HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFATASIA PAGE THIRTY-NINE

755 66 10
                                    

Kallona yake cikin zuzzurfan nazari hannunsa duka biyu cikin aljihunan trouser dinshi. ya dade yana kallona sannan yabi doguwar rigar atamfar jikina da kallo wadda ta yamutse, ta futa hayyacinta, hular kaina tana gefena don haka cukurkudadden gashina a matukar hargitse yake kamar dai mahaukaciyyar nan sabon kamu wadda ake gudun kusantarta don kar tayiwa mutane illa. yau kwanana shadaya banyi wanka ba, balle wata banza kwalliya. toh ni kaina ma ban gama sanin halin da nake ciki ba balle na kula da kaina na gyarashi.

A nutse ya soma takowa cikin dakin ya tsaya a bakin gadon yana kallona fuskarshi dauke da matukar tausayi, jimami da tashin hankalin yanayin da ya sameni. Amma kuma bayan abinda baifi dakika biyar ba sai ya daure fuskar tamau ya soma muzurai irin wanda na gani a tare da shi farkon haduwarmu a garin Jedda! ji nayi gabana ya fadi, don ya sauya daga friendly Ya Mahmud din sa'a daya zuwa mugun nan da ya kusa karyamun yan yatsu a garin Makkah.
cikin dakakkiyar murya yace "Taso ki biyoni parlour yanzun nan" yana gama fadin haka ya juya yana huci. ai babu shiri na mike na rufo masa baya cikin tsoro.
Dada da Baba Rabi da Ya Nuratu na zaune a parlour sai duk suka zubo mana idanu suna kallon yanda film din namu zai kwashe ni da shi. "Nuratu tashi ki hadamun ruwa mai zafi a toilet din wannan yarinyar?" ji nayi cikina ya sake bada wani sauti "kululuuuu", wato sunan nawa ma ba zai fada ba! Toh wai ko dai Ya Mahmud din yana da twin brother ne. daya mai kirki daya mugu, nafi yarda da hakan gaskiya domin big brother dina da na sani mai jin kai da tausayina ne, mai kyautatamun ne mai son sakani farin ciki sabanin wannan wanda bai san far'a ko murmushi ba, balle wata kalmar tausayi ko tausasawa.
Babu musu Ya Nuratu ta mike ta shiga dakina don cika umarnin babban Yaya. wata muguwar harara ya watsomun sannan ya nuna mun hanyar dakin alamun na shiga.
cikin tsananin tsoro na shige ina waiwayenshi don gani nake kamar zai rufeni da duka ne.
Muna tsaye cirko cirko a dakin Ya Nuratu ta futo daga toilet, sai da ta wani dan risina ma sannan tace masa ta hada. cikin daure fuskar da tafi ta dazu yace "Maza bita tayi wanka ta wanke wannan bolar da ke kanta tas, na baku mintina ashirin da biyar ina dakin nan a zaune. Ke kuma (ya dubeni) wallahi idan kikai mata gardama sai nayi miki dan banzan dukan da zan sake tayaki badda kamanninki. wuce kuje." Ai kafin ma ya rufe baki na kutsa kai cikin toilet din domin tuni ya soma kiciniyar zaro belt din jikinsa.
A toilet babu wanda yace wa kowa komai, illa dai ta bude drower da nake aje kayan wanka ta ciro mun shot da crop top ta mikomun sannan ta saki labulen da ya zagaye jacuzzin.
A hanzarce na sauya kayan daga doguwar rigata. sai da ta daidaici nagama sannan ta zuge labulen ta soma debo tarkacen mayukan wanke kai duka na kamfanin "BODY SHOP" ta soma wanke mun gashina tana tajewa cikin nutsuwa da tausasawa. duk da haka ba karamun zafi nakeji ba amma bance komai ba. bayan ta wanke gashin ya futa tas sai ta ciro karamun towel ta nade mun shi ciki. sannan ta hada wani ruwan cikin jacuzzin ta soma cudamun fatar jikina da ke sarari. har da tafin kafata sai da ta bata nata extra care din sannan ta sake sauya ruwan ta zuge mun labule ta futa. ta zuge mun labulen tana jirana.
