Tsayawa nayi cak a sakamakon jin kafafuna na niyyar zubewa a wajen. Wannan ya bashi damar karasowa gefena tare da yan yaran da baza su wuce shekaru shida ba. "Assalamu Alaikum" ya sake magana a karo na biyu. Ji nayi kamar a mafarki scene din yake faruwa. "Daman anawa musulmi sallama yaki amsawa?" Yayi magana a karo na uku. Sai a lokacin na saisaita kaina na kirawo nutsuwata da class dina na kalle shi cikin isa nace "wa Alaikumus salam, amma kuma bai dace ka tsayar dani cikin public haka ba" murmushi yayi duka hakoransa talatin suka bayyana farare tas sai na soma ganin kamannin wani indian actor mai suna "Shahid kapoor" a tare da shi. "Ok..I'm sorry ma'am ki bani phone number please idan kinaso na daina binki" rolling eyes dina nayi nace "kawai kuma sai na baka number na ko?" Yayi murmushi sannan yace "fine...idan baki bani ba kuwa yana nufin duk inda kikasa kafa zan mayar da tawa daga nan har zuwa duk ranar da kika shirya bani bazan gaji da binki a baya ba" juyawa kawai nayi na tafi ina ganin kamar babu class na bada number da sauki haka. Amma kuma me? Duk inda nayi yana biye dani da yan yaransa! Wannan ya sanya na sake juyowa cikin fushi nace "Malam please ka daina bina banaso" cikin kwaikwayon muryata shima yace "Malama please ki bani number sai na tafi" murmushin mugunta nayi a lokacin da na tuna zan iya bashi number bogi. Sai dai kuma ya zanyi da sonsa da ya yi mun shigar sauri lokaci daya? Dole na shiga kira masa numbobin yana shigarwa a wayarshi sannan ya kira. A hankali sautin ringtone din iPhone dina ya soma tashi. Yayi murmushi mai kayatarwa sannan yace "na zata zaki bani fake ne ko wadda ta daina aiki! Sannan ya dubi yaran yace musu "my babies meet your new Aunty name? Ya dubeni yana dage giranshi. "Zara" na fada a sanyaye. "Good!! meet your new Aunty.... Aunty Zara" duka yaran suka soma dariya suna kallona. Sannan daya yace "Aunty Zara do you have sweet?" Dariya sosai yaran ya bani na soma murmushi. Cikin high tone baban yace masa "what's wong with you Fahad? Kowa ka gani sai ka roke shi sweet?" Jakata na balle duk da nasan bani da sweet din sai chocolate din bounty da muka futa da Aisha ran nan ta siya ta bani. A jakar na barsu ban sake bi takansu ba sai yau din da na dauko jakar. Guda hudu na ciro kowanne na bashi biyu suka amsa suna ta murna. Kallonsu yayi yace "oya what do you tell Aunty?" Gaba daya suka hada baki suna dariya suka ce "Aunty thank you" nayi murmushi nima nace "you are welcome" sannan na wuce da sauri don ganin maganganun na shirin yin yawa.
Dakyar na lalubo Aisha da yaran suna ta bata wahala ita kuma ba gwanar son yara ba. Na shiga yi mata dariya. Rai a bace tace "wallahi Zara yaran nan ba karamar wahala suka bani ba yau" cewa nayi "ke dai Allah ya baki yaya kamar goma muga yanda zakiyi? Yara biyu su dagula miki lissafi haba Aisha?" Tabe baki tayi tace "Allah ma bazai amsa addu'arki ba Insha Allahu. Yaro daya ko biyu zan haifa" nayi murmushi kawai ina mamakin wacce irin mutum ce Aisha!
Tare muka futo da ita ta shiga motarta nima na shiga tawa na dau hanya! Lokacin da na iso gida ana ta kiraye kirayen sallar magrib. Sai lokacin na tuna motar aro na dauka. Gabana yai wata irin faduwa a dalilin tuna halin mai motar nayi idan an bata mishi rai. A hankali nake tukin har na isa kofar gidanmu bugun kirjina na karuwa. Ba Lawan ya wangale mun gate na shiga a hankali. Bayan nayi parking motar dai dai yanda na daukota na balle murfin na futo ina addu'ar Allah ubangiji yasa Ya Omar bai zo gidan bayan na futa ba.
