HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE THIRTY-THREE

865 64 6
                                    

Kallon Aisha kawai nake tana kuka amma nikam zuciyata ce take wani irin suya kamar zata tarwatse, kaina yayi mun nauyi har bana iya juya shi yanda nake so! inama nima zanyi kukan da hawaye kamar yanda take yi? kila ko zan samu sassaucin radadin da nake ji. A maimakon na rarrasheta sai kawai na mike na bude Windows din dakin na tsaya a gabansu ina shakar iskar da hadarin da ya taso yake bayarwa don ji nayi sanyin Acn baya wadatar dani. mun kai mintina goma a haka kafin ta mike ta shiga toilet ta wanko fuskarta ta futo! Gefena tazo ta tsaya ta dafani sannan ta soma magana "Zara bamu da isashshen lokacin tunani da maganganu mafuta kadai ya rage mana mu nema, wacce hanyar kike gani zamu fi samun saukin shawo kan al'amarin cikin sauki?Wa zamu tunkara da wannan maganar? ya kamata muyi hanzari domin bamu da lokaci isashshe, Ni a ganina mu samu Gwaggo muyi mata bayani dalla dalla tun daga farko ina kyautata zaton zata fi kowa fahimtar mu kuma kinga itace me yankewa, ita kadai ce zata hana aurenki ya hanu! ko ya kika gani?" kallonta kawai nake tana rattabo jawabi babu kakkautawa   bansan lokacin da nayi murmushi ba!
Gyara tsayuwata nayi sosai sannan na fuskance ta kafin na soma magana a nutse!  "Kina tunanin abu ne mai sauki bada wannan labarin ga Gwaggo? kina da tabbacin akwai wanda zai yarda cewa ba bakinmu daya da ke ba? kina tunanin ba za'a ce plan muka hada kawai don lalata wannan auren ba? idan bakiyi tunanin haka ba ki fara yanzu! A mutanen duniya kakaf ni banga wanda ya dau aure da muhimmanci irin Gwaggo ba, banga kuma wanda baya magana biyu irinta ba, Idan da akwai abinda yafi komai wahala a yanzu shine sauke ra'ayin Gwaggo akan Imam domin ya dade da siye zuciyarta da kyawawan halaye da nagarta da karramawa da mutuntawa! abu na biyu shine bamu da kwakwkwarar hujja a hannunmu wadda take da karfin da za ta iya rushe auren da ya rage sati uku a daura shi! Abu na uku kuma mafi muhimmanci shi ne Ni Zara wallahi tallahi bazan janye auren Imamu don kar na cutu ke kuma na jefa ki cikin matsala ba! ki sa a ranki wannan ba me yiwuna bane! Ikirarin da Imam yayi yana nufin bata miki suna da mutunci da daraja da kima ne a idon duka duniya ciki har da mahaifanki, da yan'uwanki da danginki da masoyanki da duk wani mai muhimmanci a raguwarki.....wani bakin Fenti zai goga miki wanda har abada ba zai goge ba, don ko da zai dawo yace karya ne, hakan ba zai wadatar da wasu mutanen su yarda da ke ba! Imamu hatsabibin gaske ne, kuma mutum me hadarin gaske, kina tunanin duk bai shiryawa faruwar hakan ba? ya san girman amincin da ke tsakaninmu da kuma soyayya don haka na tabbatar yasan zaki iya irin wannan sadaukarwar a kaina kamar yadda kikayi ta soyayyar da kike masa!
ina kuma tabbatar da cewa ta inda zai bullo mana sai ta fi wannan masifa da tashin hankali a garemu!
Kaddara ce ta shigo mana muna zaman mu Aisha! kuma dole ta fada akan daya daga cikinmu ko kuma ta raba amincin mu! babu yanda zamu iya guje mata domin ta sakamu cikin tarkon da babu kofa babu matsera!
Na yarda da kaddara Aisha kuma nayi alkawarin zan sadaukar da farin cikina domin gudun faruwar batanci ga rayuwarki. Zan auri Imamu ko da hakan na nufin fadawa cikin takaici da bakin ciki da tashin hankali. ni dai nasan kome zan fuskanta ba zai kai shi zafin ganin na zuba ido wani ya bata miki rayuwa ba alhalin ina da yanda zanyi na kareki! "
Cikin dauriya Aisha tace "wannan ba zai yiwu ba Zara! sam! wallahi ba zaki auri Imamu alhalin mun san halinsa ba, ya muna ganin kashi da rana zamu taka da daddare? aure wasa ne? ki aure shi? kome zaiyi sai dai yaje yayi amma ba zaki auri mutum irinshi ba" ta sake fashewa da wani sabon kukan me bayyanar da tsantsar bakin ciki da tashin hankalin da take ciki. Dafa kafadarta nayi nace "Aisha ki rage wannan koke koken domin idan kikace kuka zakiyi toh hawayen ki zasu kare baki gama amfani da su ba, ki karfafa zurciyarki Aisha! Duk abinda ya faru da bawa mukaddari ne daga Allah kuma rubutacce ne! babu yanda zamu yi sai dai muyi ta addu'a akan Allah ya fiddamu daga tarkon da muka fada! Abinda nake tunani yanzu  shine email din nan da aka turomun hoton da Imamu da Jidda da kuma address din nan! shi zan bi nagano kowaye don na tabbatar koma waye a bayan al'amarin baya tare da Imamu kuma akwai abubuwan da ya sani masu yawa game da shi! ina fatan kila ta wannan hanyar mu samu wata makama, amma fa ko mun samu Aisha ba yanzun nan zamu yi amfani da ita ba, domin a yanzu idon Imamu da shirinsa akanmu suke, don haka cigaba zamuyi da shirye shirye kamar babu komai kafin lokacin!"
Dakyar na shawo kan Aisha ta daina kuka amma har yanzu ta kasa yarda da na auri Imamu akan dalilin ikirarin bata mata suna da yace zaiyi! cece kuce me yawan gaske muka yi kafin na kamo hanya na taho gida.

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now