Ni na karasa wankan gabadaya nayi alwala kamar yanda na saba sannan na saka jibgegiyar bath robe(rigar wanka) na har kasa fara sol da ratsin gold mahadin towel din kaina duka yan gidan "VERSACE" na futo ina jin wata irin sanyayyiyar iska na kadani me salama da rahma. lallai tsabta rahama ce.
Bakina ma mintina biyar nayi ina bashi nashi extra care din da kakkarfan toothpaste da mauth fresheners don a kwanakin nan shima yaga ta kansa.
Mintuna arba'in muka kwashe kafin mu futo hannuna sarke cikin na Ya Nuratu kamar wata wadda zata gudu. Ya Mahmud na zaune bakin gado da belt a hannunsa yana jiranmu! yana ganinmu ya mike tsaye sannan yace "maza ki shirya ku futo ina parlour ina jira! don stay long!" ta amsa mishi,  sannan ya kada kai ya futa.
Gaban dressing mirror ta zaunar dani ta shiga busar mun da gashina tare da shafe shi da mayukan gashi na "Body shop" masu kamshi sannan ta nade mun shi cikin band ya kwanta lambau gwanin sha'awa! barina tayi ina shafa mai da body oils da sprays masu sanyi ta koma wardrobe dina ta ciromun kaya.
Cikin minti goma na kammala shiryawa cikin sassaukan skirt and blouse na super. tana cikin dauramun dankwali ne naji zuciyata tayi wani irin bugu a dalilin kamshin da ya karade dakina! kamshin mutum daya da tafi kowa amfani da wannan kamshin, kamshin amiyinata na yau da kullum, kamshin abokiyar sirrina, kamshin turaren "Empire oud" na gidan turaren "Al musbah" wanda bata rabo da shi ako da yaushe cikin jikinta da kayanta da handbag dinta.
tuni na fizge kaina daga hannun Ya Nuratu na rugo parlour a guje ina cewa "Aisha ce! wallahi kamshin Aisha ne" sai dai kash! ina zuwa falon nayi sak, a maimakon ganin abinda nayi harsashe da doki, da murdaddiyar fuskar Ya Mahmud na soma cin karo. A hargitse na nufi kofa ina dube dube sannan na dawo kusa da Dada na zauna na kalleta jikina na tsuma nayi magana ta kashin kaina a karon farko tun bayan rasuwar Aisha!  "Dada kamshin turaren Aisha nake ji! tana ina? kamshin Aisha ya cika gidan nan wallahi" wani irin murmushi tare da Hamdala Dada ta saki tana kallon Ya Mahmud. hannunta na kama nace "Dada don Allah tana ina? wallahi dagaske na jiyo kamshin turarenta Dada" murmushin fuskarta ne ya sauya zuwa wani expression na tausayi da jimami! a sanyaye ta dube ni tace "Zara kin taba ganin wanda ya mutu ya dawo? Aisha ta rasu kuma ba zata sake dawowa ba" Ji nayi gabana ya yanke ya fadi, tsoro ya kamani. shikenan ta faru ta kare! abunda nake gudu kenan nayi magana komai ya tabbata, shiyasa nafi ganewa zaman da nakeyi na mafarki, ina jiran ranar da zan farka!
Sunkuyar da kaina kasa nayi kawai nayi shiru, yanzu Aisha ta ta mutu? Aisha ta rasu? ta tafi kenan?" Ya Mahmud ne ya taso ya komo gefena suka sani a tsakiya shi da Dada. cikin murya mai taushi da tsantsar nutsuwa ya soma magana.

