanzu bamu daina mujadala da ita ba! Imamu ne yace "ki dauka mana? it may be important" don kar ya zargi wani abu na bude jakar na ciro wayar! "Big Brother" screen din ya nuna! da wide smile nayi swiping na dau kiran! cikin murna nace
"heloo! Big brother i miss you sooo much! 2days wayanka not reachable! me ya faru? yaushe zaka taho?"
cikin dariya yace "huh! Little sister when will you change? wannan questions lokaci daya?"( Tun bayan dawowarmu daga tafiyar da mukai muka kallabawa juna big brother da little sister ) cikin dariyar nima nace "huh' uh! someone cannot miss his brother kuma? duka fa doki ne" gyaran murya yayi yace "kina jina Zara?" Anan na gano maganar da zaiyi ta gaba mai muhimmanci ce don haka nima na nutsu nace "eh inaji" sannan ya soma magana! "Naso kwarai fiye da tunaninki na taho amma wani akwai........" cikin sauri na katse shi da cewa "big brother can i call you later? muna hanya ne tare da Imam!" cewa yayi "all right! don't forget to call me! take care!" daga nan muka ajiye! Motar shiru tayi na wasu mintuna kafin Imamu yace "menene ake son discussing ba'a gabana ba? me ake boyemun? ina cewa nima na zama family?" dariya nayi cikin  zuciyata amma a fili cewa nayi "Me za'a boye ma kuwa? hirar ce naga zata iya daukan mu lokaci me tsayi shiyasa naga gara idan na koma gida na nutsu a kira shi!" girgiza kai yayi yace "hira ko magana?" cikin kosawa da zancen nace "Duka babu wanda babu" sannan na sauya maganar da wata!
Ana kiran sallar magriba ya ajeni a gidan Mami ya tafi!

Gidan cike na same shi da kawayen mami masu zuwa tayata tsare tsare, dakyar na samu kaina daga hannunsu na shiga daki na watsa ruwa na sanya kayan bacci na kwanta! take na tuna zan kira Ya Mahmud don haka na mike na dauko wayar na dawo gadon na kwanta ina latsa lambobinsa!
bugu daya ya dauka "Hello sister kun dawo" nace "eh mun dawo na kagu naji maganar da zaka mun Allah yasa dai lafiya" cikun nutsuwa yace "No lafiya kalau sai dai nasan ba zai miki dadi ba" gabana ne ya fadi kafin nace "kuma kace lafiya kalau? menene don Allah?" sai da ya furzar da hucin bakinsa sannan yace "Little sister kiyi hakuri, bazan iya tahowa bikin ki ba" cikin mamaki nace "what? bangane ba? ba zaka zo ba? idan baka zo ba waye zaizo?" sanyaya murya yayi yace "calm down sister! kiyi shiru ki saurare ni" raina a bace nace "inajin ka" yace "yauwa my little sister! kina jina? aiki ne ya taso mun zuwa America in less than two weeks kuma yana da matukar amfani ga career na! sannan ina gamawa akwai taron da hukumar WHO zata gabatar akan cutar Ebola tare da wasu kunguyoyin lafiya na kasashen Africa! ina kammala wannan aikin akwai patient dina guda biyu da zanyi wa CS wadanda nayi wa IVF kwanakin baya! kuma ni nakeso na tsaya akan aikin!
Nayi iya bakin kokarina Zahra naga na tattara ayyukan na cire ko kwana hudu ne nazo amma ba zaiyu ba! kinga na dade ina hutu ban dade da komawa aiki ba! I don't know ko kin fahimci ba da niyya ne nayi wannan ba" ajiyar zuciya na saki a hankali! duk da nayi matukar rashin jin dadin zuwan shi amma hakan bai rufemun ido na kasa gano uzurinshi ba! don haka nace  "Na fahimce ka Brother! na gamsu! kada ka damu wallahi babu komai, kaje kayi ayyukanka a nutse ka tayani da addu'a! but you have to promise me kana kammalawa zaka zo ka ganni" Cikin tsananin farin ciki yace "ohhh That's my girl! dadina da ke akwai tunani mai zurfi! nagode sosai da kika fahimce ni! kuma nayi miki alkawari ina gamawa da aikina zan taho Nigeria kinji? addu'a kuma ba sai kin roka ba, kullum ina yi miki sister!  Allah ya baki wanda zai kula da rayuwarki cikin amana da aminci da tausasawa! Allah yasa ki cikin farin cikin da ba zai yanke ba ya baki zuri'a mai albarka" Tuni hankalina ya soma tashi da addu'o'in shi domin nasan ba suzo dai dai da mutumin da nake shirin aura ba, farin ciki kuwa tun kafin auren mukai sallama da shi balle kuma bayan na shiga gidan, na tabbatar babu abinda zai biyo baya sai tarin bakin ciki da tashin hankali da masifar da bansan iyakar su ba!
"Zara! Zara!!" firgigit na dawo daga tunanin da na tafi tare da amsawa! cewa yayi "are you okay?" nace "i'm fine Brother bacci nake ji" a sanyaye yace "okay! take care of yourself!" daga nan mukai sallama na aje wayar!
Gabadaya ji nayi gajiya da baccin da ke tare dani sun gushe! wani mugun tashin hankali ya ziyarceni!
kullum kwanakin farin cikina ne suke karewa, wacce irin rayuwa zan fuskanta a gidan Imamu? wanne irin shiri yayi wa aurenmu? wanne irin plans ya tsara a kaina? wacce ukubar yayi niyyar jefa rayuwata ciki?" wannan tunanin ya haddasawa darena kunci da tunani da radadin zuciya! har Mami ta shigo dakin, nayi maza na kulle idanuna kamar na dade da bacci, har ta kammala shirin baccin ta ta kwanta ban motsa ba!
Haka na kwana tunkur ina tunani zuciyata kamar zata balle don ciwo da radadi!
Da safe haka tashi da wani irin slight headache mai nukurkusar kwakwalwa da jijiyoyinta! haka na futo nayi breakfast a kasalance sannan mai gyaran jikina ta soma aikinta a kaina! bani na samu kaina ba sai bayan azahar sannan nayi wanka na dau mota zuwa gidan Ihsan! yau muke meeting da manyan kawayenmu akan bukin! komai na bukin Aisha da Ihsan ne suke shiryawa babu hannuna babu yawuna, sai dai na bisu da "toh" kawai! Gidan a cike na same shi da kawayena, tsoffin class mate dinmu na secondary school da kuma course mate dinmu na yanzu duk da ni na daina zuwa makarantar!
Ganinsu ya sani sakewa muka dinga hira da wasa da dariya! harda masu reharzing rawan da zasuyi na shigo da amarya da step dance! ni dai na kan bisu da ido ne kawai ina fatan dama ace wannan auren babu wata sarkakkiya acikinsa, dama babu wani boyayyen al'amari aciki, da babu abinda zai hanani farin ciki da alfahari da dombin soyayyar iyayena, yan'uwana, da kawayena suke nuna mun!
Bamu muka tashi ba sai wajen karfe bakwai na dare! sannan kowa ya nemi hanyar gidansu. tare da Aisha muka taho gidan Mami zata kwana, yawanci yanzu takanzo mu kwana tare tunda lokacin bikin ya matso kusa.

Muna shigowa na tarar da A.Laila tazo! a guje naje na rungume ta ina murna! tace "kai Zara kinga kyan da kikayi? masha Allah! sai da kin rame sosai tunanin me kike yi?" murmushi nayi nace "A. Laila babu komai inaga zirga zirga ne da rashin hutu" mun dade muna hira kafin naja hannun Aisha zuwa kitchen, don duka abincin gidan an cinye! kallonta nayi nace "me zamu dafa Aisha? cikina ba zai dau Indomie ba" dariya tayi tace "meye kuke da?" nan muka shiga bude bude muna neman abubuwan da zamuyi amfani da su! a karshe muka futo da tarkacen kayan chicken  shawarma! ita na bari tana hada sauce din da za'a saka a ciku nikuma na hada mana oreo milk shake! kafin wani lokaci mun hargitsa gidan da kamshi! daga yin shawarma biyu muka buge da yin guda goma don su Mami duk cewa sukai zasu ci! a Tray muka shirya namu abincin muka futa muka bar Aya tana gyara abubuwan da muka bata.
Dakin Mami muka koma muka barbaje muna cin abincin muna santi!
  
"Zara jibi zanje Katsina fa?" cikin yamutse fuska nace "katsina kuma? me zakiyi a katsina?" cewa tayi "visiting din Iky!" murmushi nayi "Allah sarki Iky daman ba busy nake ba mu tafi tare! amma kema dai Aisha ba dake ake zuwa kullum ba, ki bar Umma mana taje, kina ganin yanda muke tsakiyan shirye shirye" a nutse tace "Umma ba zataje ba, kinga gobe cikin dare Daddy zai dawo kuma baza taji dadi babu wanda yaje ba" da confusion nace "ah toh ke da waye zakije  babu Umma ba Daddy?" sai da tayi tsaki sannan tace "Ya Aslam mana! daga dawowanshi zai fara shiga harkokin mutane" nayi wata muguwar dariya sannan nace "amma Ya Aslam ya dawo baki gayamun ba Aisha? what kind of sister are you? kice wani love trip aka shirya aka fake da visiting" pillow ta rarumo akan gado ta jefomun fuskata! nayi maza na tare ina dariya! idan akwai wanda Aisha ta tsana babu gaira babu dalili toh Aslam ne! Aslam dan yayan Umma ne Uncle Taufeeq suna zaune Kaduna! shi ba cewa yayi yana sonta ba ma kawai he is being so nice and caring to her amma tabi ta damu kanta akanshi!
bayan na gama dariyan ne nace "ok! naji a mota zakuje?" tace "flight zamu bi sai mu dawo a mota" nace "Allah ya kaimu, ki tunamun pls kafin ki tafi gobe zan baki sako ki kai mata" tace "in ban manta ba nima" na harare ta "da yake ba ke zan baiwa ba"
mikewa tayi ta tattara duka kayan da mukai amfani da su ta futa ba tare da tace komai ba! kullum jikinta a sanyaye yake amma kwana uku zuwa yau abun yayi yawa, sai tayi shiru ita kadai kamar me tunanin wani abu idan ka tambayeta tace ita babu abinda take tunani! Duka ta saka damuwa a ranta game da aurena da Imamu, tama fini ramewa!

If you are reading this on friday, don't forget to read suratul kahf! jumu@ Mubarak to you all!

Hausa Arab yana ci gaba yana kara zafi, domin labarin na dab da sauya akala zuwa wani abu mai jan hankali? ko menene? akwai abubuwa masu yawa da zasu faru wanda yake nuna daga yanzu ainihin labarin yake farawa! da kuma  wani abu wanda zai tsuma ranku da zuciya, gaba kadan kuma wani babban abun mamakin da baku taba kawowa ba zau faru!duka dai cikin wannan labari!
ku biyoni!

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now