Kai ai da yazo ma da tuni a farfajiyar wajen nan zan ganshi yana tsaye yana huci yana jirana! Wannan ya bani kwarin guiwar shiga falon.
Sallamar tawa ce ta katse dai dai lokacin da na shigo cikin falon a sakamakon ganin Ya Omar zaune akan kujera fuskarnan babu rahama babu sassauci. Dada na tsaye ta zumbula dogon hijab dinta tana niyyar tayar da sallah. Habawa ai cillar da jakar nayi a guje na ari ta kare na bude kofar na futa da gudu. Ya Omar ya taso shima ya biyoni a guje abinda ya karamun kwarin guiwar gudun. Filin gidan muka shiga zagayewa yana bina a guje cikin tsananin fushi nikuma gani ba dai iya gudu da zillo ba duk dabararsa ya kasa kamani. Jin an idar da sallah ya sanya yayi wata irin kwafa ya futa daga gate din gidan.
Nikuma nayo cikin gida a guje na shige dakina na bar Dada tana tikar dariya. Ko ta mecece? Oho!!.
Bayan na zura key ne na fada gado ina mayar da numfashi kafin na kece da wata irin dariyar mugunta. "Gaskiya na iya gudu" idan na tuna yanda na dinga wana Ya Omar ina zizzille masa sai naji dariyar ta dawo sabuwa domin fuskarsa a wannan lokacin kawai abun dariyar ce. Iya haushi na shaka masa saidai fatan Allah ya hana haduwar mu a wannan kwanakin don na tabbatar sai na raina kaina.
A karshe dai toilet na fada nayi wanka da alwala nazo na shimfida dadduma nayi sallah. Ina matukar jin yunwa amma babu yanda na iya domin babu tsautsayin da zai sake futar dani daga dakin nan kafin shabiyu na dare.
A maimakon nayi zaman banza sai na dauko cardboard da drawing materials dina na soma zana hoton wani jibgegen mutum mai katon ciki tsaye ya rike kugu gefe guda na zana wata siririyar yarinya doguwa mai kyau rike da flower da dan card. a saman card din na rubuta "I'm sorry Ya Omar...i will never ever go near your car again" ina colouring zanen ina tikar dariya domin na tabbatar wannan zanen sai yafi daukar motar bata wa Ya Omar rai yanda ya tsani qiba a rayuwarsa kullum yana gym yana work out wannan 6pack din yanda yake ji da shi kamar ba mutuwa zaiyi wataran a binne shi ba. Ya tsani yaga mutum mai qiba a rayuwarsa ko mace ko namiji musamman yaga katon ciki......
I'm stubborn right? Daya daga cikin manyan halayena kenan da kowa ya sanni da su. Allah ya hore mun tsokana. Idan na saka mutum a gaba komai girmansa sai yayi kuka.
Sai dai kuma kafin nayi sabo da mutum har ya gano hakan ana dadewa.i look very innocent da zakai tunanin idan aka samun yatsa a baki ba zan iya cizawa ba.
A karshe dai ban futo daga dakin nan ba sai shabiyu da kwata sannan na shiga kitchen na hada tea mai kauri na debo damnbun nama acikin karamun plate da goran ruwan Faro karami na dawo dakina. A gaggauce na kammala ci na saka pj dina na kwanta. Na dauki wayata na sa a charji naga miscall guda goma daga wata kyakykywar special number. Babu tantama mutumin da na hadu da shi yau ne. Ya salam! Ya akai banji wayar ba? Ina can ina jan fada na yar da jakar a parlour. Mtsw! Yanzu ya zanyi? Sake duba wayar nayi sai naga messages guda biyu sun shigo na farko yana cewa.
"Salam beautiful! How was your day? Na kira ki bakya picking dafatan kina cikin koshin lafiya?" ..Imamu.Wow! I chuckled! Thats lovely. So sunanshi Imamu! What a sweet name!
Na sake bude dayan shikuma cewa yayi.
"I Love you Fatima!! .... ..i just cant wait to tell you this words"
Wata irin ajiyar zuciya nayi idanu na ya cika da kwalla. This is the most beautiful message ive recieved this year! Masha Allah. I love you too Imamu! Na fada a fili ina murmushi!
Ban iya bacci ba a wannan daren sai tunane tunane kala kala.