"Zara look at me!" shiru nayi sai da ya sake maimaitawa sannan na dago na kalleshi! "ke musulma ce?" na girgiza kaina cikin mamakin tambayar! ya sake cewa "Duk musulmi yasan imani! kinsan menene shika shikan imani?" na gyada kaina a hankali!
yace "Good! lissafamun su" a sanyaye na soma koro karatun islamiyyata har ina tuna muryar Malam Shu'aibu mai  daukarmu Tauheed da lokacin da yake mana wannan darasin
"Shika shikan imani guda shida ne! Na daya shine an tu'u mina billahi' ka gasgata cewa akwai Allah, kasan Allah da sunayensa da sifofinsa da ayyukansa!
'Wa mala'ikatahu': Kayi imani ka gasgata da akwai mala'iku. wasu halittun Allah da Allah ya wakilta ga wasu al'amura kamar saukar da wahayi, saukar da ruwan sama, rubuta lada ko zunubin dan'adam, karbar rayuka da sauransu.
(Wa kutubuhi) ka gasgata litattafan da Allah ya saukar ga Manzanninsa wadanda suke koyar da dan'adam ka'idoji da iyakokin ubangiji da yanda mutum zai gudanar da dukkan rayuwarsa.
(Wa Rusuluhi) Ka gasgata Manzannin Allah da duk abubuwan da sukazo da shi.
(Wal yaumil akr) ka gasgata cewa alqiyama gaskiya ce. akwai ranar karshe ranar da za'a nunawa kowa matsayinsa na abinda ya aikata a duniya na alkhairi ko na sharri.
(Wa tu'uminu bil Qadr! Khair wa sharr) ka gasgata cewa duk abinda ya sameka daga Allah ne, ka yarda da duk abinda yazo maka mai dadi ko mara dadi ka yarda da Allah ka dogara da shi. ka karbi kaddarar ka hannu bibiyu." ina kaiwa nan Ya Mahmud yace "barakallahu feeki! toh akan na karshe nakeso muyi magana Zara! wato kaddara! ita kaddara wani rubutu ne akan mutum wanda baya gogewa, mai kyau ko mara kyau, mai dadi ko mara dadi, idan har kana rayuwa to tabbas dole kaddara ta sameka ta hanyar da bakayi zato ba, amma me? me yake nuna kai musulmi ne na kwarai? me yake nuna ka yarda da Allah kayi imani da shi? Zara shine ka karbi ko wacce irin kaddara ce da hannu biyu ka yarda da Allah kasan cewa da ikonsa da saninsa komai yake faruwa! hakurinka da juriyarka sune abinda Allah yake jarrabawa. hakane ko ba haka bane?"
A sanyaye na girgiza kaina! yaci gaba da cewa "Akwai wanda yafi karfin Allah ya jarrabe shi?" na girgiza kai ya sake cewa "Akwai wanda yafi karfin kaddara?" na sake girgiza kaina. ya kuma cewa "Imanin musulmi zai cika babu wannan sharadin na shida acikin shika shikan imani?" na girgiza kai! yace "Toh Zara menene dalilin da yasa ke ba zaki karbi jarrabar da Allah yayi miki ba? meyasa ba zaki yarda da kaddara ba? me yasa ba zaki yarda cewa Aisha ta amsa kiran mahaliccinta ba?! Zara Kullu nafsin za'ikatul maut! Dukkan rai sai ta dandani mutuwa, kin taba ganin wanda akace ba zai mutu ba?" na girgiza kaina. yace "kin taba ganin wanda yafi karfin mutuwa?" na kuma girgiza kai yaci gaba " Toh Aisha ta mutu, Iya wa'adin da Allah ya dibar mata na numfashi kenan kuma sun cika akwai mahalukin da zai hana?" na girgiza kai! "Ina Dadynki?" a raunane nace "Ya mutu!" yace "toh mutuwar shi ta sa kin daina rayuwa? ta sa Dada daina rayuwa ko kuwa Mami taki hakura ta bishi?" na girgiza kai! yace "idan da mutuwa zata bar wani, wa zata bari? mafi girman halittar Allah! mafi alkhairin duniya da lahira Manzon Allah SAW! Zara bamu zo mun tarar da shi ba! toh Aisha wacece ita kuma yar wacece da ba zata mutu ba?" nace "babu" yace "Zara Aisha ta tafi, ta amsa kiran Ubangijinta kuma ba tayi sauri ba, mu da muke raye bamu yi jinkiri ba, kowa da lokacinsa Zara! ita nata ne ya cika ta tafi, muma zaman jiran tamu mukeyi! don haka ki kadaita Allah ki daina wannan shirmen Allah baya farin ciki da abinda kikeyi, Allah ba zai alfahari da ke cikin bayinsa masu imani da shi ba Zara kina son haka?" Wani matsanancin tsoron Allah da imani ne ya shige ni irin wanda ban taba ji ba a rayuwata! zuciyata tayi matukar rauni tayi laushi nadama mai yawan gaske ta kamani tare da tsoron fushin Allah a kaina. a sanyaye na soma cewa "Astagfirullah! Allah ka yafe mun, Allah nayi nadamar abinda nayi, Allah idona ya rufe da kaunar baiwar da ka dauke hankalina ya gushe! Allah na tuba ka yafemun! Allah na karbi kaddararka hannu bibiyu Allah ka bani hakuri da juriyar rashin Aisha! Allah na roke ka ka bani nutsuwa ka sanyaya mun kwakwalwata da zuciyata na samu danganan karbar wannan gingimemen rashi da nayi "
a lokacin da nake wannan furucin Dada kuka ta fashe da shi, Ya Mahmud na hawaye masu dumi, Nuratu ta rike Baba Rabi itama tana nata kukan mara sauti, amma ni sam idona bai kawo ruwan ba! hawayen basu samu damar sakkowa ba duk yanda zuciyata ta karye kuwa.
cikin dauriya nace
"Ya Mahmud nagode da tunasarwar ka! nagode da kulawarka! you are the best  brother anyone could ever wished for! Allah ya saka maka da alkhairi! Allah yajiqan Aisha! Allah yajiqan Aisha! Allah ya sadata da Annabin rahma! Allah ka baiwa Aisha madaukakin masauki a gidan aljanna ka haskaka mata kabarinta ka fadada mata shi! Allah kayi mata rahamarka Ya Allah" 
************************************

salam! how was it? do you have a friend like Aisha? have a ever lost a loved one? mutuwa da akwai ciwo musamman mutuwar wanda kuka shaku da Shi don haka kada kuga laifin Zara da gigicewar da tayi! Allah dai  ya kawo mana Ya Mahmud ya kawo taimako!

one more update before we close! Insha Allah!

HAUSA ARAB PART 1Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu