HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE TWENTY-ONE

932 68 7
                                    

A hankali nake motsa fatar saman idanuna ina juya su kafin na samu damar dage su a hankali na bude! wanda kwayar idanuna suka dira a kansa wani matsakaicin mutum ne baki mai kewayayyiyar fuska ma'abociyar haiba da kwarjini! ba wani kyakykyawa bane amma sam ba zakaso dauke idonka akan nashi ba! farar labcoat ce a jikinsa wuyansa rataye da stethoscope yayinda idanunsa ke sakaye da garai garai din medicated glasses! a dakikun da basu fi goma ba na yi wannan hasashen!
"are you okay? can you talk?" ya fada cikin British accent da sassanyar murya! What the hell is wrong with me? why am i checking him up?" firgigit na dawo da tunanina duniyar da nake! na soma tunanin toh ina ma na san wannan bawan Allah? meya kawo shi wajena? idan zan tuna ai ina kwance ne kan doguwar kujerar falon Dada kaina na barazanar rabewa biyu! sai na soma juya kwayar idona ina karade dakin da kallo! dan karami ne mai wadataccen haske! daga painting har komai na dakin farine sol! dana kalli jikina sai naga kayan da suke jikina ne dai na dazu sai dai kimono din da aka cire mun aka barni da armless top dina fara sol! farar nurse ce a bayan likitan tana dauke da tasar da aka cika da tarkacen likitoci dukan idanunta akaina! a hankali na sake maida dubana ga likitan da na soma bude ido akan fuskarsa! "He is quiet! just observing and reading my face" saida na lashe busassuna lebbana na samu damar soma magana a hankali!
"meya kawoni nan? Ina Dada? ina Mamina? meya sameni?" murmushi ya danyi wasu lafiyayyaun ingantattun hakora masu bayyanar da samun kulawa ta musamman suka bayyana tare da siririyar wushirya a tsakaninsu! da sautin da yafi na dazu karfi yace "don't worry! kina asibiti ne! wadanda kike tambaya kuma suna nan tare da ke! amma zaki dan huta zuwa wani lokaci kafin a soma shigowa a miki hayaniya" a hankali na girgiza kaina! ya sake cewa "yanzu me yake damunki?" cikin rashin kuzari nace "Kaina yana mun ciwo!".
"bayan shi fa?" ya dora da wata tambayar! na girgiza kaina a hankali! sai lokacin tunanin abubuwan da suka faru dani a yau suka sake tariyowa cikin kaina. na kuma tabbatar ba mafarki nayi na tashi ba kuma ba wasa bane! sai naci ciwon kan ya kuma tsauri! "hello!" firgigit na juya ina kallonshi! cikin daurewar fuska yace "kin farka daga halinda damuwa ya saka ki ciki kuma zaki sake cigaba da tunanin abinda zai maida ke cikin damuwar? kinyiwa kanki adalci kenan?" a wannan karon da hausa yayi magana! murmushi kawai nayi bance komai ba! ya kammala examining dina aka tsira mun allurai. kafin su futa na soma bacci!

Ban sake farkawa ba sai karfe tara da arba'in da uku na safiyar washegari! Ya Sadik na soma gani a gefen gadona kan kujera! na juya idona gefensa Dada ce a tsaye kaina tana tofa mun addu'o'i! Su biyu ne tak a dakin! cikin rawar murya Dada tace "Zara kin tashi? sannu!" a hankali na soma karanto kalmar shahada kafin na daga mata kaina! Ya Sadik ya mike da hanzari yana cewa bari ya kira Doctor! mintina biyar suka shigo tare! Likitan jiya ne ya shigo tare da umartar su Dada su futa! da murmushi ya dubeni yace "kin tashi?" na girgiza kaina a hankali! "yanzu meye yake damunki?" nace "babu komai! inaso na tafi gida ne kawai" wani murmushin ya sake yi sannan yace "idan zuwa gobe munga kin daina wannan tunanin da ciwon kai zamu iya sallamarki!" na dan yamutsa fuska nace "Naji sauki ni! ba tunani nake ba" bai sake magana ba ya soma yiwa Nurse magana yana rubutu cikun file dina sannan ya juya ya barta dani ya futa! allurai tayi mun sannan ta taimakamun nayi brush nayi alwala! bayan nan su Dada suka shigo! Nan aka taimakamun nasha tea na biya bashin sallolin da suke kaina a zaune sannan na koma na kwanta!
Dada ce ta dawo kujerar gefen gadona ta zauna! hannunta ta dora akan goshina ta soma magana a hankali! "Zahra'u! meye yake damunki? meya shiga ranki yake saki tunani irin haka har damuwa take son yi miki illa? me kika rasa? me kikeso? likita yace damuwa matsananciya da tunani suka jefaki cikin halin da kike ciki! ki gayamun ko menene kikeso Zara nikuma nayi miki alkawari zan yi miki shi in dai bai fi karfin ikona ba"

