HAUSA ARAB💫💫💫 BY CUTYFANTASIA PAGE THIRTEEN

887 66 8
                                    

Duka wasu shirye shirye da tsare tsare sun kammala daga fannin angwaye da amare. invitation card yaje hannun duka wadanda ake bukatar su halarci wannan taro a yau lahadi kenan da ya rage saura kwana biyu a soma gabatar da shagulgulgunan wannan buki. gareni abun ba haka yake ba domin ni kwanakin yinsu nayi cikin gudanar da assignment dina na farko akan alakar da ke tsakanin Imam da Aisha. na fara bincike na ne ta bangaren daga wayar Aisha da ta Imamu wadanda suka kasance basu da wuyar zuwa hannuna. duk da ba karba nayi kai tsaye ba fakar idonsu kawai nakeyi na dauka.
na fara da wayar Imamu ne a ranar da yazo gidanmu ya kai sallar magrib sai ya zube wayoyinshi da hula ya futa da Ya sadik suka tafi masallaci bayan ya ga shigata ciki. suna futa nikuma na dawo na dau wayar. guda daya akwai password dayar kuma babu. ita na dauka na nemi waje na zauna na fara bincikawa. da messages dinshi na fara kirjina na dukan uku uku da fargabar abinda zan gani.
banyi nisa ba naga sunan Aisha anyi saving da besty kamar yanda ya saba kiranta a gabana. swiping nayi sai da nazo na can farko wanda suka fara musaya. sai da na rufe idona na bude ina karanto duka addu'ar da tazo bakina sannan na bude text din. ga abinda idona ya fara cin karo dashi:

"Na bar diary na a motarka i am begging you with name of Allah kada ka bude mun ko da wasa kada ka bude mun. sirrina ne kuma Allah ya hana bude sirrin wani ina hanyar zuwa gidanku na karba in nazo bakin gate zan ma waya"
Ga kuma kwanan wata nan. na duba wata biyu da suka wuce kenan!
banga amsar da ya bata ba sai wani text din da ita ta sake turowa tana cewa

" Ko da wasa Imam kada ka dauki wannan maganar da muhimmanci domin ko a mafarki haka ba zai taba faruwa tsakanina da Zara ba domin in akwai wata halitta mai muhimmanci a wajena Zarah ce"

kaina yayi mugun daurewa da wannan maganganu da kuma abinda suke nufi. na sake dauriyar cigaba wannan ma itace ta tura masa.

"Kada kayi kasadar yin wannan
gangancin domin babu abinda zai janyo sai kiyayya da gaba da kuma tashin hankali mara iyaka. duk duniya banga abinda ba zan barwa Zarah ba ciki har da farincikina"

Ya salam! na fada gumi na tsatstsafo mun domin rashin sanin yanda wadannan maganganu suka dosa kai tsaye. sanin bani da lokaci ya sanya na sake cigaba sai a lokacin naga reply din Imamu wadda naji kamar zanyi zawo kafin na bude.

"idan hakan na nufin kunnowar
3rd world war i'm never gonna let this go! and i promise you zan tsaya akan maganata a kowanne rintsi"

Gabadaya kaina ya kulle tamau na rasa gane wanne tunani zanyi na fahimci yaren da sukeyi? wacce hanya zanbi nagane inda maganar ta dosa? meye suke jayayya akansa?meye ya harzuka Imam yayi wannan alkawarin? cikin sanyin jiki da rawar hannu na cigaba da karatun text na gaba da Aisha ta turo mako biyu da suka gabata.

"Imam ka sameni a park and zoo yanzu kuma kada ka taho da motarka"

Duka idanuna na zaro hankalina yayi bala'in tashi! har haduwa suke a wani waje? innalillahi wa'inna ilaihi rajiun!! me ke shirin faruwa dani ne?
Text na karshe dake cikin wayar kwana uku da suka wuce Imam ya tura mata! ga abinda ya rubuta

"Thank you! i will try my best insha Allah"

kasa nayi da wayar cikin sanyin jiki da kunar zuciya da fargaba mai yawa. na tabbatar akwai wata alaka mai karfi da ke tsakanin Aisha da Imam. akwai kuma abinda suke kullawa sannan ba wannan text din bane iya communcation dinsu. nayi iya bincike na babu abinda na sake samowa cikin wayar sai na mayar da ita na ajiye.
ko da ya dawo nayi matukar kokari ban nuna mishi komai ba don haka mukai sallama kamar yanda muka saba ya tafi.

Ta fannin Aisha kuwa a E-mail dinta na soma gano wani abu. ranar da zan bude naga ta sake password abunda ya bani mamaki domin babu wani account dinta na social media ko nawa wanda bamusan password din juna ba.(do you see how close we are? do you understand how attach our lives are) kiranta nayi na tambayeta sai tace babu komai kawai ta sauya ne kuma zata turomun sabon Password din. maganar da har yau bata turo ba nikuma ban sake mata maganar ba.
ranar wata monday na je gidansu na samu Aisha bata nan Umma ta aikesu kasuwa da Driver. cikin sa'a na shiga dakinta sai naga system dinta yashe akan gado a kunne da azama na hau gadon na dawo da hasken screen din na saka password. unfortunately tana cikin karanta messages dinta na E-mail aka kirata ta tashi ta manta bata futa daga ciki ba. ban sha wahala ba nagano sakonnin Imam!
zuciyata na bugawa na shiga dubawa ban samu damar gane yaren da suke ba kamar yanda nagani a tashi wayar amma lallai rokonta yake tukuru akan wani abu wanda ita kuma taki yarda. musamman a wata message da yake cewa

HAUSA ARAB PART 1Where stories live. Discover now