HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTUFANTASIA PAGE FORTY-FIVE

832 64 4
                                    

Su Mami ne suka soma tafiya mu kam bamu bar asibitin ba sai wajen 9 Ya Nuratu ta jani dakyar muka tafi. Don ji nake kamar nayi ta zama ina kallon babyn. Ihsan har yanzu bacci take don tasha wahala sosai.
Muna dawowa Ya Nuratu ta soma shiri ita da Amal, Dada ce tace lallai ta shirya su tafi Kano tare da Ya Mahmud taga gida. A tsarin Ya Nuratu ba tai niyyar zuwa ba, domin basa jituwa ko kadan da Inna badi'atu, Kamar ba ita ta haife ta ba. Sai da Dada tayi mata nasiha sannan ta yarda ta soma shirin.
Nikam ba karamun farin ciki nayi ba da jin zabin da Daddy yayi wa Ya Mahmud na Amina, Allah yana kallo bana masa sha'awar Safna ko kadan! Bana mishi burin auren mace irinta kuma ina mamakin yanda akayi ya amince da auren nata, inaga hakan bai rasa nasaba da zamansa cikin turawa tsayin shekaru. Amma idan ba sabo da zama cikin turawa ba babu abinda zai kai shi tunanin auren mace mara kamun kai irin Safna. Don haka sai murna ta ta sake karuwa akan ta da.
A lokacin baya na sha addu'ar Allah ya kulla soyayya tsakanin Ya Mahmud da Aisha duk da ban taba furtawa wani ba,amma naso kwarai ace ya samu mace irin Aisha. Ashe akwai abinda Allah ya rufe. Da hakan ya faru sai ana gab da biki zata mutu ya sake fadawa halin da ya shiga a lokacin mutuwar Jawahir kilama a soma Canfa shi ace a dalilin sa matan ke mutuwa. Allah sarki Aisha! A kullum kwanan duniya sai nayi kewarta, babu wani abu da zai faru dani ban tuna Aisha ba. Saboda da ita na saba, ita kadai na saba gayawa damuwata da farin cikina, da ita nake shawara, da ita muke kashewa mu haka rami mu binne babu wanda ya sani. Wata shakuwa ce tsaukaninmu irin ta yan uwan da suka futo ciki daya.
Hakika nayi rashi! Nayi babban rashin da bazan maye gurbin shi ba. Tsakanina da Aisha sai addu'a wadda bana mantawa, duk lokacin da na nisa zanyi mata.

Wanka nayi na shirya na yafa gyalena na futo! Tuni Baba Rabi ta hada abincin da Dada tace tayi na tafi da shi asibiti!
Amal na kalla wadda take ta faman kumburi tasha kwalliya cikin voile riga da skirt mai kyau da saitin gold dinta wuya da hannaye! Kamo hannunta nayi nace "Amal yaya dai? Ko kayan ne bakyaso kike fushi?" Cikin shashsheka tace "Ni banason naje gidan Inna! Nafi so na zauna anan! Kice wa Maama na zauna anan" a raina Allah wadai nayi da halin Inna. Yar cikinta da yar mitsitsiyar kwallin jikarta na gudun zuwa wajenta saboda mugun hali.
Tsugunawa nayi na kamo hannunta na soma lallashinta "No Amal ba haka ake ba! Ya zaki bar Maama tafi ita kadai wajen Inna? Kinaso Inna tayi fada meyasa bakije kin gaida ta ba?" Shiru tayi tana niyyar soma kuka na sake cewa "And you know what? Amaryar Ya Mahmud tana kano ko bakya so kije ki ganta?" Sai lokacin tace "da Uncle zamu je?" Na girgiza mata kai ina cewa "yes! da shi zaku tafi Amal! Are you happy now?" Tayi murmushi tana daga kai.
Dada ce tace "Allah ya kyauta halin Badi'a Allah ya dawo da ita kan hanyar gaskiya! Wannan bakin hali har ina? Ace naka yana gudunka kiri kiri saboda bakin halinka" Ni dai gum nayi da baki kaina a kasa domin ina kunyar idon Ya Nuratu. Ita kuwa kamar ta fashe da kuka don takaici, a dole za tai wannan tafiyar ba don tana so ba.
Ya Omar ne yayi sallama ya shigo! Cikin murmushi nace "mu futo ne Ya Omar?" Harara ta yayi yace "Wai don Allah gani kike kamar lokaci daya aka haifemu mukai kuruciya tare ne?" Dariya ya bani yanda yayi kicin kicin yana masifa. Dada tace "kaga fara zuwa mu kammala abinda na kira ka sai ku soma fadace fadacen naku idan ma casuwa zaku yi zan baku wuri" murmushi nayi nace "Dada yanzu menene laifina? Daga nace mu futo?mu da muke expecting baby anytime ba dole ana ganin shi a tambaya ba" da sauri ya nufo ni na tashi a guje nayi bayan Dada ina dariya.
Muna cikin haka Ya Mahmud yayi sallama cikin wata kamilalliyar shiga. Babbar riga ta blue din voile wanda ya amshe shi sosai. Ya daidaita wata tsadaddiyar hula akan gyararriyar sumar sa sai walkiya yake. Kamar yau ne daurin auren. Kamshin "La Nuit" ya karade falon.
Futowa nayi daga maboyata ina cewa "wow! Ya Mahmud you look extra-ordinarily handsome!soo Masha Allah" na karashe "Masha Allah" da wani tone na yabawa ina yiwa Ya Omar gwalo domin shima irin kayan ne a jikinsa bambamcin kawai shi nashi karamun dinki ne. Ya Omar da Ya Sadik duka farare ne sol dogaye masu matukar kyau, shikuwa Ya Mahmud yayi duhu duk da ba baki bane, Amma idan ana yi maka maganar kyau zalla mara gauraye toh Ya Mahmud abun misali ne! Zakai matukar mamaki idan aka ce ma bahaushe ne, baiyi kama da fulanin ba, kana ganinsa zaka dauka cikakken balarabe ne duk da farin shi bai yi yawa ba. Yanayin gashin sa da har yau yake a kanannade kamar na sabon jariri, da kuma kalar idanun shi wani irin fari kamar nono, bakin ma baki wuluk babu sirki, an diga wani abu mai maiko da zaka dauka hawaye ne ya taru, idanun marasa juriyar kallo ne, don da kansu suke lumshe kansu kamar masu jin bacci.
Bayan haka kuma wani sinadari da wata baiwa da kwarjini da ilhama Allah ya wadata shi da su wadanda suke futar da shi unique cikin daruruwan mutane. Duk kwalliyar da yayi dacewa take da shi! Duka kalar da yayi amfani da ita kyau take masa both English and traditinal wears.
Sirrin armashin gayun nashi kuma bakomai bane illa tsabar tsafta, wayewa, da sanin abinda ya dace da shi sannan komai nashi mai inganci ne, kuma unique. Wannan guntun handkerchief nashi designer ne da sunan shi balle kuma tufafinsa da takalman sawarshi. He is sure, a designer Guy. Ya amsa wannan sunan!
Bai tsaya anan ba, ya samu karin nagartattun halaye. Yana da far'a sosai musamman ga mutanen da ya saba da su! Yana sanyin rai da raguwar zuciya mai tausayi da jin kan na kasa da shi, yana da kyauta da son farantawa mutane. Sai dai kamar kowanne mutum tara yake bai cika Goma ba.
Cikakke Wanda yafi Goma cika sai Annabin Allah saw. Mahmud na da nashi cikas din irin na kowanne Dan Adam.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now