A hankali na dago ina kallonta! nayi mamakin wannan furucin na Dada domin sai ta kure zakiji Dada na rarrashin mutum! tafi ganewa fada da nasiha amma rarrashi har da me nakeso? abun da mamaki! da ace babu matsalar da ke tsaninta da Mamina toh kawai cewa zanyi tamun alfarma ta janye maganar aurena da Imam bana son shi! amma yanzun akwai abinda yafi wannan muhimmanci! naga na gyara tsakaninta da diyarta zaifi komai yimun dadi! duk da bansan yanda zata fahimci maganar ba!
ina cikin tunanin ta katseni ta hanyar jijjiga kaina a hankali! nayi firgigit na dubeta! cewa tayi "Zara wannan tunanin ne fa ba'aso! shine kuma likita yace ya janyo miki halin da kike ciki! duka shekarunki nawa da zaki cinye irin wannan damuwar a ranki? meye amfaninmu idan har zaki kukan wani abu har ya kai ga ta saki damuwa? ki gayamun abinda yake damunki!
cikin karfin hali da muryar tausayi na soma magana! " Dada kiyi hakuri ki taimaka ki daina fushi da Mami da Ya Mahmud don Allah ki yafe musu!"
wani irin kallo tayimun har sai da cikina ya duri ruwa! sannan tace "waye ya gaya miki ina fushi da su? waye ya gaya miki abinda ya faru?"
Da duk dauriyata naci gaba da magana hawaye na bin kuncina!
"Dada naje gidan Mami ne zan kwaso kayana da na bari na buki sai na samu ciwon Ya Mahmud ya tashi yana ta wani abu har ya futa hankalinsa!" da Su Ya Sadik muka tafi asibiti da shi aka kwantar da Shi a daren! kowa na tambaya me ya faru baya amsamun sai dakyar Ya Sadik yayi mun bayani! Dada kiyi hakuri ki taimaka ki yafe musu! suna son ki Dada kuma suna neman afuwarki don Allah ki yafe musu!" na fashe da matsanancin kuka!
hankali tashe Dada ta dubi Ya Sadik tace "Saddiku? hakane abinda ta fada? Mahmud na gadon asibiti? kuma ciwonshi ya tashi?"

