HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE THIRTY-SEVEN

886 71 7
                                    

"And now you have gone away and left us with the memories of your smile"

Kallon Umma kawai nakeyi amma kwakwalwata ta kasa fahimtar dani abubuwan da take son na fahimta! Ga dai Aisha a kwance babu numfashi, amma sam na gaza gasgatawa dagaske Aisha ta mutu! Kaina ya kasa yarda ya dau kalmar mutuwa akan Aisha! wannan karon na karyata idanuna, na karyata kunnuwana kuma na karyata duka abubuwan da nake gani a zahiri wadanda suka fi dacewa ace a fefen majigi suke faruwa.

su Mami ne suka zo suka daga Umma daga gaban Aisha suna bata hakuri yayinda karfin kukanta yake karuwa. Dada ta riko hannuna ta taso dani zuwa inda take zaune tana nazarina!
babu abinda ake wannan falon banda kuka! wasu na fili wasu na zuci, wadanda basu yi kukan kuma idan kalli fuskarsu ba zaka so ka kara ba!
Nidai na zama mutum mutumi, bana cewa uhm balle uhm uhm! Kawai dai ina jiran lokacin da zan farka daga baccin da nake har wannan mummunan mafarki ya shigo mun!

mintina ashirin bayan nan yan'uwan Daddy na Kaduna suka iso, kowanne yana shigowa zai fadi ya rafsa kuka yana jajanta wannan gimgimemen rashi na matasan guda biyu! Yan'uwan Umma ma na kusa sun zo kafin zuwa safiya iyayenta su iso daga Bauchi!

Manyan matan cikinsu harma da Dada su suka shiga cikin dakin da aka dauki Aisha aka kai don yi mata wanka da sutura! daya dakin kuma Ya Aslam! karfe gomasha biyu dai dai aka kammala hadasu! Anan ne Ya Omar da Ya Sadik sukai sallama suka tafi gidajensu da cewa zasu dawo da safe jana'iza!
Bayan an kammala shiryata ne aka kira Umma da Daddy suyi mata addu'a! ba'a samu wanda yafi wani jarumta a cikinsu ba, zubewa sukai gaban gawar suna kuka na tashin hankali mai tsuma ran duk mai saurare! dakyar aminan Daddy suka futa da shi zuwa guess room dinsa suna bashi baki! ita kuma Umma aka maida dakinta aka kwantar a dalilin suman da tayi! sannan aka kira likita.

Lokacin da na shiga dakin Aisha tsayawa nayi cak ina karewa dakin kallo! komai na zaune tsaf inda ya dace qal qal! banda katuwar rug carpet din da ke tsakiyar dakin da aka nannade aka mayar da tabarmar da aka kwantar da gawar Aisha a sankame! An nade duka jikinta da farin yadi an daddaure ta.
A sanyaye na isa gaban drower gado na bude, diary dinta ne a farko har zan ciro shi sai kuma na mayar na rufe na bude drower kasan na dauko al'kurani!

Kusa da kanta na dawo na zauna tare da tsirarun mutanen da ke dakin ciki harda Ya Nuratu da Dada! surat Yaasin na bude na soma karatuna a bayyane! babu abinda nake ayyanawa a raina sai "Idan har mutuwa kikayi Aisha dagaske, to ai babu abinda ya dace na nuna miki na kauna da ya wuce na karanta miki al'kurani a kan gawarki!" cike da confidence nake karatun siririyar murya mai taushi! sai sauran matan suka dinga bina a hankali, ina kaiwa karshen sura zan dawo farko, Nakan sabunta alwala acikin toilet din dakin nayi karatun kamar sau biyar ko shida!

Karfe hudu wasu bakin suka kuma sauka, dakin ya kara cika, amma sam ban yarda anyi magana ko da sau daya ba, karatu mukeyi gabadaya da murya guda, cikin taushi da karyewar zuciya! Dada kam casbahar ta ce kawai a hannunta tana ja, idan ta dau lokaci ta kafeni da idanunta tana mun wani irin kallo mai ma'anar "Ba'a hayyacinki kike ba"

koda minti daya ban tashi daga gaban gawar Aisha ba sai dai yin alwala kawai. har akai kiran assalatu, muka tashi mukayi sallah gabadaya, ita kuwa tana kwance babu motsi babu numfashi! a parlour mukayi sallah, muna idarwa Yan Bauchi na isowa! kakar Aisha da yan'uwan Umma maza da mata motoci shida! Nan fa gida ya kacame da sabon koke koke! Ni dai ina rakube jikin Dada ina kallon mutane dai dai kamar wata sabon kamu!

Ana cikin haka Ihsan ma ta iso! taci kuka ga gode Allah! tana ganina ta fado jikina ta sake fashewa da wani matsanancin kukan! ni dai da ido nake binta kawai tunanina a tsaye cak! Dakyar Dada ta samo kan Ihsan ta nutsu ta daina kururuwar kukan da takeyi! Babban wan Umma ne ya shigo falon ya tsaya a tsaye ya soma nasiha da nuna rashin dacewar ihu da koke koken akan gawa, ya fadi abubuwan da ya dace muyi! sannan aka samu sautin koke koken ya ragu sai masu share hawaye da shashsheka! sai masu salati da kiran Allah!

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now