Kiran sallah ne ya tashe ni daga nannauyan baccin da bansan lokacin da nayi shi ba. Bakina dauke da addu'ar farkawa daga bacci na tashi zaune sannan na laluba dankwalina na daure kaina na shiga toilet nayi alwala. Bayan nayi raka'atanil fajr na saurara masallaci suka tada sallah na bi jam'i. Kamar kullum bayan na kammala azkar din safe alqur'ani na na dauko na bude surah kahfi na karanta na karanta surah maryam da surat Daha. Favourite surorina a alqurani. Sannan na nade kayan sallar na koma gado na kwanta. Ban tashi bude idona ba sai shadaya na safe.
Cikin sauri na shiga toilet nayi brush na dora hijab akan kayan baccina na futo muka karya tare da Dada.
"Jiya haka kika kwana baki ci komai ba kenan?" Cewar Dada. Murmushi nayi mai sauti sannan nace "na futo Dada amma sai wajen Shabiyu da rabi na sha tea na koma daki"
Girgiza kai tayi tace "sai ki zauna cikin taka tsan tsan kuwa don ina jiye miki haduwarku. Dariya nayi sosai.
Ta sake cewa " idan ya ritsaki a parlour ko a kitchen naga filin da zaki irin gudun jiya. Yarinya kamar dila? Bansan inda kika koyo tsokana ba nikam! Indai Aliyu ne kinci bashi don ba'a cin bashinsa a kwana lafiya" har ta gama maganar ban daina dariya ba. "Dada kawai daga daukar mota? Sha'awa ta bani wallahi. An wanke sai kyalli take" girgiza kai tayi tana cin sandwich. "To an gaya miki wankin na banza ne? Shiryawa fa yayi zaije zance safiyyan ta dawo daga Amrika jiya" wow!!! Bakina yayi forming "O" shape." Allah sarki Ya Omar. Gaskiya ban kyauta ba.....wallahi bansani ba Dada. Shiyasa temper dinshi tafi na kullum"
Murmushi Dada tayi tace "kya dai hadu dashi." Sosai naji tausayin sa. Domin nasan irin son haukan da yakewa Sofiyya amaryarshi nan da watanni hudu. Sofiyya yar gidan minister of women affairs ce Hajiya Naja'atu saleh. Her only child a duniya. Duk da gatan da take ciki Tana da mutsuwa da kamun kai da kuma addini ga ta kyakykywar gaske. A halin yanzu likata ce kwararriya ta bangaren paediatric (yara). Kwata kwata satinta hudu da kammala karatun amma sai jiya ta dawo Nigeria daga kasar NewYork din America.
Toh ba dole kuwa Ya Omar ya wanke mota ba. Gaskiya ban kyauta masa ba.
Ni kaina na saba da ita sosai tun lokacin da Ya Omar ya kawo ta ta gaida Dada mukai exchanging contact muna yawan magana ta WhatsApp wani lokacin kuma nakan kirata mu gaisa. She is very nice and friendly!
Sau biyu yana kaini gidansu.
Ita kuwa wadda Ya Sadik zau aura balarabiyar Hurgada ce ta kasar Egypt. Mazauna Nigeria gabadaya hausar ta bata futa. Daga Arabic sai turanci. Tare sukai karatu da Ya Sadik a American University of Paris. Daga nan sukai matukar shakuwa wadda ta rikide ta koma soyayya. Wannan kenan!Ina komawa daki waya na dauka na kira Aisha! Yeah to tell her abinda ya faru jiya da yamma a Maitama park. Bamu taba boyewa juna wani abu ba. She is my best friend and the sister i never had. Tare muka taso makaranta daya islamiyya daya komai tare muke yi. Mun wuce kawaye mun wuce aminai mun koma yan'uwa domin har iyayenmu mun kulla su zumunci mai karfi. Bayan na kammala bata labarin ihu ta sanya mun da ya kusa kashemun dodon kunne! "So bestie has finally..." katseta nayi a cewa "kinga don Allah sai mun hadu a school gashinan yana kira" ban jira komai na na katse kiranta na dauki na Imamu wanda yake ta shigowa tunda na fara wayar.
Hello dearis! How is this page?
Am i boring you? I need your comments.inaso naji daga gareku.
VOCÊ ESTÁ LENDO
HAUSA ARAB PART 1
Ficção GeralAlqalamin qaddara yana aiki akan kowa ba tare da zabin wance ko wane ba. Kowanne bawa da irin na shi salon rubutun, na wani ba irin na wani bane.