A hankali cikin tsoro Ya Sadik ya daga kansa! cikin matsanancin bacin rai Dada tace "amma baku gayamun ba? yana kwance a asibitin ba'a sanar mun ba? yanzu suna ina? wanne asibitin ne? wanne halin yake ciki?"
a sanyaye Ya Sadik yace "kiyi hakuri Dada! amma babu wanda yake da kwarin guiwar tarar ki da magana akan Ya Mahmud ganin yanda ranki ya baci! amma kiyi hakuri Dada ki mana afuwa!" sake cewa tayi "Yanzu yana ina? ya jikin nasa?"
ya sake tausasa murya yace "Babu laifi Dada da sauki! amma sun wuce London yau da asuba! domin ya samu ingantacciyar kulawa tunda ciwon ba karami bane kuma likitoci sun sake jaddadawa idan aka barshi cikin damuwa da tunani komai na iya faruwa dashi!"
zaraf Dada ta mike tsaye! sai kuma ta koma ta zauna! babu zato ta barke da kuka matsananci! har kasa Ya Sadik ya zuba guiwoyinshi cikin kaduwa yana baiwa Dada hakuri!
cikin kukan take cewa "buga mun babanku ka bani"
sake tausasa murya yayi yace "Don Allah Dada kiyi hakuri ki mana afuwa ba da gangan muka ki sanar miki ba! ba nufinmu mu bata miki ba! sai don ganin yanda ranki ya baci kuma ba laifin Daddy bane wallahi Dada! kiyi musu uzuri!" da murya mara karfi tace "cewa nayi fada zan mishi? ka buga mun kawai bani" ba'ason ransa ba ya shiga neman family line din Daddy, bugu biyu ya dauka! sai da ya gayar da shi sannan ya baiwa Dada wayar! dukanmu na mujiya muka zuba mata muji irin abinda ta tanadarwa Daddy na bacin rai amma ga mamakinmu cewa tayi "idan da hali inason jirgi zuwa gobe idan kuma ba zai samu ba kada ka damu zamu shiga na haya gobe da wuri nakeso na sauka a garin London!" kallon kallo muka shiga yi da ni da Ya Sadik kowanne yana tunanin abinda zai faru!..
-----------------------------------------------------------______________________________________
Lokacin da muka sauka garin London ruwa ake sosai wanda ya saukar da wani sanyi da ni'ima mai ratsa jiki! Daga Dada sai Daddy mukai tafiyar kasancewar su Ya Sadik suna shirin tafiya honey moon da matansu. la'asar likis muka shiga gidan Daddy na Sussex Garden! komai an shirya shi tsab. an kunna duka heaters din gidan ya dau wani dumi! Duka angle din gidan an aje sassanyan turarukan ruwa masu amfani da iska irinsu Mango and Papaya! wannan duka aikin Helen ce mai kula da gidan!
Daddy ko zama bai ba ya wuce Oxfordshire! Dakin da na zaba na bude na kai kayana sannan na futo na shiga kitchen don samar mana abinci domin Dada bata yarda da cin abincin bature ba! ko kwano Helen ta wanke bata cin abinci a ciki! in an magana tace kafiran banza kafiran hofi! dole ta baka dariya!
komai an aje a kitchen din ga cefane cikin kwaton kwando komai fresh! kifi na dauka nayi marinating na adana sannan na futo da ingredient din Tuna spaghetti. cikin lokaci kadan na kammala aikina na hada wa Dada Kunun tsamiya na jera mana komai a tsakiyar parlour! sannan na koma dakin Dada na sameta tana waya da Kawu Sulaiman! sai da ta kammala nace "Dada na gama abinci bismillah! ko nan zan kawo miki?" cikin murmushi tace "kai, dadina da ke Zara zafin nama da sanin abinda ya kamata! yanzu har kin yi girki?" nima murmushin nayi nace "Dada ai nasan ba abincin Helen zakici ba gashi rabonmu da abinci tun safe!" "Toh Allah yayi miki albarka Zara" cikin jindadin addu'ar Dada na amsa muka futa parlour! tayi matukar jindadin kunun da na dama mata musamman saboda babu abinda tafi so a garin irin kunu! bayan mun kammala na tattara kayan na kai kitchen sannan na shafa mata maganin ciwon kafarta da indai akai tafiya sai an mata amfani dashi saboda zirga zirga!
Dakina na dawo na janyo Ipad dina na shiga Skype na kira Aisha! sau uku tana ringing ta katse bata amsa ba! sai na tura mata message mun iso lafiya na kashe ipad din na kwanta!
washegari ma ni nayi mana break fast sannan na shiga aikin dakina! jera komai nayi cikin wardrobe na jera kayan kwalliya kan vanity table! na sauya bedsheet daga fari zuwa purple na kunna burner na saka sandal wood ko'ina ya dau kamshi mai dadi!
karfe hudu na yamma Daddy ya iso! nayi maza na shiga toilet nayo wanka na shirya! Black pencil Armani trouser da top dinshi pitch na kawo jacket mai kauri black na dora! booth dina har guiwa yake duka jikinsa gashi ne shima black! na feshe jikina da turaren Swiss Arabian masu nauyi wanda suka Dace da wether din!
tare da Daddy muka kama hanyar Liverpool a mota daya! lokacin da muka isa asbitin andawo da Ya Mahmud kenan da dakin aune aunen likitoci a galabaice yake sosai! Mami ta futo daga dakin kenan tana share hawaye tayi tozali da mu! Da wani irin shock, suprise da emotion take kallonmu! kawai sai gani mumai Dada ta karasa ta rungume Mami ta barke da kuka tana cewa Mami ta yafe mata! itama Mamin sai ta fashe da matsanancin kukan ta rukunkume Dada! Daddy kawai murmushi yake yayi folding hannuwanshi a kirji yana kallon wannan scene mai kayatarwa!
Nikam kofar dakin Ya Mahmud na tura na shiga cikin sanyin jiki!
a kwance yake magashiyan yana baccin wahala! duka jikinsa na'urorin likitoci ne kala kala sai dai babu oxygen din alamar numfashinsa na tafiya dai dai! wasu siraran kwalla suka dinga biyo idanuna! ko na menene bansani ba!

hello lovies💞💞 it's been a while! i am sorry for the late update! I am super busy wallah!
through out this month bazan samu daman update koda yaushe ba! amma i promise you ina samun nutsuwa zan dinga update every 2days!
thanks for your understanding💝💝
Enjoy!!

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now